Marhalolin Jagoranci



Marhalolin Tafiyar Imamanci

Tafiyar Imamanci ta fara ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya bar duniya cikin watan Safar, shekara ta goma sha daya bayan hijira har zuwa wafatin Imam Hassan Askari (a.s) a watan Rabi’ul Awwal, shekara ta dari biyu da sittin bayan hijira. Cikin wadannan shekaru, tafiyar Imamaci ta ci zango hudu, wanda a kowanne Imamai sun dauki matsayi fitacce gaba ga mahukuntan al’ummar musulmi.

MARHALA TA FARKO:-

Wannan ya kunshi matakin kame baki ko mu cematakin taimakawa mahukunta. A wannan zango jinjirar al’ummar musulunci ta yi famada hadarin magabta wanda yayi mata kawanya. Yayin da wadannan magabta suka jibarazanar da sakon musulunci  yake masu, sai sukadana tarkon su daga wajen daularmusulunci suna dakon wata damadomin su aukawa wannan sabuwar al’umma. A wani janibin kuwa akwaiadadi mai yawa na sabon-shigamusulunci wadanda hankalinsu ba zaiiya daukar halin rarraba cikinal’ummar musulunci ba, saboda hakaduk wata tsagar da ka iya faruwa za tazama barazana ga tushen al’ummar da ma samuwarta. Na uku, karkatar da ta sami al’umma bata yi tsananinda har mutum kamar Amirul MumininaAliyu ibn Abi Talib(a.s) wandaya fi kowakaunar kubutar sakon musulunci da al’ummarsa, ba zai iya juremata ba. La’alla wanna halinda ya sami jama’ar musulmi shi ne abin da Manzontsira Muhammadu (s.a.w.a) ya yiishara da shi lokacin da ya yi wasiciga wannan dalibinsa wanda yake farda, da ya yi juriya  idan ya auku.

Wannan zangon ya dauki tsawonrayuwar Imam Ali (a.s) fara daga wafatinManzon Allah ( s.a.w.a) har zuwa karbarsa halifanci. Imam ya yi sharhinmatsayin da ya dauka cikin takardarda ya rubuta wa mutanenkasar Masar yayin da ya nada masu Malik Ashtarhakimi. Ya ce:- “Saina kame hannunayayin da na ga masu juyawa sun juyawa musulunci baya, suna kira

 zuwashafe addinin Muhamamdu (s.a.w.a). Sai na ji tsoron idanban taimaka wa musulunci da ahlinsa ba, zan ga tsagewada rugujewa tattare da shi. Da haka zai faru, to da musibar da za ta sami musulunci ta fi tsanani a gare ni bisa ga kubucewar shugabancin ku.……sai na bayar da gudumowata a abubuwan da suka  faru”(1)

Yayin da shugabanci ya kauce masa sai ya hakura domin musulunci, lokacin da al’umma ta fuskanci hadura masu girma sai ya mike domin kare musulunci da al’ummarsa, yana mai shiryarwa da aiki a fagagen siyasa da soji  da zamantakewa. Cikin Nahjul Balaga da sirar Imam Ali, akwai bayanai masutabbatar da irin nau’in kokarinsa a zamanin shugabancinsa.

MARHALA TA BIYU:-

Zangon rike ragamar shugabanci. Wannan zangon ya dauki shekaru hudu da wata tara na halifancin Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma wasu watanni na halifancin dansa Hassan (a.s). Duk da wahalhalu da matsaloli da damuwa da tsanani da yake tattare da wannan zangon, kamar yadda duk wata hukuma mai ra’ayin juyi take fuskanta, mafi haske da ban sha’awan shafuffukan tarihi ne suka kunshi bayanin aikace-aikacesa, kamar su mu’amala mai cikakkiyar dan Adamtaka da adalci da tsananin lizimtar hukunce-hukuncen musulunci ta fuskoki dabam-dabam wajen gudanar da al’ummar musulunci da kuma rikon magana daya da fayyacewa da jaruntaka wajen aiwatarwa da kuma daukan matsayi.

Wannan zango na tarihin imamanciya zama abinkoyi wanda Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka yikira domin aiwatar da shi a rayuwar  siyasada zamantakewa, tsawon karni biyu. MabiyaAhlulbaiti suna kankame da son wancan yanki natarihin musulunci, suna neman dawoda shi, suna kuma auna tsare-tsaren da suke rayuwa cikinsuda wancan zamani mai ban sha’awa. Da wannan ma’aunin  ne suke tuhumar tsare-tsarenda suka baude wa turbar musulunci. Mai ra’ayin sauyi a al’ummar wacceda bidi’a da baudiya suka addaba. Wannan halin da al’umma take cikinsa ya dorawaImaman da suka biyo baya nauyimai tsanani da mas’uliya  mai girma.

MARHALA TA UKU:-

Shi ne wandaya dauki shekara ashirin,tsankaninsulhun Imam Hassan (a.s) a shekara ta 41 H zuwa shahadarImam Hussain (a.s) a shekara ta 61 H.  Bayan sulhun Imam Hassan (a.s) an soma wani nau’in aiki mai kama da sirri wanda kuma manufarsaita ce maidoda jagorancin musulunci wa ma’abotansa na gaskiya tunda lamarin yana bukatar dako harsai mulkin Mu’awiya ya kare. Cikin wannan gajeran lokaci an fuskantar da kokarin kyautata  yanayi wajen yin shimfida ga zango na gaba.

MARHALA TA HUDU:-

A nanya kamata mu yi bayanimai dan dama, tun da wannan zangonshi ya shafi laccarmu domin a ciki Imam Sadik (a.s) ya rayu. Cikin wannan zangon da ya daukikusan karni biyu, tafiyar Imamancita ci gaba kan wani dogonlayi domin canja al’umma harta dace da ra’ayin musulunci a dukkanin fagage wadanda suka hada da jagorancinsiyasa. Tafiyar sashe ta yigalaba sashe kuma ta gamuda ci baya; tana tattare da nasara mai girma a fagen tunani da akida, tana cudanyeda salo daban daban na dabarungudanar da kira, abin adonta kuwashi ne ikhlasi da sadaukarwa da fana’i da girman dan adamtakaa idon musulunci, halayen da suka kai kololuwa da kuma matukar kyau.Wannanmarhala ko zango ya faradaga watan Muharam shekara ta 61

bayan hijira, bayanshahadar Imam Hussain  bin Ali (a.s). Kamar yanda mukaambata, cikin wannan  zangon, al’umma ta karamotsawa kwarai da gaske a fagen manufa(watau aidiyolojiyya) da tinkarar baude-baude ba jirkice-jirkice, 13  wadanda matattarar iko da kuma kwakwalen jahiliyya suka wanzar. Waccar motsawa manufarta gudanar da aiyuka tsawo lokaci dominkafa hukumar musulunci mai tafiya bisa turbar Alkur’anida sunnar  Ma’aiki (s.a.w.a) kamar yanda Imam Ali (a.s) ya misalta.



1