kaddara a mahangar shi'a



Imam Sadik Alaihis Salam Ya ce:

"Wanda Ya yi da'awar cewa bada Ya auku ga Allah Ta'ala game da wani abu bada irin na nadama to agurinmu wannan Kafiri ne a game da Allah mai girma. Har ila yau kuma Ya ce: "Wanda Ya raya cewa wani abu Ya yi Bada ga Allah wanda da Ya kasance bai san shi ba jiya to ni ba ni ba shi''.

Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kamar nuni da ma'anar "Bada" yadda ta gabata kamar yadda Ya zo daga Imam Sadik Alaihis Salam cewa: "Bada bai taba yiwuwa ga Allah ba kamar yadda Ya yiwu gare shi ba a kan Isma'ila dana.

Don haka ne wadansu marubuta daga cikin bangarorin musulmi suka dangata Bada ga Shi'a Imamiyya don yin suka ga mazhaba da tafarkin Ahlul Bait (AS) suka sanya shi Ya zama abin kyama ga Shi' a. Sahihin al'amari a nan shi ne mu fadi kamar yadda Ya fada a Alkur'ani :

 "Allah Yana shafe abinda Ya so kuma Yana tabbarwa Asalin littafi kuma gare Shi Yake." Surar Ra'ad: 39.

Abin nufi shi ne cewa Allah Ta'ala na iya bayyana wai abu a bisa harshen Annabinsa ko waliyinSa ko kuma a zahiri wata maslaha ta sa bayyanawar sa'an nan daga baya kuma Ya shafe shi Ya zama ba abinda Ya bayyana da farko ba, kamar yadda Ya faru a kissar Annabi Isma'il (A.S.) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S.) Ya ga yana yanka dan shi a mafarki.

Wato kenan ma'anar maganar Imam Alaihis salam sai ta zama kenan cewa: Lalle babu wani abu da Ya bayyana ga Allah Ta'ala na daga al'amari a kan wani abu kamar yadda Ya bayyana gare shi a kan Isma'ila dansa domin (Allah) Ya dauke shi (Isma'ila) Kafin shi (Imam Sadik (A.S.) domin mutane su san, (cewa) shi (Isma'ila) ba Imami ba ne, bayan a zahiri Ya riga Ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.

Abu da yake da "Bada" a ma'ana kuma shi ne shafe hukunce­hukuncen shari'o'in da suka gabata da shari'ar Annabinmu Muhammadu sallallahu Alaihi wa ahlihi hatta ma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen shi Annabin namu sallallahu Alaihi wa ahlihi.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2