Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma



6-Ibn Hajar Haitami Makki Shafi’i (ya rasu shekara ta 973) Ya kasance ya yi riko da dalilin da dukkan malamai suka hadu a kansu wajen kafa hujja a kan kasantuwar mustahabbancin ziyarar Manzo. Sannan yana karawa da cewa: Sabawar wani malami guda a kan wandannan dalilai kamar Ibn Taimiyya ba ya cutar da wadannan dalilai da a ka hadu a kan ingancinsu. Domin kuwa malamai da yawa sun bibiyi maganganusa kuma suna rashin ingancinsu. Daya daga cikinsu kuwa shi ne Izz Bn Jama’a ne. Kamar yadda Ibn Hajar yake cewa: “Ibn Taimiyya mutum ne wanda Allah ya batar da shi, Sannan ya sanya masa tufafin kaskanci”. Sannan Sheikh Takiyyuddin Subki wanda dangane da matsayinsa na ilimi kowa ya aminta da shi, littafi na musamman ya rubuta don kalu balantar fatwowiyin Ibn Taimiyya. [9]

7-Muhammad Bn Abdul wahab yana cewa: Mustahabbi ne ziyayar Manzo amma wajibi ne mutum ya yi tafiya zuwa wajen domin ziyara da yin salla a wajen.[10]

8-Abdurrahman Jaziri marubucin littafin nan (Alfikhu Ala Mazahibil Arba’a) Inda kawo fatwowiyin dukkan malaman mazahaba guda hudu na Sunna, yana cewa: Ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan mustahabbai, sannan hadisai sun zo a kan hakan, sannan ya cigaba da kawo hadisai guda shida da suka yi bayanin a kan ziyarar Manzo da ladubbanta. [11]

 Sakamakon cewa duk shugabannin fikhu guda hudu ba su yi wani Karin bayani ba akan abin da aka ambata a sama ba, yana nuna cewa duk malaman wannan zamani suma sun tafi a kan hakan.

9-Shekh Abdul Aziz Bn Baz yana cewa: Duk wanda ya ziyarci Manzo mustahabbi ne ya yi salla raka’a biyu a (radahar Manzo) Sanna ya yi wa Manzo sallama, Sannan mustahabbi ne ya je “Bakiyya”domin ya yi sallama ga shahidan da a ka rufe a wajen. [12]

 A nan zamu takaita da wannan abin da muka kawo dangane da wannan al’amari mai son Karin bayani dangane da haka, sai ya koma zuwa ga “Risalar da muka rubuta a kanhaka a cikin harshen larabci. [13]

 

Ziyarar Kabarin Manzo A Mahangar Kur’ani Da Sunna

A: A Mahangar Kur’ani Mai girma

 Kur’ani mai girma yana bai wa al'ummar musulmi umarni da su je wajen Manzo su nemi gafararsa sannan su nemi Manzo (s.a.w) don ya nema musu gafarar Allah madaukaki: “Duk lokacin da suka zalunci kawunansu (zunubi) idan suka zo wajen Manzo suka nemi gafa kuma Manzon ya nema musu gafar a wajen Allah, lallai Allah mai rahama ne kuma mai karbar tuba. “[14]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next