Ladubban Zamantakewa



Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Idan madaukakin al’umma ya zo muku, ku girmama shi[27]”.

Cikin wata ruwaya, an fassara sharif (madaukaki) da mai kudi, ma’abucin kyawawan dabi’u da karimci da tsoron Allah[28].

Wannan hukumci ma ya kasance cikakke da ya hada komai da komai, an ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani hadisi abin dogara yana cewa: “Wanda ya karrama dan’uwansa musulmi da yazo wajensa, to ya karrama Ubangiji Madaukaki ne[29]”.

KiranMutum da Mafi Kyaun Sunan da Ya Fi So

c) – Kiran mutum da mafi kyaun sunan da yake da shi, da kuma kiransa da alkunyarsa idan yana nan, saboda akwai girmamawa cikin hakan da kuma nuna soyayya gare shi.

Kulayni ya ruwaito daga Abil Hasan (a.s) ta hanya abin dogaro yana cewa: “Idan mutum yana nan ka kira shi da (sunan) alkunyarsa, idan kuwa ba ya nan a kira shi da sunansa”.

Mai yiyuwa wannan bambanci saboda la’akari da cewa shi suna yana bayanin mai sunan ne cikakken bayani, saboda haka a lokacin da ba ya nan ne yake bukatuwa da cikakken bayanin kansa, sabanin idan yana nan saboda kasantuwarsa ita kanta bayani ne gare shi.

A baya mun kawo hadisi daga Imam Sadik (a.s) inda yake cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Abubuwa uku suna nuni da kaunar mutum ga dan’uwansa musulmi: zai tarbe shi da sakin fuska da murmushi a lokacin da ya hadu da shi, zai buda masa wajen zama idan ya zauna kusa da shi, sannan kuma zai kira shi da mafi kyaun sunan da yafi so”.

An ruwaito cewa Ma’aikin Allah (s.a.w.a) ya kasance ya kan kira sahabbansa da alkunyarsu don girmama su da janyo zukatansu, ya kan sanya alkunya ga wadanda ba su da ita, sai a dinga kiranu da wannan alkunyar da ya sa musu.

Haka nan ya kan sanya alkunya ga matan da suke da ‘ya’ya da ma wadanda ba su da shi, hakan kananan yara, ta hakan ya kan faranta musu rai.

An ruwaito cewa wata rana Umar ya ce wa Suhaib: “Me ya sa ake kiranka da alkunya alhali ba ka da da”, sai ya ce: “Manzo ne ya sanya min wannan alkunya ta Abu Yahya”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next