Hakkin Harshe



Daya daga cikin masu hikima yana cewa: "A kwai fa'ida dubu bakwai a cikin yin shiru, kuma sun hadu cikin kalmomi bakwai, da kowace kalma akwai dubu a cikinta. Yin shiru ibada ce ba tare da wahala ba, kuma ado ne ba tare da kwalliya ba, kwarjini ne ba tare da mulki ba, katanga ce ba tare da wani garu ba, wadatuwa ne daga kawo uzuri gun mutane, hutun mala'iku masu rubutu ne, sutura ne ga aibobi".

Sannan a wannan zamanin akwai bahasin cutar da mutane da baki amma ta hanyar shan hayakin taba, wannan lamari abu ne mai muhimmanci domin yana haifar da cututtuka ga wadanda ake hura wa wannan hayaki, kuma yana samar da gurbata iskar da suke shaka, sannan yana nuna karancin hankalin mai shan taba a cikin mutane.

Don haka yana da muhimmanci masu tunani da hankali su kiyaye inda zasu sha taba, idan ya kasance lallai suna son yin haka, to sai su samu wurin da yake kebantacce daga cikin mutane, domin gudun kada su dauki alhakin mutane masu yawa, sai wannan ya kasance musu zunubin cutar da mutane, kuma su daukin nauyin hisabin haka a lahira.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Saturday, May 14, 2011

 [1] Amali: Sheikh Dusi; 548.

[2] Jawahirul kalam, jawahiri, j 14, s: 112.

[3] Hujurat: 10. Mizanul hikima, babu ahammiyatil islah bainan nasi, Raishahari, j 2, Hamish s: 1622

[4] Biharul Anwar: Majlisi; j 71, s 270.

[5] Surar Ma’ida: 27.

[6] Adda’awat: Kudbuddin Rawandi; s 20.



back 1 2 3