Alamomin Soyayya



9 / 2

Rawar Da Soyayya Take Takawa Ga Rayuwar (Makomar) Mutum

A- Tashin Mutane Tare Da Wanda Suke So

331. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya so mutane za a tashe shi tare da su[9].

332. Daga littafin Amali na Sheikh Dusi daga Abdullahi dan Hasan daga iyayensa (A.S): wani mutmu ya zo wajen Annabi (S.A.W) sai ya ce: ya manzon Allah, mutumin da yake son wanda yake salla, amma ba ya salla sai ta farilla, kuma yana son mai sadaka amma ba ya sadaka sai ta wajibi, kuma yana son mai azumi amma ba ya azumi sai na watan ramadana? sai Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Mutum yana tare da wanda yake so[10].

333. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka riki wani abu daga aiki na gari, ka kuma yi abota da aboki nagari, hakika mutum yana da abin da ya yi ne, kuma a lahira yana tare da wanda ya so[11].

B- Tashin Masoya Ahlul Baiti (A.S) Tare Da Su

334. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya so mu zai kasance tare da mu a ranar lahira, kuma da wani mutum ya so wani dutse to za a tashe shi da shi ranar lahira[12].

335. Littafin Amali na Abdullahi dan samit: Abuzar ya ba ni labari –ya kasance karkatarsa da yankewarsa zuwa ga Ali (A.S) da Ahlul Baiti ne (A.S) sai ya ce; na ce: ya annabin Allah, ni ina son mutane amma ba na iya yin ayyukansu. Ya ce; sai ya ce: ya kai Abuzar! mutum yana tare da wanda yake so, kuma yana samun sakamakon abin da ya yi ne. Sai na ce: ni ina son Allah da manzonsa da ahlin gidansa, sai ya ce; kai kana tare da wanda kake so[13].

336. Littafin da’aimul islam: daga Abu Ja’afar Muhammad dan Ali (A.S): hakika wasu mutane sun zo masa daga khurasan, sai ya duba wani mutum daga cikinsu da hakika kafafunsa sun tsattsage, sai ya ce masa: meye haka? Sai ya ce: nisan hanya ne ya dan annabin Allah, kuma wallahi babu wani abu da ya zo da ni daga inda na zo muku sai sonku Ahlul Baiti (A.S). sai Abu Ja’afar (A.S) ya ce: yi albishir, kai wallahi za a tashe ka ne tare da mu. Sai ya ce tare da ku ya dan manzon Allah ?! Sai ya ce: haka ne, babu wani bawa da zai so mu sai Allah ya tashe shi tare da mu, shin akwai wani abu addini idan ba so ba, Ubangiji madaukaki yana cewa: “ka ce idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni sai Allah ya so ku” [14].[15]

9 / 3

Abin Da Yake Faruwa Na Aibi Da Abin Ki Sakamakon So

337. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Son abu yana makantarwa yana kurumtarwa[16].

338. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: idon masoyi makauniya ce daga aibobin abin so, kuma kunnensa kurma ne daga munin ayyukansa[17].



back 1 2 3 4 next