Masa'aloli Daban Daban



Masa’aloli Daban daban

T: Idan mu'amalar manyan malamai da azzaluman shugugabanni zai iya sanya su su rage zaluncinsu, shin yin hakan ya halatta a gare su?

A: Idan har malami yana da tabbacin cewa mu'amalarsa da azzalumin (shugaba) zai iya hana aikata zalunci kana kuma zai yi tasiri wajen hana shi aikata munkari ko kuma ya ga wani lamari muhimmi da ke bukatar kulawa to babu wata matsala ga hakan.

T: Na yi aure tun shekarun baya da suka wuce, kuma ni na kasance mutum ne mai kula da addini, to amma abin bakin ciki matata ba ta kula da ayyukan addini sosai, a wasu lokuta kana bayan magana mai tsanani sai ta yi salla kuma ta sake bari, hakan yana damu na, don haka mene ne ya hau kaina a irin wannan hali?

A: Abin da ya hau kanka shi ne tsara hanyoyin da suka dace wajen gyara ta, da kuma nesantar duk wani aiki da bai dace ba, to amma ka sani cewa zuwa wajen tarurruka na addini da kuma kai ziyara ga gidajen wadanda suka damu da addini yana da tasiri mai girman gaske, wajen gyara.

T: Idan mutum ta wasu hanyoyi ya gano cewa matarsa wacce suke da 'ya'yaye da ita-tana wasu ayyuka na boye da suka saba wa kame kai, sai dai ba shi da wata takamammiyar hujjar da zai tabbatar da hakan (kamar samun shaidar da ke shirye ya ba da shaida kan hakan), ta yaya mutum zai yi mu'amala da wannan mace tattare da cewa 'ya'yayensa za su rayu ne karkashin irin wannan mace? Kana yaya mutum zai yi mu'amala da irin wadannan mutane masu aikata wannan mummunan aiki da ya saba wa shari'a, idan har ya san hakan? Tattare kuma da rashin dalilai akansu ballatana ya kai su gaban shara'a?

A: Wajibi ne a nesanci mummunan zato da kuma dogaro akan dalilan zato, to amma yayin da ya tabbatar da faruwar haramun to wajibi ne ya hana ta ta hanyar tunasarwa da kuma nasiha da kuma hani kan munkari, idan kuwa hakan bai yi amfani ba, to sai a kai al'amarin ga kotuna na kwarai idan har akwai abubuwan da aka tabbatar da su.

T: Shin ya halatta ga mace budurwa ta taimaki saurayi wajen karatu da sauransu tattare da kula da wajiban shari'an musulunci?

A: Babu matsala ga hakan, amma ya kamata ayi gagarumin taka tsantsan daga irin waswasin shaidan, kuma wajibi ne a kula da hukumce -hukumcen shari'a yayin hakan kamar rashin kebancewa da mutum ajanabiyi.

T: Da za'a samu afkuwar almundahana da kuma rub da ciki a cikin Baitul mali, sai aka samu wani mutumin da yake ganin da zai hau wannan matsayi da ya hana faruwar wannan al'amari, to amma yiwkwar hakan ya ta'allaka da ba da cin hanci ga wasu mutane don su zabe shi, to shin yin hakan ya halatta.

A: Abin da ya wajaba kan mutanen da suka ga faruwar sabawa hukuncin shari'a shi ne hani ga munkari tare da la'akari da sharuddan hakan da kuma dokokin sharia, don haka ba ya halatta a ba da rashawa ko kuma aikata wani aiki da ya saba wa doka wajen hana faruwar fasadi, na'am da hakan zai faru ne a kasar da hukuncin musulunci ke gudana, to a nan wajibin mutane ba kawai ya kare a kan gazawarsu ga yin umurni da kyakkyawan aiki da hani da munkari ba ne, face dai wajibi ne a gare su kai al'amarin ga hukumar da abin ya shafa.



1 next