Adalci Da Daidaitawa



NA UKU: ADALCI DA DAIDAITAWA

A baya yayin da muke magana kan wannan batu mun bayyana cewar sun samo asali ne daga akidar wajibcin adalci da haramcin zalunci, da kuma cewa mafi bayyanar misdakin adalci cikin alaka ta zamantakewa shi ne daidaitawar mutum a kan kansa.

Haramcin Zalunci

Haramcin zalunci bai takaita kawai ga mutum ya aikata (wani aiki na) zalunci ba, face dai dole matsayar mutum ta kasance mai kin zalunci ne a dukkan bangarori. Muna iya ganin hakan cikin wadannan al’amurra masu zuwa:

a)– Mayar da Abin Da Kwace

Idan wani ya zalunci wani mutum na daban, misali ya kwace masa dukiyarsa, ko kuma ya kwace ko take masa wani hakki daga cikin hakkoki, idan daga baya ya tuba, to dole ne ya mayar da abin da ya kwace daga wajen mutumin da ya zalunta, wannan shi ne ake kira da ‘mayar da abin da aka kwace (zalunta).

Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Zalunci uku ne: zaluncin da Allah ke yafewa (gafatarwa), da zaluncin da Allah ba Ya yafe shi, sai kuma zaluncin da Allah ba Ya barinsa. Zaluncin da Allah bai yafe shi, shi ne shirka, shi kuwa zaluncin da Allah ke yafe shi, shi ne zaluncin da mutum ke yi wa kansa cikin abin da ke tsakaninsa da Allah, amma zaluncin da Allah bai barinsa shi ne zaluncin da mutum ya yi wa sauran mutane[1]”.

Daga Wahab bn Abdur-Rab, da Ubaidullah al-Tawil, daga wani dattijo daga dattawan al-Nakh’ yana cewa: “Na gaya wa Abi Ja’afar (a.s): Na kasance gwamna tun lokacin Hajjaj har zuwa yau din nan, shin zan iya tuba (za a iya karbar tuba ta)?, sai ya ce: sai Imam ya yi shiru, sai na sake masa wannan tambaya sai ya ce: A’a, har sai ka mayar wa masu hakki hakkokinsu (da ka take)[2]”.

Daga Abi Basir yana cewa: “Na ji Aba Abdullah yana cewa: Duk wanda ya ci dukiyar dan’uwansa cikin zalunci kuma bai mayar masa ba, to ya ci garwashin wuta a Ranar Kiyama[3]”.

Haka nan idan ya zalunci wani zalunci na ma’anawiyya kamar giba (cin nama – yi da wani a bayansa), cin mutumci, kazafi da dai sauransu da za mu ambato su nan gaba, don haka ya zama dole ya yi kokarin mayar da wannan hakki tare da neman gafara daga wadanda ya zalunta – bayan neman gafara daga wajen Ubangiji Madaukaki – da neman gafara da ayyuka na kwarai gare su da mutumta su da dai sauran abubuwan da ake daukansu a matsayin mayar da hakki ga wadanda aka kwace.

b)– Shiriya Bayan Bata

Mai yiyuwa daya daga cikin mafi bayyana da girman nau’in zalunci na ruhi ga sauran mutane shi ne batar da su daga hanya madaidaiciya da tura su zuwa ga bata, idan har mutum ya gano haka ya kuma tuba, to dole ne ya yi kokarin shiryar da su zuwa ga gaskiya da komar da su zuwa gare ta.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Akwai wani mutum a zamanin farko da ya nemi duniya ta hanyar halal amma bai samu ba, ya nema ta ta haramun bai samu ba, sai Shaidan ya zo masa ya ce: Ashe ba zan nuna maka wani abin da za ka iya samun duniya da shi ba, sannan kuma ka kara yawan nemanka? Sai ya ce: Na’am, sai ya ce masa: Ka bi duniya da kuma kiran mutane zuwa gare ta, sai ya aikata hakan jama’a kuma suka bi shi, ya kuma samu duniya, daga baya sai ya yi tunani yana mai cewa: shin me na aikata ne? na kirkiro wasu abubuwa na duniya na kuma kira mutane zuwa gare ta, babu lokacin da zan so tuba face sai wani daga cikin wadanda na kira ya zo ya mayar da ni, ta yadda har ya kan je wa mutanen da ya kiraye su yana ce musu: abin nan da na kiraye ku gare shi karya ce, ni na kirkire shi, su kuwa sai su ce masa: ina, karya kake yi gaskiya ce, face dai kai ne ka ke cikin shakku kan abin da kake kai, sai watse su bar shi. Lokacin da ya ga haka sai ya ya nemo sarka ya daure wuyansa da ita, yana cewa: ba zan taba kunce ta ba har sai Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mini. Sai Allah Ya yi wahayi wa daya daga cikin AnnabawanSa Ya ce masa: Ka gaya wa wane cewa: Da daukakaTa da za ka ci gaba da rokona har…ya yayyanke ba Zan gafarta maka ba har sai ka dawo da wanda ya mutu a kan abin da ka kiraye shi gare shi da dawo daga wannan tafarki[4]”.

c)– Taimakon Zalunci

Kamar yadda ya haramta mutum ya aikata zalunci da kansa, haka nan ya haramta masa ya taimakawa azzalumi cikin zaluncinsa, ko kuma ya kasance daga cikin masu taimakon azzalumai bisa fahimtar da mahangar al’umma.



1 2 3 4 5 next