Kyawawan Halaye



Mafi muhimmanci shi ne kariya ga addini da mazajen Shi’a suka yi ta hanyar shiryarwar Ahlul Baiti (A.S) wajan fuskantar barazanar nan ta masu musun samuwar Allah da zindikai, ko kuma fuskantar bacewa da gurbacewar dabi’u da ya game dukkan sasannin duniyar musulmi a Madina da Makka da Kufa da Basar da Sham da Bagdad da sauransu, har ya bayyan a sarari ta hanyar tattaunawa da bayani da makarantu da mabiya Ahlul Baiti (A.S) suka assasa da dabi’u da suka siffantu da su, da kuma dauki-ba-dadinsu da dukkan lalacewa da fasadi da zalunci[4].

2-Samar Da Jagoranci Na Gari

Gabatar da jagoranci na gari ta hanyar jama’a ta gari a cikin al’ummar musulmi wanda ya kasance a zamanin da da amfani na kashin kai ya kusa ya zama ya mamaye ya kuma yi galaba a kan amfanin al’umma gaba daya, maslahar mutum daya sai tafi karfin maslahar musulunci da mAbuyansa gaba daya, aka sayi zukata da harsunan mutane kuma aka yi kasuwanci da addini da hadisin Annabi (S.A.W) domin gyara dukkan nau’in tasarrufi da aiki karkatacce da barnar mahukunta da shugabanni da jagororin yaki da wazirai karkatattu suke aikatawa musamman a lokacin hukumar umayyawa.

Ahlul Baiti (A.S) sun himmantu da wannan al’amari matuka har sai da imam sadik ya kira shi’arsa su zama koyi na gari a aikace tsakanin msusulmi domin kiyayewa ga al’ummar musulmi ta wani bangare, da kuma shiryar da su zuwa tafrki madaidaici ta wani bangaren.

Kulaini ya rawaito da sanadi sahihi daga Safwarn dan Yahaya daga Abu Usama Zaid Asshaham ya ce: (Abu Abdullahi ya ce da ni: “Ka gaya (isar) wa wanda kake ganin yana bi na daga cikinsu yana kuma karbar zancena sallama, kuma ina yi muku wasiyya da tsoron Allah madaukaki mai girma, da tsantseni a cikin addininku, da kokarin bin Allah, da gaskiyar zance, da rikon amana, da tsawaita sujjada, da kyawon makwabtaka, da wannan ne Muhammad (S.A.W) ya zo, da kuma bayar da amana ga wanda ya ba ka na gari ne ko fajiri, domin manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana umarta da mayar da (amanar) zare da allura. Ku sadar da zumuncin al’ummarku, ku halarci zanajarsu, ku gaida marasa lafiyarsu, ku bayar da hakkokinsu, hakika namiji daga cikinku idan ya yi biyayya a addini da tsentseni ya yi gaskiya a magana ya kuma bayar da amana ya kyautata dabi’a tare da mutane sai su ce wannna Ja’afari ne, sai wannan ya faranta mini rai ya sa ni farin ciki, sai a ce wannan tarbiyyar Ja’afar ce, idan kuma ya kasance ba haka ba sai bala’insa da aikbinsa ya same ni, sai a ce wannan tarbiyyatarwar Ja’afar ce, wallahi babana ya ba ni labari cewa mutum yana kasancewa a kAbula daga shi’ar Ali (A.S) sai ya zama shi ne adonta, ya fi kowa rikon amana, da kuma mafificinsu hukunci da gaskiya, mafi gaskiyarsu zance, shi a ke ba wa wasiyyoyi da ajiya, sai ka ga ana tambayar kabila game da shi sai su ce: Ai babu kamar wane?! hakika shi mai amana ne, mafificinmu gaskiyar magana[5].

Fakara ta karshe a wannan hadisi tana nuna wa a fili wannan muhimmin al’amari da mabiya Ahlul Baiti (A.S) suka tabbatar da shi cikin abin da ake rawaitowa daga imam Sadik daga babansa imam Bakir (A.S)[6].



[1] - Wannan sharadi an sanya shi ne domin ya zama sabuwar ka’ida a cikin al’ummar musulmi, wato mayar da tafarkin shaihaini ya koma yana da tsarki da zai yi daidai da sunnar annabi (S.A.W) shi kansa, wannnan kuma abu ne da imam Ali (A.S) ba zai taba karbarsa ba, haka nan ma ahlul bait (A.S) da kuma jama’ar da suka yi imani da wilayarsa da shugabancinsa.

[2]- Ma’alimul madarasataini\ 1: 477-484. Yana ciratowa daga Nahajul Balaga sharhin Ibn Abil Hadid 4: 8-9. Tahkikin Muhammad Abul fadl Ibrahim;

[3] - Zamu iya fahimtar muhimmancin samar da jama’a ta gari wajan karbar shugabanci ta hanyar fahimtar nazarin Ahlul Baiti (A.S) ga al’amarin jagoranci.

[4] - Zamu yi littafi na musamman game da sanin wannan dalla-dalla.

[5]- Alwasa’il 8: 398, J2.

[6]- Karin bayani zai zo game da wannan a bahasin Kyawawan dabi’u da tsarin zamantakewa.

 



back 1 2