Koyarwar Ahlul Baiti (A.S)



Ba makawa cewa daya daga manyan hadafofi masu muhimmanci na samuwar imamai (A.S) da kuma bayaninsu game da sakon karshe shi ne jagorancin musulunci da kuma isar da shi zuwa ga daraja madaukakiya na kamala, kamar yadda muka san haka tun farko a wannan bahasi[2]. Ta yadda ya zama yana daga tsarin ubangiji ga wannan sako ya zama ya kai tsarin musulunci zuwa ga daraja ta kamala da ta dace da shi a tsawon lokaci da yake jibantar hukunci da jagorancin da yake al’amari ne da ake iya samun hakikaninsa da siffantuwa da shi ga imamai ma’asumai goma sha biyu (A.S)

wanda a mafi karancin kaddarawa za a iya kwatanta shi da tsawon lokaci da rayuwarsu ta dauka har karni uku idan mun yi la’akari da mafi karancin shekarun imamai goma sha biyu (A.S).

wannan kamalar zata iya yiwuwa a kaddara ta a kan dukkan matsayi na tarbiyya da ilimi, ko kuma a matsayin hukunci da alaka da tsari, da kuma matsayin arziki da cigaban tattalin arziki, da kuma lamuni da daukar nauyin tafiyar da rayuwar zamantakewar al’umma, da kuma karfin soja, da yaduwar da’awar musulunci da kuma wayewar musulmi a sasanni daban-daban na duniya, da makamantansu a sha’anonin rayuwa na danadamtaka, ta yadda zai zama hakikanin gasgatawa ga fadinsa madaukakin sarik: “Domin ya ci nasara a kan addini dukkaninsa koda kuwa mushrikai sun ki[3]“.

 Nesantar da Ahlul Baiti (A.S) daga wannan matsayin na asali –da ya bayar da dama ga mummunan ijtihadi na kuskure da son rai na da kin gaskiya na ‘yan siyasa- ya sabbaba wannan cibaya da rushewar al’umma da mummunan matsayi da rayuwar da musulmi suke akai, kai har ma da rayuwar da danadam ya yi ta tun farko har zuwa lokutan da suka rigaya. Kuma mutum ne ya jawo hakan kamar yadda shi ne ya jawo faruwar wannan al’amura a dukkan lokutan da a kan samu fuskantar rushewa da ci baya a tsawon tarihin dan Adam. Tun lokacin da Allah ya halicci Annabi Adam (A.S) ya sanya shi da shi da matarsa a aljanna, da ma sauran wurare da aka yi magana game da sauran sakonnin annabawa (A.S) yayin da dan Adam ya ki amsa wa sakonsu da kiransu na addini: “Mutane sun kasance al’umma daya sai Allah ya aiko annabawa masu albihsir da gargadi ya kuma saukar da littafi da gaskiya tare da su domin su yi hukunci tsakanin mutane a cikin abin da suka saba, babi wannan ya saba sai wadannan da aka zo musu da shi bayan hujjoji sun zo musu don zalunci daga garesu sai Allah ya shiryar da wadanda suka yi imani ga abin da suka saba a cikinsa na gaskiya da izininsa Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga tafarki madaidaici”[4]

Imamai (A.S) sun yi kokari su mayar da gaskiya zuwa ga wajan da ya dace da ita, suka kuma yi shiri domin karbar jagorancin musulunci bayan an nesantar da su daga gareshi bayan wafatin manzo (S.A.W). daya daga cikin dalilin wannan shirin shi ne gina al’ummar musulmi saliha ta gari da zata iya zama muhimmiyar gudummuwa da zata iya bayarwa wajan jagorancin musulmi.

Zai iya yiwuwa mu yi la’akari a bayyane ta hanyar karanta wannan marhala da imamai uku na farko Ali, Hasan, da Husaini[5] (A.S) suka rayu a cikinta, ta yadda ya zama sun yi kokarin karbar jagorancin al’umma bisa hadafin kai al’ummar musulmi zuwa ga wancan matsayi na wannan marhala ta hanyar bayani na siyasa da jagorancin al’umma.

