Asasin Sani



Kuma Ma'anar wajabcin hankali babu abinda take nufi illa fahimtar neman sani da hankali Ya yi da kuma lizimtar yin tuntuntuni da kokari a jiga-jigan  akida.

Koyi da wani a rassan al’amuran addini (taklidi)

Rassan al'amuran addini su ne hukunce hukuncen shari'a wadanda suka shafi ayyuka, su ba hukunce-hukuncen ba ne wajibi a yi bincike da ijtihadi a kansu sai dai ma idan ba su kasance daga cikin muhimman al'amura wadanda suka tabbata da ingantattun hujjoji kamarsu wajabcin salla da zakka da azumi ba to dayan uku ne Ya wajaba:

Ko Ya yi ijtihadi Ya yi bincike a kan dalilan hukunce - hukunce idan yana daga cikin masu iya yin hakan ko kuma ya zama mai ihjtihadi, idan yin ihjtihadi zai wadatar da shi.? kokuma Ya yi koyi da Mujtahidi wanda Ya cika sharruda. Wato Ya zamanto cewa wanda zai yi koyin da shi, mai hankali ne, Adali ,mai kiyaye kansa, mai kare addininsa, mai saba wa son ransa. mai bin umarnin Ubangijinsa"

Duk wanda ba Mujtahidi ba ne kuma ba mai yin ihtiyadi ba.kuma bai yi koyi da mujtahidi wanda ya cika sharuda ba to dukan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, ko da kuwa ya yi salla ya yi azumi ya yi ta ibada duk tsawon rayuwarsa, sai dai idan aikinsa Ya dace da ra'ayin wanda zai yi koyi da shi daga baya,ya kuma yi gamon katar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah ta‘ala.

Ijtihadi

Mun yi Imanin cewa: ljtihadi (matsayin tsamo hukunce-hukunce) a rassan hukunce-hukuncen shari'a wajibi ne da wajabcin kifa'iyya da ya doru a kan dukan musulmi a zamanin boyuwar Imam,wato ma'ana cewa ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Amma kuma idan har wani da zai iya kuma zai wadatar Ya dauki nauyin yi to Ya fadi daga kan sauran musulman, sai su wadatu da wanda Ya dauki nauyin yin hakan kuma Ya kai ga matsayin ijtihadi kuma Ya zamanto Ya cika sharudan, sai, su yi masa takalidi, su yi koyi da shi, su koma gare shi a kan rassan hukunce-hukuncen addininsu.

Don haka a kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami Mujtahidi a tsakaninsu wanda Ya sadaukar da kansa Ya kai ga maisayin Ijtihadi wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo kuma Ya kasance Ya cika sharudan da suka sa Ya cancanci a yi masa takalidi, a yi koyi da shi, sai su wadatu da shi su yi masa takalidi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen addininsu.Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to Ya wajaba a kansu kowane daya daga cikinsu Ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya a tsakaninsu wanda zai dukufa domin kaiwa ga wannan mukami domin ba zai yiwu ba dukansu su dukufa domin neman wannan al'amari ko kuma zai yi wahala, Kuma bai halatta gare su ba su yi koyi da wanda Ya rigaya Ya mutu daga cikin Mujtahidai.

Ijtihadi: shine nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban Manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita, kuma ba ta canzawa ko sakewa da sakewa zamani da kuma halaye "Halalin Muhammadu(SAW) halal ne har zuwa ranar Kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa ranar tashin Kiyama.

Dalilan shari'a su ne: Alkur'ani mai girma, da sunna, da Ijma'i, da Hankali kamar yadda yaka filla filla a littafin usulil Fikhi.

Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar tarin ilimi da sani wandanda ba sa samuwa sai ga wanda Ya dage Ya wahala. Ya sallama kansa, Ya ba da kokarinsa wajen samun sa.

Mujtahidi

Abinda muka yi imani da shi game da mujtahidi wanda Ya cika sharuda: cewa shi Na'ibin Imam (A.S.) na halin boyuwar shi Imam din." Kuma shi mai hukunci ne,shugaba cikakke, abinda yake ga Imam (A.S.) yana gare shi a fannin al'amura da shugabanci a tsakanin mutane kuma duk wanda Ya ki hukuncinsa tamkar Ya ki hukuncin Imam (A.S.) wanda Ya ki hukuncin Imam (A.S.) kuwa Ya ki hukuncin Allah ne wannan kuwa a matsayin shirka da Allah yake, kamar yadda Ya zo a hadisi daga Sadikun Ahlul baiti (A.S.).

Shi Mujtahidin da Ya cika sharruda ba wai madogara ne kawai a wajen ba da fatawa ba. a'a har ma yana da jagoranci  na gaba daya,"don haka ana komawa gare shi a hukunci da raba gardama da shari'a, wannan duk yana daga cikin abubuwan da suka kebantu da shi kuma bai halatta ga wani ba Ya dauki nauyinsu sai shi, sai dai da izininsa, kamar kuma yadda bai halatta ba a yi haddi ko labadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa. "Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebantu da shi.

Wannan matsayin ko kuma shugabanci na gaba daya Imam (A.S.) Ya ba da shi ga Mujtahidi wanda Ya cika sharruda domin ya kasance na'ibinsa wato wakili ko magajinsa a yayin boyuwarsa, wannan shi ne abinda Ya sa ake ce masa "Na'ibin Imam'".

Hafizu Muhammad Sa’id

hfazah@yahoo.com

 



back 1 2