Halayen Imam Mahadi (a.s)



Game da saninsa da halin da mutane suke ciki a matsayinsa na shugaban hukuma ya zo cewa: Idan wani ya yi wata magana a gidansa to yana jin tsoron cewa; kada fa bangwayen gidansa su kai bayaninsa[55]. Idan mun yi la'akari da kayan sadarwa da ake da su fahimtar wadannan ruwayoyi yana da sauki, amma kuma ba wani abu ba ne fayyacacce, shin wadannan kayan su ne zasu fi hakan cigaba ko kuwa wani tsarin takanolaji ne sabo zai zo da shi wanda ya fi wannan da zai maye gurbin na yau.

 

Halayyar Imam Mahadi

Game da halayyar Imam Mahadi (a.s) muna iya cewa; shi yana matsayin shugaba ne kuma jagora mai alaka da mutane da yake ganin hukuma a matsayin wata wasida ta yin hidima ga mutane da kaiwa ga kololuwar kamala, da kuma katse hannayen azzalumai daga bautar da bayin Allah. A bisa hakika shi yana da tafarki irin na Imam Ali (a.s) ne wanda yake da dukiyar al'umma a hannunsa amma shi yana rayuwar talauci ta kasa ta karshe.

Imam Ali (a.s) yana cewa: Imam Mahadi s zai dauka wa kansa alkawarin zai yi rayuwa kamar na mutanensa kuma ya sanya abin da suke sawa, ya hau abin da suke hawa… ya wadatu da kadan[56]. Kuma Imam Ali (a.s) kansa ya yi irin wannan rayuwa ne a Duniya a abinci da tufafi, kuma ya yi koyi da Manzon Allah (s.a.w) ne, kamar yadda Imam Mahadi (a.s) zai yi koyi da su.

Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Idan mai juyinmu (Imam Mahadi) ya zo, zai ya sanya tufafi irin na Ali, kuma ya tafiyar da al'umma da irin hanyarsa[57].

A daidai lokacin da yake tsanantawa kansa rayuwa, sai gashi kuma ga al'umma ya kasance kamar uba ne mai yawan tausayi ga 'ya'yansa, kuma a kodayaushe yana neman abin da zai kawo musu sauki ne, ta yadda Imam Ridha (a.s) a wata ruwaya yake siffanta shi yana mai cewa: Imami ne mai tausasawa da jin kai, kuma uba mai tausayawa, kuma dan'uwan mai tausayawa, kuma uwa mai kyautatawa ga danta karami, mai gaggauta bayar da mafaka ga al'umma a cikin musiba mai ban tsoro[58].

Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: shi ne al'ummarsa take fakewa gunsa kamar yadda kudan zuwa suke fakewa gun sarauniyarsu[59].

Yardar Mutane: Yardar mutane ita ce daya daga abubuwan da suke jan hankalin mutane game da hukumomi, amma daular Imam Mahadi (a.s) zata samu karbuwa da yardar mutane gaba daya, ba kawai mutanen Duniya ba, har ma mutanen sama zasu yarda da wannan hukuma ta adalci. Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ina yi muku albishir da Imam Mahadi (a.s) da mutanen sama da kasa zasu yarda da hukumarsa. Yaya kuwa wani ba zai yarda da hukumar Imam Mahadi (a.s) ba, alhalin dukkan Duniya ya haskaka da bayyana gareta cewa; gyaran al'amarin dan Adam na Duniya da lahira yana iya wakana ne kawai a hukumar Allah madaukaki[60].

Muna iya karasa wannan maganar da wani bangare na maganar Imam Ali (a.s) domin kyautata kammalawa da yake cewa: …Ubangiji zai karfafe shi da mala'iku, kuma ya kare mataimakansa, kuma ya taimaka masa ta hanyar alamominsa, kuma ya sanya shi mai galaba a kan mutanen Duniya, kuma ya sanya su masu zuwa gareshi jama'a-jama'a suna masu son ransu da kuma bisa tilas, kuma zai cika Duniya da adalci da haske da dalili. Kasashe zasu yi imani da shi har sai ya kasance babu wani kafiri da zai rage sai ya yi imani, kuma munanan ayyuka ba zasu rage ba sai sun koma kyawawa, kuma a hukumarsa masu fika (dabbobin daji masu kisan namun daji) zasu yi sulhu tsakaninsu, kuma Duniya zata fito da dukkan albarka, kuma sama ta kwararo alheranta, kuma taskokin Duniya zasu bayyana gareshi… to farin ciki ya tabbata ga wanda ya ga wannan rana, ya ji maganarsa[61].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 next