Halayen Imam Hasan (a.s)



Amma duk da haka Imam Hasan (a.s) ya yi kokarin ganin ya sanya Mu'awiya sharuddan yin hukunci da musulunci da dokokinsa domin ya bar masa jagorancin al'umma, sai dai mu'awiya bai yi aiki da ko daya daga cikinsu ba. Wadannnan dokokin da sharuddan sun hada da:

Mu'awiya ya yi hukunci da littafin Allah da sunnar manzonsa, da ta halifofi salihai.

Mu'awiya ba zai iya bayar da mulki ga wani ba ko ga dansa, domin zai koma ga Imam Hasan (a.s), sannan bayan Hasan (a.s) sai Imam Husain (a.s).

Mutane dukkansu amintattu ne a Iraki, da Sham, da Hijaz, da Yaman da sauran kasashe, ba shi da hakkin taba wani daga cikinsu.

Shi'ar Imam Ali (a.s) duk inda suke amintattu ne su da dukiyoyinsu, da matansu, da 'ya'yansu.

Kada ya sake ya yi wani makirci ga Hasan da Husain (a.s) ko ga wani daga alayen annabi (s.a.w) a boye ne ko a fili, kuma kada ya tsoratar da wani a ko'ina a bayan kasa.

Sai dai Mu'awiya wanda bai san addini ko tsoron Allah ba, a matsayinsa na jagoran munafunci bai yi amfani da ko daya daga ciki ba, domin ya kashe duk sahabban manzon Allah (s.a.w) da na Imam Ali (a.s) na gari da suka rage, haka nan ya kashe Hasan (a.s) jikan manzon Allah (s.a.w) da duk wani wanda ya samu damar kashewa daga wadanda ba su tsira daga makircinsa ba.

Imam Ali (a.s) ya yi wa Imam Hasan (a.s) tambayoyi na hikima wadanda suka shahara a cikinsu akwai kyawawan halaye kuma duk ya amsa su. Zamu kawo su ne a takaice kamar haka:

Ya amsa katari da cewa shi ne ture mummuna da kyakkyawa. Daukaka kuwa ita ce kyautata wa jama'a, da dauke nauyinsu. Mutunci kuwa shi ne kame kai, da kuma gyara dukiya. Kaskanci kuwa shi ne sauraron dan kankani, da hana dan kadan. Da sauran tambayoyi da ya amsa su.

Ya kasance yana zama da miskinai ya ci abincinsu, wata rana ya wuce su sai suka yi masa tayi, sai ya zauna ya ci abinci tare da su, sannan kuma sai ya tafi tare da su gidansa suka ci nasa abincin.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next