Kuma imam Ali (A.S) ya samu dama a aikace ta hanyar kai wa ga wannan matsayi na jagoranci, ya ci gaba da jagoranci na wani dan lokaci gajere zuwa ga rayuwar imam Hasan (A.S) sannan sai musulmi suka zama suna da burin komawa zuwa ga lokacin da ya gabata a zamanin imam Husaini (A.S) suka nemi ya zo domin tsayuwa da wannan aiki na jagoranci har shi ne aka samu faruwar al’amarin karbala mai ban tsoro da bakin ciki.

Ba makawa wadannan zababbu na gari da imam Ali (A.S) ya samu damar tarbiyyatarwa da gina kyawawan dabi’u, da kuma tsari garesu, kuma suka yi yaki tare da shi, suka bayar da gudummuwa mai girma a wajan hidimar musulunci da kuma tabbatar da kyawawan dabi’u da ya yi kira zuwa garesu (A.S).

Hakan nan abin da imam Hasan ya tsayu da shi na kariya garesu yayin da ya zama daya daga hadafin sulhunsa mai muhimmanci tare da mu’awiya wato shi ne kariya ga wannan al’umma ta gari.

Hakika wadannan mutane na gari suna da rawa da suka taka mai karfi a zamanin imam Husaini (A.S) yayin da suka iya karya jumudin wannan al’umam da halin mika wuya ga hukuncin umawiyawa, da kuma bayar da dalili na asasi da nau’in zamantakewa na motsawar imam Husaini (A.S) wacce ta dauki shi’arin saryar (kifar) da gwamnatin umayyawa, ta kuma dauki alwashin rushe shi da kuma samar da damar tashin juyin-juya-hali da gwagwarmayar imam Husaini (A.S) mai fadi da yalwar tasiri a tsaka-tsakin al’ummar musulmi, ya kuma zama fikira da tunani mai tasriri a tarihin musulunci, kuma da yawa daga hadafofin wannan tashi sun tabbata, daga cikinsu akwai kayar da hukuncin umayyawa a karshen lokaci.

A marhala ta imaman farko uku zai iya yiwuwa a ce: Hadafin farko kuma mafi muhimmanci na gina jama’a ta gari shi ne bayar da gudummuwa wajan aikin samuwar jagornci na musulunci, wanda ake da burin samuwarsa yana mai dacewa da ayyukan da imamai goma sha biyu suka aiwatar domin kiyaye wa ga al’ummar musulmi a zamaninta na farko, wanda shi ne tsayar da shari’ar muslunci, daidai ne a matsayin samuwarta ta zahiri ta wannan hukumar musulunci da ta faru a dan wani lokaci a hannun imamai, ko kuma a matsayin nazari da tunani: yayain da imamai suka samar da tunani a cikin al’umma da yake kira domin tsayar da wannan hukuma ta yadda ya zama daya daga cikin matsi da aka samu domin kawo gyara ga hanyar tababatar da hukumar musulunci a tarihin musulunci.



[1] - A koma wa littafin Asshi’a wat’tashayyu’u na Shahid da ana nan kan shirin buga shi.

[2] - Wannan bayani ya zo a bahasin imamanci kashi na daya: Nazari.

[3] - Attauba: 33.

[4] - bakara: 213.

[5] - Imam Husain (A.S) ya san ba zai kai ga samun shugabanci ba, amma hadafinsa shi ne bayyana matsayinsa na siyasa, wannan kuma shi ne aikin da ya hau kansa na shari’a, da kuma yanayi yake tilasta masa shi, duk da hadafinsa na asali shi ne wani abu daban da zamu ambace su yayin bincike game da tarihin matakan imamai a babi na biyar.

 



back 1 2