Hakikar Shi'anci



Gabatarwa bugu na farko

Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai

Akwai abubuwan da mai karatu ba zai iya wadatuwa da su ba kafin ya shiga cikin ainihin maudu’in da muke magana a kai, domin wadannan abubuwan zasu kunshi amsa ne na abubuwan da zasu iya zowa mai karatu na daga tambayoyi yayin karanta littafin, kamar yadda haka nan kuma zasu iya sanya mai karatu ya fahimci abin da ake magana a kansa tun farko domin kada ya samu fahimtar akasin abin da littafin yake son bayani kansa. Kuma muna iya kawo wadannan abubuwa a takaice kamar haka:

1- Zai iya yiwuwa mai karatu saboda ya ga Sunan littafin "Hakikanin Shi’anci" ya dauka cewa wannan littafin zai yi magana ne kan dukkan abin da ya shafi Shi’anci ne tun daga sama har kasa. Domin kada ya fahimci hakan; Ina son in jawo hankalinsa ya fahimci cewa ni a wannan littafin ban kawo dukkan abin da ya shafi Shi’anci ba na daga bayanai da suke siffanta shi ko kuma suke magana a kan hakikaninsa ne, sai dai ni na kawo wasu abubuwa ne da zasu iya isa domin bayanin bayanin hakikanin Shi’anci kuma a lokaci guda akwai bayanin abubuwan da ake da sabani tsakanin bangarorin musulmi a cikinsa musamman wanda ya shafi sabani tsakanin wani bangare na musulmi da kuma Shi'a, kuma suka kasance har yanzu akwai jayayya da sabanin a tsakaninsu duk da kuwa irin rubuce-rubuce da aka yi a kansu tun da dadewa har zuwa wannan lokaci namu kuma suka shafi wani bayani game da Shi’anci ta fuskancin bangaren al’umma da bangaren fikirarsa.

2- Kuma a bisa hakika akwai mutane masu yawa tun da can da suka rubuta littattafai masu yawa masu zurfi fiye da wannan kuma masu tsayi da kayatarwa fiye da haka a game da â€کyan Shi'a da Shi’anci, sai dai ni ina ganin na gyara wasu abubuwan da suka kunsa ta hanyar rubutu da wani sabon usulubi da ya saba da na sauran, kuma amma ba ina cewa wannan usulubin da na zaba ya fi sauran ba ne, sai dai ina da tabbacin cewa wannan zai fi saurin kai mai karatu zuwa ga abin da yake son samu na natija a cikin karatunsa, domin kuwa ba ni ne farkon wanda ya yi kokari ya kuma yi kuskure ba, kuma irin wadannan mutane suna da yawa a tarihi.

3- Mai karatu yana iya cin karo da wasu matsalolin da miyagun asakaloli da yakoki da sa-in-sa suka haifar a cikin tarihin musulmi kamar yadda dukkan wanda ya taba lekawa tarihi zai iya ganin irin wadannan miyagun munanan abubuwan da aka haifar da su a tsawon tarihin musulmi, kuma wadanann abubuwa ne da suke sun faro bisa yanayin dabi’ar rayuwar musulmi duka da kuwa jure wa jin su yana yi wa mutane wahala, amma duk wanda ya saba da rubutu a irin wadannan fagage ya san irin girman ciwon da ake ji kuma da irin juriya da ake bukata wajen hakan. Amma wani babban abin takaici sai ga da yawa daga marubuta sun gajiya sun karkatar da alkalamin rubutunsu yana bin son zuciya da kuma bangaranci da muhimmancin wannan al’amari da yake wucewa yau da gobe da kuma irin tunkudar hadari da bala’in da yake zuwa lokaci lokaci, da kuma mutanen da suke kawo shubuhohi wadanda su ba su yi nesa da shubuhohin ba, kuma wannan turnuki zai ci gaba a wannan yanayi mai duhu kuma yana ci gaba a wannan lokaci namu muna ganinsa ba tare da mun yi wani kokarin mun tsaftace shi ba, mun fito da komai fili mun kuma ta ce shi tacewa cikakkiya domin mu kai ga wani ra’ayi da wani sakamako. Kuma ina iya maimaitawa cewa mu sani wannan juriyar ba wani abu ne mai sauki ba a bisa hakika domin mutun ya fi bin son zuciyarsa fiye da hankalinsa sai wanda kyawawan halayensa suka yi wa dabaibayi kuma addini yake tsarkake shi, kuma Allah ne muke roko ya sanya mu daga cikinsu.

