Yin Magiya



Yin Magiya;

Hada Allah Da Wasu Bayinsa Na Kwarai Don Neman Biyan Bukata

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Kur’ani yana ambatar wasu gungu Masu hakuri, masu gaskiya, masu wadatar zuci, masu ciyarwa, masu neman gafara da asubahi, ga abin da kur’anin yake cewa: “Kuma masu Hakuri da masu gaskiya da masu bautar Allah da masu bayar da imfaki da masu neman gafarar Ubangiji da asubahi”[1]

Duk wanda ya tashi da tsakiyar dare ya yi sallar nafila ya yi kuka zuwa ga Allah yana mai cewa: “Ya Allah ina rokonka don darajar masu neman gafararka da asubahi, ka gafarta mini zunubbaina”

Hada Allah madaukaki da matsayin wasu daga cikin bayinsa masu kadaita shi, kuma suka nutse a wajen kadaita shi, ta yaya zai zama shirka da Allah a cikin bauta? A bahsimmu na baya mun bayyanar da ma’anar bauta da shirka, muka ce bauta ita ce mutum ya kaskantar da kansa a gaban wani wanda ya dauke shi a matsayin Allah ko kuma ya dauka shi ne yake tafiyar da wasu abubuwa a cikin duniya’ (rububiyya) alhalin wanda yake hada Allah da matsayin annabawa da manyan bayin Allah sam ba shi da wannan akida, domin kuwa ya dauke su a matsayin manyan bayin Allah masu biyayya gare shi, ba alloli ba.

Tare da bayyana hakikanin bangare na farko wato hada Allah madaukaki da wasu daga cikin bayinsa masu biyayya gare shi ba yana nufin bauta ba ne, don haka dole ne mu ba da muhimmanci a cikin bangare na biyu wato yin hakan ya halatta a shari’a ko kuwa? Domin kuwa zai iya yiwuwa wani abu ba bauta ba ne ga wanin Allah amma bai halatta ba a shari’a.



1 2 3 4 next