Sayyid Khamna'i



AMSA:E, lallai kuwa, hakika irin matsayin da yake da shi na Jagoranci ya kere dukkan sauran matsayi da daukakan da yake da shi, shi dai mawaki ne kamar yadda kuma ya kasance masanin adabi a daidai wannan lokaci. Hakika waken da ya rubuta suna cike da fasaha da kuma ma'ana. Kamar yadda kuma Mai Girma Jagora ya kan zauna da mawaka tun shekaru sai dai hakan ba wai a koda yaushe ba ne. A lokacin da ya zauna da sanannun mawaka kuma suka gabatar da wakensu, to fa a duk lokacin da Jagora ya budi baki don ba da ra'ayinsa kan wakan za ka ga sanannun mawakan suna jinjina masa da kuma girmama irin ra'ayin da yake bayarwa saboda irin masaniyyar da yake da ita kan wake. A hakikanin gaskiya dai Jagora ya kan gabatar da sabbin abubuwa ne a lokacin da yake ba da ra'ayin nasa, don yana da cikakkiyar masaniya a fannin adabi da kuma wake. Watakila ka ji jawabin da ya yi a yayin bukin girmama (sanannen mawakin nan) Hafiz Shirazi, lalle babu wani wanda ya taba magana kan Hafiz da irin shakalin cikakke kamar yadda Jagora ya yi.

Jagora Tare Da Daya Daga Cikin Iyalan

Shahidai Daya kuma daga cikin ayyukan da yake yi shi ne ziyarar iyalan shahidai, ya kan kai irin wadannan ziyara ne kuwa ba tare da an sanar da iyalan da za a kai musu ziyarar cikin lokaci mai tsawo ba. A takaice dai iyalan da za a kai musu ziyarar ba sa sani waye ne zai kawo musu ziyara, har sai Jagoran ya iso kafin su san wane ne ya kawo musu ziyaran. Kafin nan dai akan buga musu waya a sanar da su cewa wani jami'in gwamnati zai kawo musu ziyara, hakan ma don a tabbatar da cewa suna gida ne, don haka ana bukatan su kasance a gida. A wasu lokuta na kan raka shi kai irin wadannan ziyarce-ziyarce. A rana guda ya kan kai ziyara ga iyalan shahidai kimanin uku ko hudu ko kuma biyar.

TAMBAYA:To ya ya ake zaban wadannan iyalan shahidai?

AMSA:Abin ban sha'awan shi ne cewa akan zabi iyalan da suke zaune ne a guraren da marasa abin hannu suke, wato wadanda suke nesa da gari, don kai wannan ziyara, da wuya ka ga Mai girma Jagora ya kai ziyara yankunan da masu abin hannu suke zaune, kuma a mafi yawan lokuta ya fi kai ziyara ga iyalan da suka ba sadaukar da shahidai biyu, uku ko kuma hudu. Wannan ganawa dai da jagoran ya ke yi da iyalan shahidan ta kan kasance abin sha'awa da kuma kaunar juna, ya kan yi kimanin minti talatin ko fiye a kowani gida da ya kai ziyara. Da farko dai ya kan bukaci a kawo masa hoton shahidin, daga nan kuma sai a bukaci a yi masa bayani inda shahidin ya yi shahada da kuma yadda ya yi shahadan. Jagoran ya kan yi mu'amala da iyayen shahidin cikin tausayawa da kuma kauna, idan kuwa shahidin yana da kananan yara, ya kan dauke su ya zaunar da su akan cinyarsa yana rungumarsu da nuna musu soyayya da kuma kauna.

Dukkan maganganun da ya kan yi dai sukan shafi shahidi ne, matsayin shahidi da kuma kaunar shahidi...a wasu lokuta ma dai iyayen shahidin sukan gagara magana, sai kawai su fashe da kuka saboda shaukin ganawa da suka yi da shugaba abin kauna, ba sa iya gaskata kansu kan cewa yau ga Jagora ya kawo musu ziyara don tattaunawa da su. Na sha jin da dama daga cikin iyayen shahidan da aka kai musu ziyarar suna cewa sun yi mafarkin cewa daya daga cikin waliyan Allah zai kawo musu ziyara rana guda kafin a kawo ziyarar. Wannan dai na daga cikin ayyukan Jagora na koda yaushe.

