Wuce Gona Da Iri



MISDAKIN ZALUNCI DA WUCE GONA DA IRI

A bangaren zaluntar mutane da wuce gona da iri a kansu, shari’a, kamar yadda aka ruwaito cikin wasu hadisan Ahlulbaiti (a.s), ta bayyanar da wasu abubuwa da ke nuni da hakan, ta hanyar fadaddiyar fahimtar dan’Adam ga batun adalci da zalunci, ta yadda aka ba wa mutum iko da karfi da za su sanya shi mu’amala ta musamman cikin alakarsa ta zamantakewa da sauran mutane da ba shi damar aiwatar da ayyuka masu yawa. A nan za mu yi ishara da wasu daga cikinsu:

a)– Kashe Musulmi da Cutar da Shi

Daga cikin hakan har da kashe musulmi, ko cutar da shi, ko kuma tsoratar da shi ko da kuwa da kalmomi ne ko kallo na ido, haka nan kuma taimakawa wajen aiwatar da wadannan ayyuka. Ga wasu daga cikin ingantattun ruwayoyi da hadisai da suka yi magana kan hakan:

Daga Hisham bn Salim yana cewa: Na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: “Allah Madaukakin Sarki na cewa: Ya shirya yaki da Ni duk wanda ya cutar da bawaNa mumini, sannan kuma zai aminta daga fushiNa duk wanda ya mutumta bawaNa mumini[1]”.

Daga Hammad bn Usman daga Abi Abdillah (a.s) ko kuma wanda ya ambaci hakan daga gare shi yana cewa: “Ranar Kiyama wani mutum zai zo wa wani mutum har ya cika da jininsa, alhali mutane suna cikin hisabi, sai ya ce: Ya bawan Allah, me ya hada ni da kai? Sai ya ce: ka taimaka a kaina a ranar kaza da kaza har aka kashe ni[2]”.

Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Za a tashi wani mutum a Ranar Kiyama alhali yana zuban jini, za a mika masa wani abu mai kama da kofi ko makamancin haka, a ce masa: wannan shi ne rabonka na jinin wane, sai ya ce: Ya Ubangiji ai kasan cewa Ka dauki raina ba tare da na zubar da jinin wani ba, sai Ya ce masa: haka ne, amma ba ka ji kaza da kaza daga wajen wane dan wane ba ka gaya wa wane ba har suka same wane suka kashe shi, to wannan shi ne rabonka na jininsa[3]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Duk wanda ya kalli mumini don tsoratar da shi, to Allah Zai tsoratar da shi a ranar da babu wata inuwa in ba taSa ba[4]”.

b)– Cin Mutumcin Musulmi

Daga cikinsu har da cin mutumcin mumini ko wulakanta shi ko mai kashin hakan kuwa. Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Lokacin da aka yi Isra'i da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: mene ne matsayin mumini a wajenka? Sai Ya ce masa: Ya Muhammadu, duk wanda ya ci mutumcin wani waliyiNa, to hakika (kamar) ya fito ne don yaka ta, ni kuwa ni ne mafi saurin abin da zai taimakawa waliyaiNa[5]”.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Babu wani mumini da zai wofantar da dan’uwansa alhali yana da halin taimaka masa face Allah Ya wofantar da shi duniya da lahira[6]”.

c)– Wulakanta Mumini

Daga ciki har da wulakanta mumini ko kaskantar da shi. Daga Mu’alla bn Khunais, daga Abi Abdillah (a.s) ya ce: “Na ji shi yana cewa: Allah Madaukakin Sarki Ya ce: Duk wanda ya wulakanta bawaNa mumini to ya yi shirin yaki da Ni, haka nan wanda ya mutumta bawaNa mumini ya yi shirin samun aminciNa[7]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ubangijina ya yi Isra'i da ni kuma Yayi min wahayi da abin da Ya yi min wahayi da shi, Ya gaya min cewa: Ya Muhammadu, duk wanda ya wulakanta min wani waliyiNa to lalle ya kiraye Ni zuwa ga yaki, duk kuwa wanda ya yake Ni lalle Zan yake shi. Sai na ce: Ya Ubangiji, wane ne wannan waliyi naKa? Don nasan za Ka yaki duk wanda ya yake Ka, sai Ya ce: Wancan da na karbi alkawarinsa gare ka da wasiyinka da kuma zuriyarku wajen biyayya[8]”.



1 2 3 4 5 6 7 next