Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



 Manzo (s.a.w) Yana kira zuwa ga musulmi da cewa: “Ku ziyarci kaburbura domin suna tuna muku lahira”.

 Sannan a wani hadisi daban yana cewa: “Ku ziyarci makabarta domin akwai darasi a cikin yin hakan. “

 Gaskiya ne wadannan kira tare da lura da yadda aka amfani lamirin maza kamar ya nuna cewa da maza ake, amma kamar yadda muka tunatar cewa kusan dukkan kira da ake yi a cikin Kur’ani da hadisi kamar ana kira ne zuwa ga maza, saboda haka dukkan ayoyin da aka yi amfani da su wajen umartar mutane a kan yin salla da azumi da wannan sigar ne wato an yi amfani da lamirin maza ne, amma wannan umarni ya kunshi mata kamar yadda ya kunshi maza. Kamar yadda yake cewa: Ku tsayar da salla ku bayar da zakka duk abin da kuka gabatar domin kawunanku na alheri to zaku same shi a wajen Allah”[13]

 Wannan umarni bisa lura ga ka’idar larabci kamar yana fuskantar maza ne, amma wannan hukunci ya kunshi duka maza da mata ne.

 Saboda haka kiran da a aka yi a cikin dukkan wadannan hadisai guda biyu da cewa”ku ziyarci kaburbura”duk da cewa ya fuskantar maza ne amma sakamakon haka ya hada maza da mata ne.

 Bayan wannan hadisi kuma a kawai wasu ruwayoyi da suke nuni da halascin ziyarar kabari ga mace, saboda haka a nan zamu ambaci wadannann hadisai kamar haka:

1-Muslim yan ruwato a cikin sahih dinsa daga Manzo cewa: Jibril ya sauko zuwa gare ya ce ma ni: Ubangijinka yana ba da umarni da a ziyarci kaburburan mutanen “Bakiyya” Sannan ka nema musu gafara a wajen Allah”

 Sai Manzo ya tashi daga bisa shimfidarsa ya tafi Bakiyya domin ziyara, sai A’isha ta bi Manzo (s.a.w). daga baya, sai ta fahimci umarnin da Allah ya aiko wa Manzo. A lokacin sai ta tambayi Manzo cewa to yaya zan ziyarci mutanen baki?

 Sai Manzo ya ce: “Ki ce amincin Allah ya tabbata ga nutanen wannan gida daga musulmai da muminai, Allah ya gafarta wa wdan da suka riga mu da wadanda zasu zo bayammu. [14]

Wurin da ake kafa dalili a nan shi ne wajen koyar da A’isha yadda ake ziyara, saboda haka idan ya zamana mace bai halitta ba ta ta ziyarci makabarta, a nan babu ma’ana Manzo ya koyar da matarsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next