Daga cikin ayyukansa kuma har da ziyarar da yake kai wa garuruwa daban daban, a lokuta da dama ya kan zabi garuruwan da aka bar su a baya ne wadanda suke da nisa don kai musu ziyara. Hakika irin wadannan ziyara suna dadada rai kamar yadda kuma irin tarbar da al'umma suke masa ba ta kwatankwaci. Daga cikin ayyukan da yake yi a yayin wannan ziyara har da ganawa da al'umman yankin. A kowane lokaci za ka dogon layin mutane da ya kai kilomitoci wadanda suka taru don yi masa maraba, shi kuma ya kan tarbe su da so da kauna da kuma budaddiyar zuciya, a wannan lokaci maza da mata sukan iso don ganawa da shi kuma hakan babban abin farin ciki ne ga su kansu al'umma din. Jagoran dai ya kan yi musu jawabi da kuma jin irin halin da suke ciki gwargwadon yadda lokaci ya ba shi dama.

A yayin wannan ziyara dai mu kan ayyana wasu mutane daga cikin ma'aikatan ofishin nasa don amsa wasikun mutane da kuma magance musu matsalolinsu, a wasu lokuta ma wadannan mutane sukan zauna a wannan gari har na tsawon wasu kwanaki don magance matsalolin al'umman yankin.

TAMBAYA:Mutane za su so sanin yanayin tattalin arzikin Jagoransu, zai yi kyau idan da za ka mana bayani kan yanayin tattalin arzikin Jagora, a wani irin yanayi ne yake rayuwa, kuma ta ina ne yake samun abin da yake rayuwa da shi da kuma irin dukiyar da ya mallaka?

AMSA:Ina iya cewa yanayin rayuwar Mai Girma Jagora dai, duk kuwa da irin damar da yake da ita na amfana da dukkan abubuwan da ake da su, ba ta dara yanayin yadda sauran mutanen da ba komai ba suke rayuwa. Hakika ya takaita da wannan yanayi kuma yana rike da shi, a koda yaushe kuma ya kasance mai yin wasiyya ga jami'an gwamnati da su guji yin almubazzaranci. Babu laifi idan na bayyana cewa daga cikin irin ayyukan da Jagora ya ke yi a lokutan bukukuwa na musamman na addini shi ne gudanar da bukukuwan daurin aure, a wannan lokaci ya kan tara samaruka goma zuwa sha biyu, mafi yawansu 'ya'yan shahidai ne ko kuma mutane muminai, misali a lokacin bikin aiko Manzon Allah (s), to Jagoran ba karban abin da ya wuce sisin zinare guda 14 a matsayin sadaki, ba wai yana ganin hakan ya saba wa shari'a ba ne, face dai yana da ra'ayin cewa lallai ne a kirayi mutane wajen rayuwa mai sauki, idan har sun bukaci su sanya sadaki mai yawa sama da sisin zinare 14, to Jagoran ya kan bukace su da su je wani waje don daurin auren, ya kan sa hakan a matsayin sharadi. Sai dai kuma ba ya hana a kara da aikin hajji ko kuma Umra akan wannan sadaki, hakan kuwa saboda wannan aiki ne na ibada.

Wani abin sha'awa shi ne mintoci sha biyar kafin daurin auren ya kan gudanar da jawabi da kuma ba da shawarwari ga ango da amarya dangane da rayuwa cikin sauki, ya kan shawarce su da su yi watsi da rayuwa ta jin dadi da almubazzaranci. Shi kansa ya kan lizimci wannan abu da yake fadi.

Amma dangane da masdarin kudaden da yake rayuwa da su, yana da kyau ka san cewa, Jagora dai ba shi karban wani albashi daga wani waje kamar yadda kuma ba ya amfani da kudaden da suka shigo hannunsa daga wasu gurare (kamar khumusi da sauransu) don amfanin kansa, face dai ya kan rayu ne ta hanyar kyaututtukan da masoya da mabiyansa suke ba shi. Hakan 'ya'yansa ma suke rayuwa akan wannan tafarki na sa, su ma suna rayuwa ne kamar yadda yake rayuwa cikin sauki.

 



back 1 2 3