Rayuwa Bayan Mutuwa 2



 

4-Mutanenn Annabi Nuhu Sun Shiga Cikin Azaba Bayan An Nutsar Da Su A Cikin Ruwa

“Sakamakon kura-kuren da suka yi aka nutsar da su a cikin ruwa, sakamakon haka ne suka shiga a cikin wuta, sannan ba su samu wani ba sabanin Allah wanda zai taimaka musu”. [6]

Mai yiwuwa a yi tunanin cewa mai yiwuwa saboda shigarsu wuta wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa shi ya sa aka yi amfani da shudadden aiki, wato aka ce sai aka shigar da su a cikin wuta. Amma wannan fassara sakamakon rashin dalili a kan yinta kuma ta saba wa zahirin ayar.

Domin kuwa da ana nufin cewa sai ranar kiyama ne zasu shiga cikin wuta, wato tsakanin nutsewarsu da shiga wutar, wato da an yi nuni da hakan kamar a ce; sannan zasu shiga wuta, amma ba a yi nuni da hakan ba.

Sannan kuma dole mu yi tawili a inda ake cewa, “sannan ba su sami wanda zai taimaka musu ba”wato sai mu yi tawili da cewa tunda wannan al’amari haka zai faru shi ya sa aka yi amfani da lokacin da ya wuce a cikin wannan jumla, wannan tawili kuwa ba shi da wani dalili, don haka wannan tawili ba ya inganta a nan.

Saboda haka a nan zamu wadatu da wannan, don mu kauce wa tsawaitawa a kan haka sai mu yi cikakken bayani a inda ya dace.

Rayuwar Barzahu A Cikin Hadisi

Dukkan abin da muka ambata dangane da abin da ya shafi rayuwar barzahu daga Kur’ani mai girma yake, amma a cikin maganganun Manzo da Ma’asumai (a.s) an yi cikakken bayani a kan hakan, wanda a kan haka manene a ka kebance babi-babi a kan bayanin rayuwar barzahu a cikin Littattafan hadisi da na akida. Saboda haka a nan zamu tsakuro wani abu ne daga cikinsu a matsayin misali:

1-Manzo (s.a.w) ya kasance a karshen rayuwarsa yakan ziyarci makabartar baki, sannan yakan yi magana da mutanen da suke rufe a wannan makabarta kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 next