Sayyid Sistani



3-Himmantuwa da usul da yake da alaka da fikihu :Saudayawa dalibi yakan ga malamai sun dulmiya cikin usul dulmiya da bahasin da ba ya kai wa ga komai sai tsantsar nazari da ba ya bayar da wani sakamako na fikihu a tafarkin ilimin fikihu kamar bincike game da cewa sanya wa ma’ana lafazi shin alamari ne na dabi’ar  samuwa ta halitta ko kuma abu ne na la’akari na tunani wanda irin wannan bincike ba shi da wani sakamako na a zo a gani a fikihu amma shi malamin da muke Magana akansa ya shagaltu da bincike na usul ne mai zurfi wanda yana da alaka da sakamako na fikihu kamar bahasin amm da khas da ta’adul wat tarjihi da usulul amaliyya.

4- Canji da sabuntawa :Malamin ya kasance yana dauke da ruhin neman canji ba kamar wasu malamai ba  da yawa zaka same su ba sa dauke da ruhin kawo canji , suna sa himmarsu ne kawai wajan ganin kayen bahasi ba hakikanin asalinsa ba. sai  ya shagaltar da kansa wajan warwarar wasu jimloli da ishkalin da aka yi akansu.

5-Shagaltuwa da al’amuran zamani  :kamar bahasi kan halarcin auren kafira mushrika da ka’idar tazahum da malamai suke bincike akanta a matsayin ka’ida ta hankali kadai , amma shi ya shigar da ita karkashin ka’idar iddirari wato abu na larura da ba makawa gare shi wacce ita ka’ida ce ta shari’a ba ta hankali ba kamar yadda nassi hadisai da ayoyi sun yi nuni zuwa gare ta. Haka nan ka’idar latu’adu  a cikin salla ya sanya ta akan duk wata farilla da sunna da suka hadu ko a salla ko ba a salla ba saboda karshen ruwayar yana cewa ba a sake farilla saboda sunna ai sunna ba ta iya rusa farilla . shi ya sa  ya gabatar da lokaci da alkibla akan yanke yanken salla, saboda lokaci da alkibla farilla ne ba sunna ba.

6-Duban nassi ta fuskacin zamantakewar al’umma :Wasu malamai suna duba nassi ruwaya ne ba tare da neman  fidda ma’anarta ba da kallonta ta mahanga daban daban. Amma wasu malamai kamar shi Ayatul lahi sistani suna duba ruwaya ta kowane bangare kamar yanayin zamantakewar al’umma  domin fahimtar ruwaya. Kamar hadisin da yake cewa manzo (SAW) ya hana cin naman jakin gida a khaibar, a nan zamu ga yanayin lokacin ana yaki ne kuma ana daukar kaya akan jakuna ne idan aka cinye su to wannan yana nufin raunin kayan sufuri da daukar kayan yaki  saboda haka anan ba wani abu da yake fahimtar da haramci ko karhanci na cin naman jakin gida domin hanin ya zo da bayanin masalahar da ta sanya hana cin naman jakin na yanayi da ake cikin.

7-Cikakkiyar masaniya da ilimomin ijtihadi da fitar da hukunci :Sayyid sistani ya kasance yana dagewa ko da yaushe kan cewa malami ba ya zama malami sai idan yana da cikakkiyar masaniya game da  maganar larabawa da wakokinsu da hudubobinsu domin ya zama zai iya gane ma’anar Magana ta maudu’iyya ba zatiyya ba ya kuma zama yana da cikkakken sani kan littafan lugga da mawallafanta da hanyar rubuta ta wannan duk yana daga abubuwa da za a dogara da su wajan karbar maganar ma’abocin littafin lugga. Haka nan ya zama yana da cikken sani game da hadisan Ahlul bait (AS) da masu rawaito hadisan dalla dalla domin ilmul rijal larura ne kuma dole ne saninsa ga mujtahidi. Wasu malamai sukan dogara ne da zuhuru shakhsi  na akhbar ba tare da ya hada ta da zuhurur maudu’I ba. ko ya dogara kan maganar  mawallafa littafan luga ba tare da bincike ba na kashin kansa.

8- Kwatantawa tsakanin makarantu daban daban  :Sanannen abu ne ga wanda suka halarci karatunsa sun san cewa baya kayyade tunaninsa da makaranta daya ko mahanga daya. Yana hada bincikensa ne tsakanin makarantar Mashhada da ta Kum da ta Najaf yana bincike a ra’ayoyin mirza isfahani da na sayyid burujardi da na sayyid khu’I da asshaikh Husain hilli  Allah ya ji kansu.

