Auren Mutu'a



4- Babu saki a tare da shi, sai dai mijin yana iya yafe mata muddar da ta saura a duk lokacin da ya so.

5- Ciyarwa ba wajibi ne a cikinsa sai a inda aka sa shi a matsayin sharadi a lokacin kulla auren.

6- Ba shi da iyakantaccen adadi, mutum na iya yi da iyaka adadin da ya so.

7- Ba a yi da budurwa sai da izinin waliyyinta na Shari'a.

8- Makaruhi ne a yi mutu'a da wadda ta shahara da da zina da mai zaman kanta.

9- Ya halatta ayi azalu (fitar da maniyyi a waje) yayin saduwa ba da izininta ba.

Wadannan sharudda da ire-irensu masu yawa suna iya bayyana wa kowa cewa ba a shardanta mutu'a don barna ko sangarta mutane ko raunana auren dindindin ba; sai don kara kare al'umma da rage zafi ga wadanda ba su da ikon dauwamammen aure ko wadanda suke bukatar karin lokaci don shirin auren dindindin da sauransu. Kar a manta da cewa ba don maza kawai aka shar'anta wannan auren mutu'a ba; mata ma za su iya cin gajiyarsa kusan fiye da maza. Yanzu zawarawa nawa ne suka share shekaru ba miji, ko saboda wahalhalu da suka sha a tsohon aurensu suke tsoron gaggauta sake aure; yaya irin su Ja'afar za su yi da sha'awar irin wadannan?

Wannan zai nuna kuskuren Ja'afar na kokarin nuna mutu'a da mummunan sura. Da dai zai takaita da ambaton fatawowin malaman furu'a da haka fi alheri gare shi da al'umma baki daya. Kuma ya kamata kafin zargin masu halatta mutu'a Ja'afar ya ba kansa lokacin sanin ainihin abin da suke fada a kan auren, amma abubuwan da ya bayyana sun nuna bai san fatawoyin masu halatta mutu'a ba.

Idan Shari'a ta halatta mutu'a ne don manufar saukaka wa mutane, shawarar Ja'afar na takaita da auren dindindin ba ta da mahalli kenan. Mun dace da shi a kan kira zuwa ga bin Sunnar auren dindindin amma ba tare da haramta mutu'a ba. Kuma kasancewar Manzo [SAWA] ya yi auren dindindin bai cutar da halaccinsa ba, saboda Annabi ba duk halal ya ke yi ba. Kuma ai an halatta masa rike mata fiye da hudu bayan kuyangu; yanzu Ja'afar zai iya auren mata fiye da hudu? Ko yana da hanyar samun kuyangu? Sai dai idan ya halatta wa kansa tabi'ar auri-saki, wanda zaluncinsa bayyane yake ga kowa.

Kuma ina ba masu tattauna mas'alolin addini shawara da koyon ladubban tattaunawa. Yanzu ina amfanin zargin da Muh. Umar R/Lemo ya yi na cewa littattafan Shi'a "cike suke da karya da cakuda gaskiya da karya." Wannan irin diban-karan-mahaukaciya da ya yi na hukunta "littattafan Shi'a" ya saba wa kowane irin mizani -na hankali da Shari'a. Irin wannan babban zargi ya kamata ya biyo bayan tarin misalai ne na wuraren da "littattafan Shi'a" suka yi karya da wuraren da suka "cakuda gaskiya da karya". Ya sani cewa ba a kan wasu 'yan tsiraru yake magana ba; yanzu 'yan Shi'a a kasar nan sun wuce yadda duk yake tsammani a adadi da tasiri da karfi ta kowace fuska. Ba kore samun kuskure -kai hatta ma samun ganganta karya- nake yi ga littafan Shi'a ba, amma gamammen hukuncin nasa ne yake da sa kuka da dariya a lokaci daya.

Rufewa

Na yi kokarin yin bayani ne a kan matsayin auren mutu'a a tsakanin Musulmi. Ta bayyana cewa dukkan Musulmi sun dace a kan cewa asalinsa halal ne; amma sun saba a kan wanzuwar wannan halacci da goge shi. Akwai masu ganin wanzuwar wannan halacci akwai kuma wadanda suka tafi a kan cewa an goge shi; kowa ya dogara ne da hakkin da Musulunci ya ba shi na yin ijtihadi, da yadda ya bar kofarsa a bude ga Musulmi a kowane zamani. Abin kuma sha'awa shi ne yadda Musulunci ke da fadin kirjin rungumar sakamakon ijtihadodin 'ya'yansa -matukar sun yi su bisa ka'idar yin ijtihadi- ta yadda ya ba duk wanda ya yi daidai a ijtihadinsa lada biyu na kokarinsa da samun daidai da ya yi; ya kuma ba da lada daya ga wanda ya yi kuskure saboda kokarinsa (Hadisin Bukhari ma ya tabbatar da haka).

Don haka abin takaici ne ganin yadda wasu ke kokarin takaita wa Musulunci fadinsa; da kokarin kakaba wa kansu rigar da ba ta su ba, da kokarin tilasta mutane a kan takurarren tunaninsu.Ya zama dole Musumi su kare kansu daga irin wadancan, ta hanyar lizimtar fatawoyin malamansu na furu'a da mujtahidan da suka cika sharuddan ijtihadi. Da hake ne kawai za su tsira daga fadawa rudani da rashin sanin kakkarfar majingina. Allah Ya sa mu dace amin.

 



back 1 2 3 4 5 6