Hukuncin Dukiya



Da wannan ne zamu ga cewa; lallai ilimin fikihu yana iya warware duk wani abu da ya taso na rayuwar dan Adam, don haka ne muka ga ya himmantu da bayani kan alakoki mabambanta, wadannan alakokin sun hada da: Alakar mutum da ubangijinsa, da Alkar mutum da iyalinsa, da Alakar mutum da wasu abubuwa kamar dukiya, da Alakar mutum da al’ummarsa. Wadannan alakokin suna farawa ne tun daga lokacin da aka haife shi har mutuwarsa.

Hakika imam Ali (a.s) ya himmantu da lamurran kula da dukiyar al’umma da kiyaye ta, da matukar yakar kebantarta da wasu mutane a cikin al’umma.

Irin wannan lamarin ne ya kasance a cikin duniyar musulmi kafin zuwan imam Ali (a.s) kuma ya sanya shi cikin wahalar yakar wadannan mutanen Banu Umayya da suka salladu kan dukiyar al’umma kamar yadda ya kawo a wata hudubarsa a cikin Nahajul Balaga.

Idan dai mulkin al’umma ya kasance ya doru ne bisa biyan bukatun mutane, da daukar nauyinsu, to bai halatta ba a kebanci wani aji na mutane da ita, ya zama dole ne ta shiga cikin rayuwar mutane. Imam Ali (a.s) yana cewa da wani daga cikin gwamnonisa: “Ka duba abin da ya taru gunka na dukiyar Allah sai ka yi wa wadanda suke nan hidima da shi, daga masu iyali da talauci, da yunwa, kana mai bin duk inda ake da bukata da rashi, abin da ya rage kuwa sai ka zo mana da shi domin mu raba shi ga wadanda suke gunmu” (Dirasatun Fi Nahjil Balaga: Muhammad Mahdi Shamsuddin; s 135).

Akwai irin wadannan kalamai na imam Ali (a.s) ga wadanda yake turawa don kula da dukiya ko kuma gwamnoni a garuruwa masu yawa shigen irin wannan. Kamar Ash’as dan Kais gwamnansa na Azarbaijan, da Ziyad dan Abihi, da sauran mutanen da yake turawa don kula da ayyukan Sadaka, da Maskala dan Habira, da Usman dan Hanif, da Usum dan Abbas.

Kamar yadda imam Ali (a.s) ya yi nuni da raba dukiya ga al’umma da yi musu hidima da ita daidai gwargwadon yanayi da yanayin hidimar da suke bukata a cikin wani hadisi da fadinsa: “Amma hakkinku a kaina shi ne in yi muku nasiha, in tanadi dukiyarku, in sanar da ku domin kada ku yi jahilci, in ladabtar da ku domin ku yi ilimi” (Nahajul Balaga: Bayani 34, shafi 138).

Sannan malamai sun rarraba dukiya bisa la’akari da sanin mai ita, da saninta ko rashin hakan kamar haka:

 

1- Sanin Mai Dukiya Da Sanin Adadi

Dukiyar da aka san mai ita da adadinta; ita wannan dukiyar hukuncinta shi ne a bayar da ita ga mai ita, kamar yadda take da adadinta. Wannan lamarin kuwa a fili yake idan muka duba shi a matsayin asasin rayuwar al'umma ta yau da kullum.



back 1 2 3 4 next