Adalci Da Daidaitawa



Haka kamar amsa sallama ne da kamarsa ko kuma abin da ya fi shi, kamar yadda ke cewa: ﴾ وَإِذَا حُيِّيْتُم بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّواْ بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ﴿ “Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta ko kuwa ku mayar da ita[13]”.

Akwai hadisai masu tsarki da suka zo da jaddadawa kan batun sakayayya da alheri.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) yana cewa: duk wanda ya saka da gwargwadon abin da aka yi masa, hakika ya mayar da abin da aka yi masa ne, idan kuwa ya rubanya shi ya kasance godiya, wanda ya gode ya zama karimi, duk wanda ya san cewa duk abin da ya aikata ya aikata ne ga kansa ba zai yi saibi ba wajen gode wa mutane, ba zai ki bukatarsu su kara cikin kaunarsu ba, kada ka roki waninka godiya kan abin da ka yi wa kanka, ka kuma kare mutumcinka. Ka san cewa wanda ke bukatar wani abu a wajenka ba zai karamta fuskansa daga fuskanka ba, don haka ka karamta fuskarka daga mayar masa[14]”.

Daga Aliyu bn Salim yana cewa: “Na ji Aba Abdullah (a.s) yana cewa: Akwai wata aya da aka rubutata sai na ce: wace aya kenan? Sai ya ce: ﴾ هَلْ جَزَاء الإحْسَانِ إلا الإحْسَان ﴿ da ta hau kan mumini da kafiri, mai da’a da fajiri; duk wanda aka yi masa wani abu na alheri to ya saka da shi, sai sakawar ba ita ce ya mayar da abin da aka yi masa ba, face dai ya ga cewa wanda ya aikata masa hakan yana da falalar farawa[15]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Allah Ya la’anci mai tare hanyar alheri! Sai aka ce masa wane ne kuma mai tare hanyar alheri? Sai ya ce: shi ne wanda aka aikata alheri gare shi amma ya kafirce wa hakan, ya kuma hana mai aikata alherin aikata shi ga waninsa[16]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: duk wanda aka yi masa alheri ya saka da shi, idan kuwa ba zai iya ba to ya gode da shi, idan kuwa bai aikata haka ba to ya kafirce wa ni’ima[17]”.

b) – Mayar da Hakkoki

Daga cikin hakan har da mutum ya san hakkin dan’uwansa kamar yadda dan’uwan nasa ya san hakkinsa, saboda hakkoki tsakanin muminai abu ne na musanye, kamar yadda za mu iya ganin hakan cikin wasu hadisai da aka ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) kan hakkin mumini. Daga ciki har da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Ashe ba zai kasance abin kunya ba ga wani daga cikinku idan makwabcinsa ya san (kiyaye) hakkinsa, amma shi bai san hakkin makwabcin nasa ba[18]”.

c) – Shagaltuwa da Aibin Kai da Mantawa da Aibin Wasu

Daga cikin hakan har da shagaltuwa da aibin mutum da kokarin gyaransa da kuma rufe ido kan aibobin sauran mutane. An ruwaito Abu Ja’afar al-Bakir (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Siffofi uku, duk wanda ke da su ko kuma guda daga cikinsu zai kasance karkashin inuwar al’arshin Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa: mutumin da ya ba biya wa mutane bukatunsu alhali yana bukatuwa da abin, da mutumin da bai taba gabatar da wani mutum ko jinkintar da wani ba har sai ya san akwai yardar Allah cikin hakan da kuma mutumin da bai taba aibanta dan’uwansa musulmi kan wani aibi ba har sai ya kawar da wannan aibi daga jikinsa, saboda ba zai kawar da wani aibi ba sai ya sake ganin wani aibin, ya isar wa mutum ya shagaltu da kansa daga mutane[19]”.



back 1 2 3 4 5 next