Auren Mutu'a



Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin-Kai

Fadar Goge Auren Mutu'a Da AlKur'ani

Wasu daga malaman Ahlussunna da fakihansu sun tafi a kan cewa AlKur'ani ne ya haramta mutu'a kafin komai. Daga ayoyin da suke kawowa a kan haka akwai fadar Allah cewa: "Kuma su ne wadanda suke kare al'aurarsu (daga aikata sabo); sai ga matayensu ko kuyangin da suka mallaka, to lallai su (a kan wannan) ba ababen zargi ba ne. To duk wanda ya nemi wanin wannan to wadannan su ne masu ketare iyaka" (al-Mu'uminun: 5-7); bisa la'akari da cewa auren mutu'a ba aure ba ne, kuma matar da aka yi auren da ita ba matar aure ba ce, ga shi kuma da ma ba kuyanga ba ce. Aya ta biyu da suke kafa hujja da ita ita ce ayar Saki dake cewa: "Ya kai wannan Annabi, idan za ku saki mata ku sake su ga iddarsu" (al-Talak: 1). Sai kuma aya ta uku wadda ita ce ayar gado tsakanin ma'aurata dake cewa: "Kuna da (gadon) rabin abin da matanku suka bari idan ba su da da…" (al-Nisa'i: 12).

A kan haka na ke cewa:

1- Duk an dace a kan cewa Surar Mu'uminun (wadda ayar da suke da'awar an goge mutu'a da ita) a Makka aka saukar da ita, alhali Nisa'i (wadda ayar halaccin mutu'a ta zo a cikin ta) a Madina ta sauka, ta ina saukakkiyar Makka ke iya goge saukakkiyar Madina? Da wannan ba zai yiwu wannan aya ta goge mutu'a ba. Haka wannan ya raunana abin da masu haramtawa ke doruwa a kai na cewa halattawarta a farkon Musulunci ne, wanda a rayuwar Makka kenan. A duk surorin nan biyu kuwa babu wani dalili daga dukkan bangarorin biyu da ya toge ayar mutu'a da cewa a Makka ta sauka.

2- Mutu'an da muke zance a kansa AURE ne; don haka matar da aka yi da ita MATAR AURE ce; saboda tun da har AlKur'ani ya zo da shi da sigar yarjejniya tsakanin mata da miji, ya shiga cikin tsaikon aure kenan. Da wannan za mu iya kasa auren Musulunci zuwa kashi biyu: auren dindindin da auren mutu'a; a dabi'ance zai zama suna da wuraren da suka daidaita da inda suka saba da juna.

3- Duk malaman da suka halatta Mutu'a sun wajabta idda ga matar da aka yi auren da ita a duk lokacin da auren ya kare. Iddarta kwana arba'in da biyar ne da ittifakin malaman Shi'a (zancen da wasu ke dangana musu na cewa ba sa wajabta idda a kan auren mutu'a tsabagen kage ne da shaidar zur). Wannan ya bayyana kuskuren Mal. Ja'afar na tunanin cewa wani na iya "auren mutu'a da wata (mace) na awa biyu misali, kuma tsawon rayuwar auren ya kare; wani ya ya aura na tsawon kwana biyu shi ma ya kare; wani ya aura na kwana biyar…" a ina ya ga wannan? Mafi karancin muddar dake tsakanin karewar auren mutu'a da wani sabo shi ne kwana 45. Ya kamata a rika neman sani kafin ayi magana!

4- Idan kuwa don ba saki a cikinsa ne, to ai saki ba manufar aure ba ne, shi hanyar magance matsaloli ne a lokacin da abubuwa suka rincabe suka kai haddin rashin wani magani idan ba sakin ba; don haka ne ma Manzo [SAWA] ya siffanta saki da "halal din da Allah ke fushi da shi." Kara da cewa masu halatta mutu'a sun halatta miji ya yafe abin da ya saura na muddar auren saboda kowane irin dalili ne kuwa, wanda hakan ke matsayin hanyar samar da mafita irin na saki.

5- Fadar cewa an haramta mutu'a ne da ayar gado tsakanin ma'aurata, bisa la'akari da cewa ba a wajabta gado tsakanin ma'aurata a auren mutu'a ba, wannan ba kakkarfan dalili ba ne; saboda babu abin da ke lizimta wa hatta dauwamammen aure gadon ma'aurata; bisa la'akari da cewa akwai halayen da shari'a ta yanke igiyar gado tsakanin ma'aurata, kamar a lokacin da kafirci ya gindaya (saboda kafiri ba ya gadon Musulmi); ko kisa ya shigo (saboda wanda ya yi kisa ba ya gadon wanda ya kashe). Da wannan za mu iya fahimtar cewa gado wani tanaji ne na dabam daga aure, illa dai shi aure (na dindindin) daya ne daga sabubban gado; iyakarta kenan.

6- Dukkanin wadancan ayoyi ba su fito barobaro sun haramta auren mutu'a kamar yadda ayar da ta halatta shi ta fito da halattawan ba; domin kuwa ayar da ta halatta cewa ta yi: "Abin da kuka yi mutu'a da su a kan shi, to ku ba su ladaddakinsu (wannan) farilla ne" (Nisa'i: 24). Ga shi kuwa Allah Yana fadar yadda Yake goge wata aya da wata da cewa: "Idan muka shafe wata aya ko muka manta da ita (wato muka kau da kai daga gare ta) mukan zo da wadda ta fita ko kamar ta" (Baqara: 105). Idan za mu yi amfani da yadda muka saba fahimtar AlKur'ani a nan, ya kamata mu fahimci cewa ayoyin da ake da'awar goge mutu'a da su ba su fito da haramta shi daidai da yadda ayar dake halattawa ta fito da bayanin halattawan filla filla ba. Kuma ba su zo da wani hukunci day a musanya mutu'a ba (bisa la'akari da cewa da ma can akwai tsarin dauwamammen aure kafin a halatta mutu'a). Wannan ya saba da waccan ka'ida ta "goge aya da wadda ta fi ta ko irin ta."

Wadannan dalilai shida kawai sun isa su sa dole mu ki yarda da goge mutu'a da wata aya daga AlKur'ani.

Fadar Goge Auren Mutu'a Da Hadisai

Wannan ya kawo mu nazari a kan da'awar goge mutu'a da ruwayoyi, wanda shi ne mafi karfin madogaran masu haramtawan. Ruwayoyin haramta mutu'a sun kasu kashi biyu kamar haka:

Kashi Na Daya: Su ne ruwayoyin dake dangana gogewan ga Manzo (SAWA). Irin wadannan hadisai an dangana ruwayarsu ga mutane uku:



1 2 3 4 5 6 next