Sanya Sunan Bawan Husain



Sanya Wa ‘Ya’ya Sunan Da Ya Fara Da “Abd”

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Wani lokaci sakamakon soyayyar mutum ga wani yakan kirakansa da sunan bawansa, wato “Abd ko Gulam”, manufar wannan kuwa shi ne nuna karanta ga wannan mutum da kake girmamawa.

Wani lokaci wasu mutane masu tsarkin zuciya suna tsananin kaunar annabawa da waliyya Allah, sakamakon haka ne suke sanya wa ‘ya’yansu sunan wannan bawan Allah da suke kauna tare da sanya kalmar “Abd” ko “Gulam” a farkon sunan, wato kamar su sanya wa dansu suna da “Gulam Husain” ko “Abudul Husain”. Irin wannan sanya sunan ba shi da wani hadafi wanda ya wuce nuna soyayya ga iyalan gidan manzanci, sannan fahimtar hakan ga wadanda suke da tsarkin zuciya wani abu ne mai sauki kwarai da gaske.

Tare da kula da wannan gajeruwar gabatarwa zamu yi nuni ne da wasu maganganun da wasu masu kiyayya da yin hakan suke cewa kamar haka:

Suna cewa; Ba zai yiwu ba mutum ya zama bawan wani sabanin Allah. Kamar yadda Allah yake cewa: “Lallai duk abin da yake sama da kasa sai ya zo wa Allah mai rahama yana matsayin bawa”.[1]

Tare da lura da cewa mutum kawai zai iya zama bawan Allah ne, don haka irin wannan sanya suna a kira mutum da sunan bawan wani kamar “Abdul Husain” bai halatta ba domin kuwa wannan yana bayar da kanshi na shirka ne!



1 2 next