4- Haka nan kuma wani yana iya cewa duk da abin da ka ambata dazu haka ne, to mene ne amfanin wannan littafin a cikin irin wadannan al’amuran? Sau da yawa mukan samu abin mamaki na dagewa da nacewa a kan jefa irin wadannan mas’alolin kamar hakan, kai kace ba a yi magana game da wannan al’amari ba, kuma ba a yawaita tambaya da amsa a kan hakan ba a wurare masu yawa. Suka ce; wannan al’amari shi ne kusan abin da yake sanya mutum yana samun nutsuwa da cewa wadannan al’amura da ake ta magna a kan su ba zasu samu wani warwara ba kuma ga lokacin mai tsada da ake ta batawa a kansu a irin wannan al’amarin.

Idan muna son amsa a kan haka muna iya cewa masu ganin cewa kofa a toshe take to suna son ke nan mu sallama kuma mu yi saranda ga wadannan kalubale da suke fuskantar mu, alhalin ba mu da wani abu da zai iya ba mu mafita sai fuskantar duk wani kalubale. Kuma babu wani lokaci da babu masu bincike kan gaskiya kuma duk wadanda shubuhohi suka rinjaya suna demaucewa ne a cikinta kuma suna da yawa, kuma yin kunnen shegu da bukatun irin wadannan nau’i biyu na mutane ba tare da an taimaka musu ba abu ne wanda masanin sakon karshe na wannan addini da ya zo domin daukaka rayuwa zuwa ga mafi alherin al’amari ba zai iya jure shi ba. Kuma barin wadannan marubuta masu rudarwa su yi wasa da kwakwalen musulmi shi ma wata bayar da gudummuwa ce ga masu kawo rudu. Mu masu kira ne domin share irin wannan alekakai daga tafarkin musulmi har sai hanya ta kasance shararriya a gabansu. Kuma dukkan sakamakon da za a samu a wannan fage yana kasancewa ya yi daidai da kiran nan na da’awar musulunci da kuma yin daidai da jihadi da alkalami da tunani, kuma ba ya daga cikin hankali mu kyale mai rashin lafiya ba tare da mun ba shi koda kwankwada daya ta ruwa ba, alhalin muna da iko a kan hakan kamar yadda muke gani.

Sau da yawa mutun ya rayu tsawon zamani cikin son rai da gajiyawa sannan sai ya koma zuwa ga gaskiya sakamakon alkaluman marubuta masu tsafta da suka gyara masa tunaninsa musamman ma idan wadannan alkaluma suka iya daukar bisa hanya mai sauki kuma suka kasance daga zuciya tsarkakkiya, kuma suka dora rayuwarsa a kan tsarin musulunci mai tsarki.

5- Wani abin da yake iya saukake magana game da abin da yake faruwa na sabani tsakanin bangarorin musulmi tun da ta faru, ba ta kai zuwa ga asasi ba, tana matsayin fagen rassa ne kawai duk da da yawa daga mutane suna son su isar da ita zuwa asasi ta hanyar ba ta wani suna daban da kuma kokarin shigar da wasu abubuwan ta bayan fage. Sai dai idan mun lura sosai zamu ga ta faro ne daga asasi zuwa ga rassa, kuma matukar muna son gaskiyar lamari dole ne mu fara maganin wadannan al’amura. Kuma matukar hankula suna da sabani wajen riska da fahimta kuma fahimta ta sha bamban to abu na hankali shi ne mu ce; sabanin da yake cikin mas’alolin tunani abu ne na tunani da hankali kawai abin da yake jawo mantuwa ga irin wannan shi ne kuntata tunani da kuma son rai.

6- Tun da mas’alolin wannan littafin suna da yawa don haka ne mai karatu ba zai samu maudu’i daya ba kuma saboda haka yanayin da zai samu kansa game da hakan zai sassaba. Tare da cewa idrakinmu ga wannan mas’alolin da wannan maudu’i na akida ya tattaro su, sai dai rassan wannan maudu’i mabambanta ne, kuma mu muna idrakin cewa akwai dan musamaha a cikin abin da ake kira akida, domin tana iya yiwuwa ba ya daga abin da mutm yake imani da shi wani lokaci, sai ya kasance wani shi’ari ne kwai da yake da maslaha a cikinsa ko kuma al'adarsa take doruwa a kansa. Kuma wannan sirri ne da ya sanya zamu ga wasu mutane wani lokaci suna riko da wasu tunani da sun san batacce ne. Sai dai yin aiki da tunanin da mutum yake da shi yana daga dalilai mabambanta ne, kuma wannan yana daga musibarmu da bala’in da ya same mu a yau.



back 1 2 3 4 5 6 next