Raja'a –komowa-



(2)Na biyu:  Karyata hadisan da suka zo game da ita.

(1)A bisa asasin Kaddara cewa muhawarorin biyu daidai suke, sam yin imam da ita ba a daukarsa a matsayin kyamar da masu adawa da Shi'a suka juya ta kuma nawa ne daga cikin abubuwan da suke daga cikin korarru wadanda sauran bangarorin musulmi suka yi imani da su ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su,amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba.

Akwai Misalin su da dama, cikinsu akwai:

Yarda da yiwwar rafkanuwa ga Annabi (SAW) ko kuma aikata saboda kuma imani da Wanzuwar Alkur'ani' da kuma batun wa’idu da kuma imani da cewa Annabi bai ba da nassi kan halifan bayansa ba.

To dangane da Muhawarori biyun da muka kawo a dauka cewa ba su da wani asasin ingancin tabbatar da raja'a amma ai mun riga mun bayyana cewa ita ra`ja'a wani nau'i ne na tayar da mamaci ko kuma komo da ainihin jiki. sai dai kawai cewa ita tana aukuwa ne a wannan duniyar.     Dalilin kuma da ke tabbatar da yiwuwar tashin kiyama shi ne dalilin da ke tabbatar da ita babu wani abu kuma da zai sa a yi al'ajabi game da ita sai dai kawai don zukatanmu ba su saba da ita ba ne a rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu da sabubbanta da abubuwan da ke hana ta da za su sanya yin ikrari da ita ko mu kore ta. da kuma fahimtar cewa abu ne marar sauki ga mutum ya yarda ya gaskata abinda bai saba da shi ba. wannan kuwa kamar wanda ya ga cewa tayar da mamata abu ne bako ya ce: "wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu". Aka ce masa: "Wanda Ya fare su a farkon farko shine zai raya su kuma shi a kan kome masani ne'". (Yasin: 78-79)

Na"am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali akai na tabbatar da ita ko kore shi, ko kuma mu ka raya rashin dalili to wannan kuwa zai kallafa mana komawa ga nassosin addini wadanda suke daga tushen wahayin Ubangiji. Kuma abinda zai tabbatar da yiwuwar raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Alku’ani kamar dai mu’ujizar annabi Isa (AS) a raya maiacce: "Kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho kuma ina rayar da matattu da izinin Allah." Surar Ali Imran: 49.

Da kuma fadin Allah Ta'ala: "Ta yaya Allah zai raya wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah Ya matar da shi Shekara dari sa'an nan kumo ya raya shi." Surar Bakara: 259.

Da kuma ayar da ta gabata da ke cewa: "Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu." Surar Mumin: 11.

Ma'anar wannan ayar ba za ta fito daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba koda yake wasu masu tafsiri sun wahalar da kansu wajen yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba kuma ba zai tabbatar da ma'anar ayar ba.

(2) Muhawara ta biyu:- kuwa wadda take cewa hadisai game da ita raja'a Kagaggu ne kawai wannan da’awar ba ta da wani asasi. dominraja'a na daga cikin al'amuran da suke ba makawa sun zo daga Ahlul Bait (A.S.) daga hadisai masu tafarkunan ruwaya da dama.

Bayan duk wannan ashe ba a yi mamaki ba game da mashahurin marubuci mai da'awar sani kamar Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, saboda yana cewa; "Ai Yahudanci Ya bayyana a cikin Shi'anci ta hanyar batu game da raja'a" Don haka ni nake cewa gare shi:

"To ai Yahudanci ma ya bayyana a Alkur'ani game da batun Raja'a" kamar yadda ya gabata game da ayoyin Alkur'ani da suka ambaci raja'a.

za kuma mu kara masa da cewa:

Alal hakika babu makawa Yahudanci da Nasaranci su bayyana a cikin da dama daga abubuwan da aka yi imani da su da kuma hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi Mai girma (SAW) ya zo yana mai gaskata Shari'o'i da suka gabata, kuma koda yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. To bayyanar Yahudanci da Nasaranci a wasu abubuwan da Musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin Musulunci idan ma har aka dauka cewa Lalle raja'a daga akidojin Yahudanci take kamar yadda wannan marubucin yake da'awa.

Ko ta halin kaka dai raja'a ba wai tana daga cikin jiga jigan addinin (Musulunci) da ya wajaba a dauke ta a akida ba ne da kuma yin bincike a kanta sai dai kawai imani da muka yi da ita biyayya ne ga hadisai ingantattu daga Ahlul Bait (A.S.) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga Karya, kana kuma tana daga cikin al'amuran gaibi da suka ba da labari game da ita kuma aukuwarta ba gagara badau ba ne.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2