Nuna Kauna Ga Mutane



NA HUDU: KYAKKYAWAR DABI’A DA NUNA KAUNA GA MUTANE

A baya yayin da muke magana asasai da ka’idoji mun bayyana cewar kyakkyawar dabi’a da kauna jama’a na a matsayin asasin tafarkin budaddiyar tunani a bangare guda, a bangare guda kuma yana a matsayin abin da alakoki suka kumsa na kyawawan dabi’u, wanda shi ne soyayya, a karshe ma wannan soyayya za ta iya zama imani da addini da akida idan ta kasance saboda Allah ne, kamar yadda daman hakan shi ne abin da ake so.

A baya mun yi nuni da wasu nassosi da ke karin bayani da kuma jaddada wannan asasi na alaka ta zamantakewa.

Mai yiyuwa ne ma a sake samu wannan hakika a wani bangaren na daban a bangaren alaka ta gaba daya, kamar abin da aka riga da aka yi nuni da shi a babin budaddiyar tunani na cewa takurawa mutane ya kan haifar da kiyayyarsu, haka nana bin da aka ruwaito na hana musu da husuma, ko kuma gargadi kan kiyayya ga mutum.

MuminiMai Saukin Kai Ne

Baya ga hakan, za mu iya ganin Ahlulbaiti (a.s) suna jaddada wannan batu da kwadaitarwa kan mumini ya kasance ma’abucin saukin kai da tausasawa a alakarsa ta zamantakewa da sauran mutane.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) cikin wani hadisi abin dogaro yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ashe ba zan ba ku labarin mutumin da wuta ta haramta masa ba a gobe (kiyama)? Sai suka ce: Na’am Ya Rasulallah!, sai ya ce: makusanci mai saukin kai da tausasawa[1]”.

Akwai wasu hadisai na daban da suka jaddada hakan, kamar abin da aka ruwaito cikin wani hadisi cewa: “Mumini mai saukin kai da tausasawa ne, tamkar rakuma dubu da aka daure su waje guda, …..[2]”.

Dukkan wadannan a bangaren alaka ce ta zamantakewa, amma a bangare alaka ta siyasa ko kuma wajen kula da wajibin da ya hau kansa ko kuma alkawurra da yarjejeniyoyi ko imani da akidarsa, a nan ana bukatarsa ya kasance mumini mai karfin hali da tsayawa kyam da rashin sassauci. Don haka ya zama dole mu hada tsakanin tausasawa cikin alaka ta zamantakewa da kuma karfi da rashin sassauci cikin asasi na imani da akida.

Abin da ruwaito cikin wani hadisi da ke siffanta mumini da sakin fuska da kyautatuwar zama na tabbatar da hakan. An ruwaito cikin hadisi cewa: “Aikata ayyukan alheri da kyakkyawar dabi’a na janyo so da kauna, kuma suna shigarwa Aljanna, rowa da turbune fuska yana nesanta (mutum) daga Allah, da shigarwa cikin wuta[3]”.

Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Wani mutumi ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce masa: Ya Rasulallah! Ka yi min wasiyya, daga cikin abin da ya yi masa wasiyya da shi har da cewa: ka fuskanci dan’uwanka da sakakkiyar fuska[4]”.

Daga Hasan bn Husain ya ce: Na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ya Bani Abdul Mutallib, kada ku yi kokarin samun kan mutane da dukiyarku, ku fuskance su da sakakkiyar fuska da kyawawan dabi’u[5]”.



1 2 3 4 5 6 7 next