Imam Mahadi (a.s)



 

MahangarShi'anciGame Imam Mahadi (A.S)

Acikin masu bayanin karshen zamani, musulunci ne kawai shi ma a mazhabar Shi'anci ya yi bayanin dalla-dallan wannan al’amari da zurfi. Ta yiwu wasu su yi tsammanin cewa imamanci shi ne asalin abin da ya zo da batun imam Mahadi (A.S), amma wannan ra’ayi ba daidai ba ne, domin sakon Manzo (S.A.W) shi ne ya fara zuwa da batun imam Mahadi (A.S) kamar yadda muka kawo ayoyi masu yawa daga kur’ani game da al’amarin, haka nan daruruwan ruwayoyi sun shaida da akidar zuwan imam Mahadi (A.S), shi ya sa ma musulmi suka yi imani da zuwan Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Ali (A.S) da Fadima (A.S), kuma sunansa da kinayarsa irin na Manzo (S.A.W) ne[1].

Asalin imani da zuwa imam Mahadi (A.S) ya faro ne daga ruwayoyi tun zamanin Manzo (S.A.W) wanda ya zo da bayani a fili yankakke daga annabi (S.A.W) game da Mahadi mai zuwa karshen zamani, wannan kuwa yana nuda dalilin ingancin mahangar Shi'a[2].

Tawaturyana daga cikin abin da yake nuna ingancin magana ta yadda tsammanin karyar magana zai koru, idan mun duba zamu ga hadisan da suka yi bayni game da zuwan Mahadi (A.S) suna da tawaturta ta yadda hankli ba ya wani kokwanto wajan karbarsu.

AllamaDiba’diba’i yana cewa: Idan aka bi kididdiga za a samu sama da ruwayoyi 3000 da suka zo daga annabi da imamai (A.S) game da zuwan imam Mahadi (A.S)[3].

Malaman Shi'a gaba dayansu sun tafi a kan tawaturancin ruwayoyin da suka zo game da imam Mahadi (A.S), haka nan shafi’i ya tafi a kan hakan. Kuma an rawaito hadisai masu yawa game da imam Mahadi (A.S) daga malamai masu yawa na Ahlussunna kamar; Ahmad, Ibn Dawud, Ibn Majah, Tirmizi, Bukhari, Muslim, Nisa’i, Baihaki, Mawardi, Dabrani, Sam’ani, Ibn Sari, Ibn Asakir, Kisa’i, Ibn Asir, Hakim, Ibn Jauzi, Ibn Abil Hadid Mu’utazili, Ibn Sabbag Maliki, Ibn Magazili Shafi’i, Muhibbuddin Dabari, Shabalanji da …, a takaice bayyanar imam Mahadi wani abu ne da aka yi ittifaki a kansa[4]. A wasu ruwayoyin ma an ambaci sunansa da sunan babansa a matsayin cewa shi dan imam Hasan Askari (A.S) ne[5].

Daga cikin manyan littattafai akwai littafin “masnad Ahmad bn Hambal” wanda ya mutu a shekarar 241H, a kwai hadisai game da imam Mahadi da ana iya samun su a jildi (mujalladi) na daya da na biyu, da na uku, da na biyar[6].

Ma’abota littattafai shida na sihahussitta da Ahmad dan Hambal sun rawaito hadisai daga Umar dan Haddabi, da Abdullahi dan Mas’ud, da Abdullahi dan Umar, da Abdullahi dan Abbas, da Sauban, da Jabir dan Abdullahi Al’ansari, da Jabir dan Samura, da Abdullahi dan Amru, da Anas dan Malik, da Abu Sa’idul Khuduri, da Ummul muminin Ummu salama (R.A) da wasunsu[7].

Mas’alar karshen zamani tana daga cikin mas’alolin farko na asasi a musulunci bayan tauhidi, da annabta, da ranar kiyama, kuma babu wani bahasi da aka yi da ya kai na wadannan hadisai[8]. Hatta da malamai a hijaz mas’alar bayyanar imam Mahadi suna ganinta a matsayin mas’ala ta asasin addini ba rassansa ba[9].

Don haka mahadiyyanci idan mun yi la’akari da karshen zamani yana matsayin daya daga laruran addini mai tsarki na musulunci ne, ta yadda wadanda suka yi musun sa suna iya fita daga addinin musulunci:

“Wanda ya karyata da Mahadi (A.S) hakika ya kafirta”[10].

