Tarbiyyar Rai



Tarbiyyar Rai

Rai shi ne bangaren badini na dan Adam wanda ba a ganin sa amma ana riskarsa da mariskai na badini, don haka ne kowane mai rai yana riskar samuwarsa da cewa yana da samuwa. Amma jiki shi ne bangaren zahiri na dan Adam wanda yake ana riskarsa da mariskai na zahiri, kamar gani, ji, shaka, dandano, da sauransu. Da wannan ne zamu kai ga natijar cewa mutum yana da bangarori biyu ne na badini da zahiri, kuma asalinsa shi ne badininsa, amma a fili muna iya fahimtar asalinsa wato badininsa ta hanyar zahirinsa ne.

Ran mutum tana da rassa da bangarori kamar yadda jikinsa yake da gabobi, wadannan bangarori sun hada da zuciya, da hankali, da Saken tunani (Khayal), da Saken zuciya (Waham), sai kuma Rundunar Sha'awa, da Rundunar Fushi.

 Zuciya: Ita ce bangaren samuwar mutum mai juya shi wacce idan ta samu haskaka da hasken shiriya babu wani abu da yake bubbugowa daga gareta sai umarnin alheri. Amma idan ta cika da duhun bata to sai ta lalace, sai ta kasance babu wani abu da zai zo daga wurinta sai umarni da sabo. Don haka ne ma ruwaya ta zo cewa a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuwa ta baci dukkan jiki ya baci, ita ce zuciya[1].

Kuma ita wannan zuciya ita ce gidan ubangiji a cikin duniya da bai yarda a sanya kowa a ciki ba sai shi, don haka ne wanda ya yarda ya sanya wanin Allah a cikinta to sai ya tabe. Sai dai sanya wanin Allah ba yana nufin babu wani a ciki ba, abin nufi shi ne idan akwai wani abu a cikinta to ya kasance don Allah, kamar dai son annabawa, da waliyyai, da bayin Allah saboda Allah.

Hankali: Shi ne bangaren rayukan bayi mai riskar sanin abubuwa kamar yadda suke ko sabanin hakan, ana son cika wannnan bangaren da hasken ilimi da sanin Allah madaukaki da siffofinsa, da annabawansa da wasiyyansu.

Idan wannan bangare ya samu hasken ilmi to babu wani abu da zai yi sai kokarin haskakawa sauran gabobi da abin da ya dace da wanda bai dace ba, sai ya rika nuna hanya ga mutum domin ya kai shi zuwa ga rabautarsa. Shi fitila ce ta sauran bangarori da idan suka fada duhu zai haskaka musu, kuma shi zai bayar da mafita ta gari da nuni zuwa ga hanyar kwarai.

 Amma idan ya jahilci ubangijinsa, da siffofinsa, da sakonsa, ya kasa tantance gaskiya da karya, sai ya rude ya shiga dimuwa, rundunar jahilci ta mamaye shi, sai wauta ta durfafe shi, duhun rashin sani ya lullube shi, sai ya jagoranci bangarorin sha’awa da fushi zuwa ga hanyar lalaci da bata, domin shi makahon jagora ne wanda bai san mafita ba.

Hankali shi ne jagoran tafiyar a dukkan wadannan bangarori na rai, kuma shi ne yake tantance mai kyau da maras kyau sai ya yi umarni da kyakkyawa, ya hana yin mummuna, kuma ya tace ya auna guda biyun sai ya ware mai amfanarwa da mai cutarwa domin ya yi umarni da da rinjayar da amfanuwa daga na farko, da kuma nisantar na biyu.

Saken Tunani (Khayal): Shi ne bangaren rai wanda yake tuna abubuwan da suke da surarsu da hotonsu a cikin tunani, wasu sun faru wasu kuwa ba su faru ba, yana iya haifar da wata sura ta wani abu mai kyau ko mai tsananin muni. Wannan bangare yana daga cikin bangaren da ya fi komai hadari domin yana sanya waswasi, da firgici, da tsoro, misali idan mutum yana shi kadai, ko yana cikin duhu musamman yara wannan bangaren yana iya azabtar da su har su fita da gudu.

Daga cikin ayyukansa yakan iya daukar surar abubuwan da ya riska sai ya hada su, kamar ya sawwala wani dokin zinare mai fika-fikai, da kaho. Da wannan ne zamu fahimci hadarin wannan bangare na Saken tunani, da cututtukan rai da yake jefa mutane kamar waswasi.



1 2 next