TAFARKINSA NA FIKIHU

Tafarkinsa na fikihu yana da kasu kashi  uku ne:

1- Hadawa da kwatantawa tsakanin fikihun shi’a da na sunna

2- Amfana da ga ilimin kanun (dokoki) a fikihu domin samun fadada wajajan amfani da ka’idojin fikihu da kuma buda tunani kan dokokin zamani  da taimakawa wajan bayanin dokokin fikihu da wuraren amfani da ita.

3- Sabunta yanayin yanda ake bayar da darasi, kamar mahangarsa ga ka’idar ilzami ta wata fuska kamar ta fuskacin girmamawa shi ya sa ma yake kiranta da ka’idar girmamawa.

SIFFOFINSA

1- Girmama ra’ayin wasu da yi musu adalci ya kasance mai binciken ra’ayin mutane  har  da na abokansa mai yawan bin littafai da kwadayin ilmi da cimma gaskiyar lamari, yana binciken har ra’ayin abokansa da na wasunsu wadanda ba malamansa ba ne  ya kuma yi munakasha da tattaunawa akan ra’ayin da girmamawa.

2-Lladabi cikin tattaunawa ba kamar yadda wasu dalibai kan yi ba shi ya kasance yana tattaunawa da ladabi ne da girmamawa ga malami kuma yana nisantar duk wata jayayya  kumayana  amsawa ga dalibi tambayarsa da tattaunawarsa da girmamawa ta fuskacin kamar luraswa da shiryarwa ga mafifici. Idan dalibi ya dage ya mayar da shi jayayya to yanaamsawa ne amma idan ya sake dagewa, sau da yawa yakan fifita shiru kan magana

3- Dabi’arsa : Yana ganin koyarwa aiki ne da ya hau kansa domin shiryar da al’umma( ba kamar aiki ne na gwamnati ba da sauransu) da kuma tausayawa ga  dalibi.  Haka kyawawan dabi’unsa suka yi tasiri akan dalibansa kamar yadda ya kasance ga Ayatul- lahi assayyid Hakim da kuma sayyid khu’i (RA)

4-Tsantseni  : Ya kasance mai lizimtar shiru  da tsantseni da nisantar duk wata hargowa ta kabilanci ko hassada da mugun kudiri da neman amfanin kashin kai. Ya kasance yana mai nisantar duk wani neman matsayi da suna da mukami da sabani kan al’amura na duniya. Kuma ya kasance mai zuhudu da tufafi na takawa da kaskantar da kai. Da dan karamin gidansa da ‘yan kayansa.

4- Kawo sabon tunani :  Assayyid sistani ba kawai malami ba ne , shi mutum ne mai wayewa da masaniya kan al’amuran zamani kuma mai budadden tunani kan wayewa da al’adu daban daban kuma yana da mahanga da ra’ayoyi game da tattalin arziki da siyasa da nazarce nazarce sababbi da tunani kan zamantakewa da faffadan tunani game da yanayin wannan lokaci ta yadda fatawowinsa suka kasance domin masalahar al’ummar musulmi.

Marja’ancinsa

Wasu malaman Najaf madaukakiya sun nakalto cewa bayan wafatin Ayatul Lahi Assayyid Nasrullah Allah ya ji kansa sai malamai suka ba wa sayyid khu’I shawarar cewa ya fitar da wani mutum da ake nuni zuwa gare shi ake girmamawa da ya cancanci mar’ja’anci da kuma kiyaye hauzar Najaf , sai ya zabi sayyid sistani saboda falalarsa da daukakarsa ta ilimi da tsarkin zuciyarsa da kyawun dabi’unsa. Bayan wafatin sayyida khu’i ya kasance cikin mutane shida da suka raka jana’izarsa kuma shi ne ya yi masa salla, bayan haka ne ya daukin nauyin marja’anci da jagoranci Hauza da aikawa da izini da raba dukiyoyi da koyarwa akan minbarin sayyid imam Al-khu’iAllah ya ji kansa a masallacin Khadra’a kuma takalidi da shi ya yadu da gaggawa a kasar Irak da Khalij da sauran yankunan duniya kamar Indiya da Afrika da sauransu musamman tsakanin malamai a Hauza da kuma tsakanin samari da wayayyun mutane wadanda suke da tunani na wayewa , har yanzu yana cikin mutane ‘yan kadan da malamai manya da yawa suka yi musu shedar a’alamiyya a Najaf da Kum madaukaka Allah ya ja zamaninsa ya tsawaita rayuwarsa.

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com



back 1 2