Mas’alar Mahadi (A.S) abu ne wanda masanan Ahlussunna kamar Ibn Abil Hadid[11], da Ibn Khaldon, da Ibnl Arabi suka yarda da shi kamar yadda masu ruwayar hadisai suka yarda da ita, Ibn Khaldon duk da ya raunata hadisai kusan 25 daga cikin hadisan da suka zo game da imam Mahadi (A.S), amma ya yarda da batun zuwan imam Mahadi (A.S) kamar yadda yake fada: Mu sani cewa shi al’amari ne da ya shahara tsakanin dukkan musulmi a tsawon tarihi, kuma akwai imani da cewa lallai a karshen zamani wani mutum daga Ahlul Bait (A.S) zai bayyana…[12]

Haka nan Ibnl Arabi ya kawo bayani game da bayyanar imam Mahadi (A.S) wanda yake daga zuriyar imam Ali da fadima (A.S) a karshen duniya da zai cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci[13].

A takaice dai muna cewa: Al’amrin imam Mahadi (A.S) al’amari ne da dukkan musulmi suka yi imani da shi[14], sai dai bambanci shi ne; Ahlussunna suna ganin har yanzu ba a haife shi ba[15], amma Shi'a suna ganin an haife shi, kuma shi ne imami na goma sha biyu, yana rayayye  a cikin mutane kamar Hidr (A.S), kodayake a cikin Ahlussunna akwai masu imani da samuwarsa a raye kamar yadda Shi'a suka yi imani da shi.

Duk da isgili da ake samu game da wannan mahanga ta Shi'a daga bangaren mulhidai masu musun Allah, amma a nan gaba a karshen duniya wannan mahanga zata tabbata. Idan muka duba ruwayoyin da suka zo game da imam Mahadi (A.S) zamu samu mamaki maras misali na karama da daraja na Manzo (S.A.W) da imamai na cewar yaya suka iya yin bayanin duniya a karshen zamani duk da kuwa samun tsawon lokaci tsakaninsu da wannan zamanin. Suna bayanin karshen duniya kamar suna nan tare abin yake faruwa.

A hadisan Shi'a wadanda suke daga duniyar gaibi da wahayi an yi bayanin yanayin tattalin arziki, da siyasa, da zamantakewa, da tafiyar da ikon shugabanci a karshen zamani dalla-dalla.

Game da mai tseratar da duniya a karshen zamani mahangar Shi'a ba kamar sauran mahangai ba ce, Shi'a sun yi bayanin game da shi dalla-dalla ne da zurfinsa, da tantancewarsa tun daga nasabarsa da rayuwarsa, da yadda aka haife shi da buyansa har zuwa bayyanarsa, da nau’in hukumarsa da sharuddanta, da waziransa da masu taimaka masa, da dukkan abin da zai faru kafin bayyanarsa da bayanta.

Don haka mahangar Shi'a game da imam Mahadi (A.S) tana da kebantattun siffofi na musamman da wata mahanga ba ta da su. Za a kafa daula madaukakiya a karshen duniya da ta saba da mahangar mulhidai da ‘yan jari-hujja. A wannan bangaren zamu yi kokarin bayanin kebantattun al’amuran mahangar Shi'a da bambancinta da sauran mahangai, sannan sai bayanin mahangar Shi'a game da karshen zamani a dunkule ta biyo baya, sannan daga karshe sai bayanin daular karshen zamani.

 


[1] - Goftumane Mahdawiyyat, Shafi: 136 – 137.
[2] - Shi'a, Allama Diba’diba’i, Shafi: 84.
[3] - Abin da ya gabata, Shafi: 465 – 466.
[4] - Al’imamul Mahadi Inda Ahlussunna, Mahadi Fakih Aimani.
[5] - Abin da ya gabata shafi 84.
[6] - J1 shafi 84 – 99 da 376.
[7] - Danishmande Amme Wa Mahadi Mau’ud, Shafi 13 – 15. A littafin ya kawo 120 daga malaman Ahlussunna da suka yi bayani game da mahadiyanci.
[8] - Mahadawiyyat, Ayatul-Lahi Kashani, Kaset na 56, Shafi: 5.
[9] - Abin da ya gabata.
[10] - Akaduddurar, shafi 157.
[11] Nahajul Balaga, Sharhin Ibn Abil Hadid, J 7, Huduba: 8, 92, 59.
[12] - Abdurrhaman Ibn Khaldon, Al’mukaddima, Fasali 52, Shafi: 311.
[13] - Muhyiddin Arabi, Futuhatul Makiyya, J 3, Shafi: 327.
[14] - Shahid Mudah’hari, Siri Dar Sireyye Ayimme Ad’har, Shafi 289 – 290.
[15] - Sayyid Muhammad Sadar, Tarih Gaiba Kubura, Tarjumeyye Hasan Iftikhar Zade, Shafi: 306 – 307.



back 1 2