Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma



 â€œAbin da muka fada dangane da wadansu, a kan abin da ya shafi ziyarar shugaban wadanda suka gabata da wadanda zasu zo kuwa da yadda ake yi masa salla dole ne mu fadi abin da ya wuce hakan. Abin da ya dace shi ne mutum tare da kaskantar da kai ya halarci haramin Manzo domin kuwa shi mai ceto wanda ba a mayar da cetonsa. Duk wanda ya tunkare shi ba zai koma ba yana mai yanke kauna ba. Sannan duk wanda ya zo haraminsa yana neman taimakonsa da biyan buakatarsa ba zai rasa abin da yake nema ba. “

 Sannan ya cigaba da cewa: Malamammu (Allah ya gafarta musu) Suna cewa abin ya dace shi ne, wanda ya ziyarci Manzo ya rika jin cewa kamar Manzo yana raye ne ya ziyarce shi. “[8]

6-Ibn Hajar Haitami Makki Shafi’i (ya rasu shekara ta 973) Ya kasance ya yi riko da dalilin da dukkan malamai suka hadu a kansu wajen kafa hujja a kan kasantuwar mustahabbancin ziyarar Manzo. Sannan yana karawa da cewa: Sabawar wani malami guda a kan wandannan dalilai kamar Ibn Taimiyya ba ya cutar da wadannan dalilai da a ka hadu a kan ingancinsu. Domin kuwa malamai da yawa sun bibiyi maganganusa kuma suna rashin ingancinsu. Daya daga cikinsu kuwa shi ne Izz Bn Jama’a ne. Kamar yadda Ibn Hajar yake cewa: “Ibn Taimiyya mutum ne wanda Allah ya batar da shi, Sannan ya sanya masa tufafin kaskanci”. Sannan Sheikh Takiyyuddin Subki wanda dangane da matsayinsa na ilimi kowa ya aminta da shi, littafi na musamman ya rubuta don kalu balantar fatwowiyin Ibn Taimiyya. [9]

7-Muhammad Bn Abdul wahab yana cewa: Mustahabbi ne ziyayar Manzo amma wajibi ne mutum ya yi tafiya zuwa wajen domin ziyara da yin salla a wajen.[10]

8-Abdurrahman Jaziri marubucin littafin nan (Alfikhu Ala Mazahibil Arba’a) Inda kawo fatwowiyin dukkan malaman mazahaba guda hudu na Sunna, yana cewa: Ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan mustahabbai, sannan hadisai sun zo a kan hakan, sannan ya cigaba da kawo hadisai guda shida da suka yi bayanin a kan ziyarar Manzo da ladubbanta. [11]

 Sakamakon cewa duk shugabannin fikhu guda hudu ba su yi wani Karin bayani ba akan abin da aka ambata a sama ba, yana nuna cewa duk malaman wannan zamani suma sun tafi a kan hakan.

9-Shekh Abdul Aziz Bn Baz yana cewa: Duk wanda ya ziyarci Manzo mustahabbi ne ya yi salla raka’a biyu a (radahar Manzo) Sanna ya yi wa Manzo sallama, Sannan mustahabbi ne ya je “Bakiyya”domin ya yi sallama ga shahidan da a ka rufe a wajen. [12]

 A nan zamu takaita da wannan abin da muka kawo dangane da wannan al’amari mai son Karin bayani dangane da haka, sai ya koma zuwa ga “Risalar da muka rubuta a kanhaka a cikin harshen larabci. [13]

 

Ziyarar Kabarin Manzo A Mahangar Kur’ani Da Sunna



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next