Marhalolin Jagoranci



A sarari yakecewa zartarda manhajar sauyi ‘yar asali a cikinal’ummar da ta sami shekaruda dama cikin karkacewar tunani da aiki yana bukatarkwararan dabaru da shiri mai tushe. A wancan lokacin, al’ummar Annabi ta rayu karkashinhukumar Mu’awiya mai cike da karkata gaskiya da musanya ta da wata fuskata jabu, halin da ya jefajama’a cikin wani barci mai nauyi tare da nisanta tunanin mutane daga ruhin jagorancimai bin ka’ida. Wannan baudewata kai harlamarin ya janyo kashe badadinManzon Allah (s.a.w.a) a Karbala, al hali wannan al’umma tana ji tanagani, al’ummar da take fama da halin fargabada rauni da fatattaka a hannun razanarwar banu Umayya.

Saboda hakasai an yiaiki tukuru kafin a iya maidowa wannan al’umma ruhinta rasashshe da mutuntakarta wanda aka tattake, hakika aiki ne mai girma wandaal’umma take bukatarsa domin sake cancantar daukar sakon Islamada kama yunkurin ciccibar nauyin rike shi. Ba makawaga wani sauyi tamkar wandaManzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci al’ummarjahiliyya da shi, sannan daga bisani a karbijagorancin jama’a.

Babu shakka dawoda rayuwa irin ta sauyi da sabontata aiki newanda baikasa samar da ita tun farkowajen tsauri da muhimmanci ba. Tajdidi irin na juyi yanabukatar imani mai karfi da azama tabbatatta da hankali mai tsarawa da tunani farkakke, wayayye mai motsawa. To wane ne mai daukar wannan nauyin?! Waccar jama’ar da ta kasatafiya tareda Imam Hassan (a.s) takuma kasa kai matsayin taimakawaImam Hussain (a.s) lallai ba taiya wannan aikin raya al’ummarmusuluncin. Saboda haka dogaro ga wanna jama’ar babuabin da zai haifar illa cintura da tabewa. Hakika motsin da Tawwabin suka jarrabada tawayen Mukhtar da Ibrahim bin Malik hujja cebabba kan abin da mukafadi.



back 1 next