Sakon Annabi Muhammad (s.a.w)



Musulunci ya sanya lamunin rayuwa ta hanyoyi masu yawan gaske, sai ya shimfida dokokin da zasu wadatar da dan Adam kamar zakka, humusi, sadaka, Baitul mali, kyauta, da ayyukan jin kai, sannan ya yi matukar gaba da jahilci da ba a taba samu ba a rayuwar dan Adam, sai ya tilasta neman Ilimi ko da kuwa a kasar Sin ne. Musulunci ya yi gaba da rashin ganin kimar dan Adam matuka, har ma ya ‘yanta bawa saboda ubangidansa ya yanke masa al’aura. Kai hatta da iradar yara da ‘yan mata yayin zabin wanda zasu aura ya ba ta kariya. Sannan a fili yake hatta da addini bai tilasta kowa riko da shi sai wanda ya ga dama.

Sannan musulunci bai taba yarda da zubar da jinin mutum ya tafi a banza ba, don haka ne ma muke kira da gwamnati da ta biya diyya ga iyalan wadannan mutanen da aka kashe wadanda ba su ji ba su gani ba, kai hatta da kisan kare dangi da aka yi wa musulmi da sunan baki a Jos a watan Safar 1431 muna neman a biya su diyyar wannan bala’in da ya fada musu. Jinin mumini ba ya faduwa haka banza ya wuce sai an biya diyyarsa, kuma ya hau kan gwamnati ne ta mika diyya ga danginsa, duba wannan misali mai zuwa da zai nuna maka matukar kima da sakon Muhammad (s.a.w) yake bai wa dan Adam kamar haka:

Kulaini ya karbo daga Hasan ya ce: Yayin da Sayyidi Ali (a.s) ya rusa rundunar Dalha da Zubair (r) sai mutanen suka gudu suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi bari saboda tsoro, kuma dan nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu, sannan sai uwar ta mutu. Sai Imam Ali (a.s) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da danta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?. Sai suka ce: Tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yaki da rushewar mutane da gudunsu. Sai ya tambaya: Waye ya riga mutuwa a cikinsu?. Sai suka ce: Danta ya riga ta mutuwa.

Sai ya kira mijinta baban yaro mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar dansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga dansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da dari biyar, sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da dari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani da banda wannan da ta jefar da shi -barinsa- ya mutu. Ya ce: Wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara. (Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa'il, mujalladi 17, shafi: 446).

Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al'ummar musulmi da biyan bukatunsu, da bayar da hakkokinsu. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Hakkin mutum musulmi ba ya faduwa banza. (Manla yahaduruhul fakih, mujalladi 4, shafi: 100). Wani hadisin ya zo cewa: Jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al'umma da yalwa da arziki, da lamunce rayuwa, da adalci.

Musulunci ya zo da tsarin da ba shi da misali: ya haramta, ya wajabta, ya kwadaitar, ya karhanta, ya halatta. Duba abubuwan da aka wajabta a musulunci guda: 115, da kuma wadanda aka haramta guda: 97, da wasu: 112, da munanan halaye guda: 95, da kuma kyawawan halaye: 83, a littafin Tafarkin Rabauta.

Duba a ci gaban makalar a bayani mai suna: Musulmin Duniya.

 

Hafiz Muhammad

hfazah@yahoo.com

Thursday, March 11, 2010

 



[1] Shi rahama ce da kariyar al'umma daga dukkan musibu da sukan faru kamar gobara da girgizar kasa, da mamayar hamada da sahara, da kuma guguwar teku, da ambaliyar ruwa, da iska mai karfi.

[2] Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 13, shafi: 151.

[3] Mustadrikul wasa'il, mujalladi 2, shafi: 490.

[4] Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 490.



back 1 2 3 4