Wuce Gona Da Iri



j)– Tuhuma

Daga cikin hakan har da tuhumar mumini, ko kuma mummunan zato gare shi.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Idan wani mumini ya tuhumci dan’uwansa imani(nsa) zai narke cikin zuciyarsa kamar yadda gishiri ke narkewa cikin ruwa[27]”.

Daga wajensa (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) cikin wani zance nasa yana cewa: Ka bar aikin dan’uwanka a mafi kyaun yanayinsa, har sai wani abin da zai kawar da hakan ya bayyana maka, kada ka yi mummunan zato ga duk wani kalami da ya fito daga dan’uwanka, matukar za ka iya ba shi wata fassara ta alheri[28]”.

CIKAKKUN MISALAN ADALCI CIKIN AL’UMMA

Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) sun jaddada jaddadawa mai karfi kan aiwatar da adalci cikin alaka ta zamantakewa tsakanin al’umma, saboda irin muhimmancin da hakan ke da shi wajen ginin al’umma.

A nan za mu yi ishara da wasu daga cikin misalan da ke nuni da hakan:

a)- Ganawa

Shari’a ta hana ganawa da yin magana kasa-kasa ko kebancewa tsakanin mutane biyu matukar akwai wani mutum na uku a tare da su. Alkur’ani mai girma ya aibata wannan aiki a kan wasu mutane da suka koma yin hakan bayan ya hane su ga hakan: “Ashe ba ka ga wadanda aka hane su ba daga ganawar, sa’an nan suna koma wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma suna ganawa game da zunubi da zalunci da saba wa Manzon Allah…[29]”.

An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani ingantaccen hadisi yana cewa: “Idan har mutane uku suka kasance waje guda, kada biyu daga cikinsu su kebance (ganawa) ba tare da na ukun ba, saboda akwai cutarwa da bacin rai cikin hakan gare shi[30]”.

b)– Karkasa Lokaci

Yana da kyau idan mutum yana magana da mutane ko kuma yana zaune da su da ya karkasa lokacin tsakaninsu daidai wa daida. An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance ya kan raba lokacinsa tsakanin sahabbansa, ya kan dubi wannan da wancan daidai wa daida. Ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) bai taba mike kafafunsa tsakanin sahabbansa ba, idan kuma zai gaisa da mutum, Manzon Allah (s.a.w.a) ba ya janye hannunsa daga hannun mutumin har sai idan shi ne ya janye, saboda haka idan mutum ya gaisa da shi sai ya janye hannunsa daga nasa[31]”.

c)– Nuna Rashin Amincewa Cikin Magana

Nuna rashin amincewa da katse mutum yayin da yake magana bai kamata ba. Kulayni, ta hanyar da aka sani, ya ruwaito Abi Abdillah al-Sadik (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Wanda ya katse dan’uwansa musulmi da ke magana a tsakiyar maganarsa tamkar ya kwarzane fuskarsa ne[32]”.


[1] . Wasa’il al-Shi’a 8:587, hadisi na 1.



back 1 2 3 4 5 6 7 next