Mauludin Annabi (s.a.w)



Sannan kuma ga wata ayar tana cewa: "...Kuma ba a sanya muku wahala a cikin addini ba..." (Hajji: 78), da take nuni da cewa; Babu wani kunci da dabaibayi da aka yi mana a kan halaccin abubuwan da haramcinsu ko halaccinsu bai bayyana ba. Don haka hannyenmu a sake suke babu wani kaidi da kuntata wa kawuka. Sannan kada wani ya ce: Ai tana dauke hukunci ne ta mayar da shi yalwa ga abin da ya ta'azzara ko ya wahalar? Sai na ce: A nan ma akwai kunci domin duk haramta alheri a cikinsa akwai kunci, kuma duk halal a cikinsa akwai yalwatawa, don haka wannan ayar tana shafar abin da muke magana a kai.

Ayar nan da take cewa: "Kuma amma ka zantar da ni'imar Ubangijinka" (Dhuha: 11). Musulmi bai san wata ni'ima da zai ambace ta ya ji dadi da tafi samuwar Annabi (s.a.w) ba, kamar yadda Allah (s.w.t) bai kayyade mana nau'in ni'imomin ba, don haka ne ma ya ce: "Ni'imar Ubanginka" ba tare da ya kayyade su ba, sai kayyade su ya sanya shi a hannun mutane, domin su ne suka san ni'imomin da ya yi musu. Sai dai ya bayyana musu wasu daga ciki amma fa ba domin ba su san su, sai domin ya karfafa wa hankali abin da yake riskarsa domin tunatar da shi ni'imominsa.

A wata ayar kuwa madaukaki yana cewa: "Babu wani alheri a cikin ganawarsu -taronsu- sai wanda ya yi umarni da sadaka ko wani kyakkyawa, ko gyara tsakanin mutane...". Ashe akwai wani alheri da ya fi taruwa da tuna wa mutane ni'imomin Allah da rayuwar annabinsu, da nuna musu kyakkyawan koyi a cikinsa?! Yanzu akwai wani mai basira da zai haramta taruwa irin wannan?!

Da wani zai yi raka'a dari biyu kowace rana ba tare da ya jingina ta da wata aya ko ruwaya ba, sai dai kawai domin yana son ya aikata alheri don samun lada. Sai ka ga mai irin wannan tunanin musun Mauludi ya ce: Ba komai, da hujjar cewa kyakkyawan abu ne. Sai dai a nan wani yana iya cewa: Ai sallar asham a zahiri kyakkyawa ce domin ibada ce, amma sai ga shi a shari'a tun farko manzon Allah (s.a.w) ya hana ta, sai dai Halifa na biyu ne ya dawo da ita kuma ya yi mata kirari da "Madalla da wannan bidi'a!. Don me Mauludi ba zai zama irin wannan ba!?

Sai in ce masa: Abin da manzon Allah (s.a.w) ya hana shi ne yin ta jam'i a masallatai a dararen Ramadan, da umarnin da ya yi na su yi ta daidaiku -a gidajensu- domin jam'i a sallar nafila ba ya inganta[1]. Don haka ne ma Imam Ali (a.s) ya hana jam'in ta a masallatai a lokacin da ya zo Kufa ya ga mutane suna yi yayin da ya aika Imam Hasan (a.s) ya shelanta haramcinta bisa sunnar Annabi (s.a.w), sai masallaci ya kaure da ihun Wayyo zai kashe sunnar Umar! (Muntahal Madalib: Allama Hilli; 358-360). Duba littattafai kan sallar Tarawihi kamar: (Buhari, da Muwatta, da Muslim).

Sai dai Halifa na biyu ya mayar da ita farkon dare, kuma ya sanya mata jam'i, sabanin umarnin manzon Allah (s.a.w) da ya hana jam'inta ya sanya karshen dare ya fi farkonsa. Sai lamarin sallar asham ta bidi'a ya yi kama da mai yin sallar azahar raka'a takwas ne da nufin ninka ladanta, a maimakon ya yawaita ladansa sallarsa zata bace ne.

Da wannan ne magana zata fito a fili cewa: Babu wani abu da yin sa yake haram shari'a ba ta yi bayaninsa ba ko da kuwa a zahirinsa wani yana ganin kyawunsa. Don haka idan wani abu ya zo mana wanda muke kokwanton muninsa ko kyawunsa, da hukuncin wadannan ayoyin da wasunsu ma yana nuna babu laifi a kan yin sa. Sannan mai Mauludi yana kafa hujjarsa da dokokin shari'a ne tabbatattu wadanda suke iya tabbatar da duk wani alheri ko wane iri ne kuwa har zuwa karshen duniya ba tare da da'awar nassi ba.

Sau da yawa da za a canja wa bikin Mauludi suna da wa'azin kasa, ko tunatarwa, ko ambaton rayuwar Manzo, da mai kin sa ya karba yana mai yarda. Amma saboda kawai an sanya masa kalmar sunan "Murnar Haihuwar Annabi" to sai ya zama laifi babba da zukata suke bakin ciki da shi. "... Ka ce: Ku mutu da bakin cikinku"!.

Idan ka ce: Wasu suna aikata haramun lokacin Mauludi, kamar kawo 'yan mata su yi rawa a gaban samari da sauran jama'a? Sai in ce maka: Ya kamata ne ka yi fada da haramun da aka sanya a cikin wannan taro, da kokarin ganin an fitar da ita daga ciki, ba fada da asalin taron ba. Domin wani lokaci a tarurrukan wa'azi har fada ne yake kaurewa, amma ba ya haramta yin taron wa'azi!.

Da zamu tsawaita magana kan Mauludi ne da yana bukatar littafi ne cikakke, sai dai zamu dakata hakan.

Duba a ci gaban makalar a bayani mai suna: Sakon Annabi Muhammad (s.a.w)

Hafiz Muhammad

hfazah@yahoo.com

Thursday, March 11, 2010

 



[1] Wasu malaman sunnan sun ruwaito cewa; ya hana ne domin jin tsoron kada a wajabta ta.



back 1 2