Yin Magiya



Amsar wannan tambaya kuwa dole ne mu koma zuwa ga ruwayoyi da tarihin rayuwar rayuwar Manzo da ta iyalansa (a.s) a nan zamu bayar da dalilai da suke tabbatar da halascin wannan al’amari na hada Allah da bayinsa na kwarai.

1-A cikin addu’ar da Manzo ya koyar da wani makaho, wacce a baya muka yi magana a kanta, a cikin wannan addu’a munga yadda aka hada Allah da manzonsa, domin kuwa ga abin da Manzo ya ce masa: ka yi alwala sannan ka yi salla raka’a biyu sai ka karanta wannan addu’ar kamar haka: “Allahumma inni as’aluka wa atawajjahu ilaika bi nabiyyika Muhammadin nabiyyir rahama”. Wato “Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantarka da manzonka Muhammad annabin rahama”. A cikin wannan hadisi zamu ga yadda Manzo ya koyar da wannan makaho wannan addu’a yadda a fili yake hada Allah da manzonsa kan ya biya masa bukatarsa. Idan har hada Allah da bayinsa na kwarai ya haramta, shin Manzo zai koyar da wannan makaho addu’a kamar haka?

2-Abu Sa’id khudri ya ruwaito daga Manzo (s.a.w) yana cewa: Duk wanda ya fita daga gidansa zuwa masallaci domin ya yi salla sai ya karanta wannan addu’a Allah zai yi masa kulawa ta musamman sannn mala’iku dubu saba’in zasu ci gaba da nema masa gafara a wajen Allah, wannan addu’a kuwa ita ce kamar haka: “Allhumma inni as’aluka bi hakkis sa’ilina alaika, wa as’aluka bi hakki mash’yaya haza.. “[2]

Ma’anar wannan addu’a kuwa shi ne kamar haka; “Ya Allah ina rokonka albkarcin wadanda suke rokonka, kuma ina rokonka da albarkacin wannan tafiya tawa…”

Mai yiwuwa wasu su ce ai wannan hadisi mai rauni ne, wato su ce a cikin danganen hadisi a kwai Atiyya Aufi, alhalin laifinsa kawai shi ne ya kasance masoyin iyalan gidan Manzo ne, Sannan kuma Ibn khazima ya ruwaito wannan hadisi a cikin sahihi dinsa ta ingantacciyar hanya a wajen AhlusSunna. [3]

3-Umar Bn khattab yana ruwaitowa daga Manzo (s.a.w) inda yake cewa: Lokacin da annabi Adam ya yi kuskure (bai aikata abin da ya kamata ya yi ba) sai ya fuskanci Ubangiji yana cewa: Ya ubangijina, ina rokonka albarkacin manzoka muhammad da ka gafarta mini”Sai Allah madaukaki ya ce masa Ya Adam ta yaya ka san Muhamma duk da cewa ban halicce shi ba, sai Adam ya ce masa: Ya Allah lokacin da halitta ni ka hura mini rai sai na daga kaina a sama, sai na ga an rubuta “La’ilaha illallahu’muhammad rasulullah” a kan kafar al’arshi, sai na san cewa lallai ba zaka hada sunanka da na wani ba sai wanda ya fi soyuwa gareka a cikin halittu…[4]

Babu wata matsala dangane da danganen wannan hadisi ko kadan, domin kuwa mustadrikul Hakim wanda aka ruwaito wannan ruwaya daga gareshi matsayinsa kamar matsayin sahihi Bukhari da Muslim yake.

Wadannan su ne ruwayoyin da suka bayyanar da tarihin tsayuwar Manzo (s.a.w) Sannan idan muka koma zuwa ga addu’o’in da suka zo mana daga A’immatu Ahlul baiti (a.s) zamu tabbatar da wannan a fili, domin kuwa sun kasance suna rokon Allah da albarcin waliyyansa a kodayaushe. Idan muka koma zuwa ga Sahifa sajjadiyya zamu samu wannan a fili.

4-Imam zainul Abideen (a.s) ga abin da yake cewa yayin da yake munajati da Ubangiji: “Ya Allah albarkacin wanda ka zaba daga cikin bayinka, albarkacin wanda ka zaba don kanka, Ya Allah don albarkacin wadanda ka zaba daga cikin bayinka, Albarcin wadanda ka zaba domin a san matsayinka da su, ya Allah albarkacin wadanda ka hada biyayyarka da tasu, albarkacin wadanda ka sanya adawa da su adawane da kai”.[5]

5- Imama Sadik (a.s) ya je ziyar kakansa Imam Ali (a.s) a Najaf, bayan ya yi gaisuwa ga Imam sai ya fuskanci Allah ya roki Allah shi wasu abubuwa wadanda sun zo a cikin wannan ziyara, a karshen addu’ars ga abin da yake cewa: “Ya Allah ka karbi addu’ata ka kuma karbi yabona. ya Allah ka hada ni tare da waliyaina, albarkacin Muhammad, Ali, Fadima, da Hasan, Da Husaini (a.s)”[6].



back 1 2 3 4 next