Hadisin Manzila



3.    Kamar yadda mutane suke bukatar annabi (a.s) haka ma suke bukatar imami (a.s), sai dai sakon Manzon Allah (s.a.w) shi ne karshe, don haka shi ne mafi cancanta ya samu masu kiyaye shi don gudun hannun da yake iya gurbata sakon

Bisa wannan dalilai ya zama wajibi ga Allah ya sanya mai gadi, mai kiyayewa, mai fassara, mai bayani ga al’umma da abin da sakon yake kunshe da shi bayan wucewar annabi (s.a.w).

Akwai dalilai da dama daga kur’ani da hadisai da suka zo game da hakan, kamar fadinsa madaukaki: “Kawai kai mai gargadi ne kuma ga kowane mutane (mun sanya) mai shiryarwa”[1].

Manzon Allah a tafsirin wanann aya yana cewa: “Ni ne mai gargadi Ali kuma mai shiryarwa”. A wata ruwaya fadinsa mai tsira da amincin Allah: “Da ni ne aka yi muku gargadi, da Ali ne aka shiryar da ku”[2]. A wata ruwaya Manzon rahama yana cewa: “Ya Salman wanda ya mutu daga al’ummata kuma ba shi da imami daga cikinsu, ya yi mutuwar jahiliyya”[3].

Kamar yadda Manzon rahama ya yi bayanin cewa bayansa halifofinsa goma sha biyu ne kuma wannan ruwaya ta zo da littattafai na Ahlussunna masu yawa kamar Sahih Muslim. Sannan kuma a wasu littattafai ya ambaci sunayensu, muna iya kawo misali daga littafin tafsirn Ibn Kasir:

Ya zo a Tafsirin Ibn Kasir a tafsirin aya ta 55 ta Surar Ma’ida cewa: Daga Maimun Dan Mahran daga Ibn Abbas, a fadin Allah mai girma da buwaya. “Kawai majibancin lamarinku (Jagoranku) Shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadanda suke tsayar da Salla suke bayar da Zakka alhalin suna masu ruku’u”. Yana mai cewa: Ta sauka ne game da Muminai kuma Ali Dan Abu Talib (a.s) Shi ne na farkonsu. Wato tana mai nuni da cewa na farkon wadanda za a mika wa wilaya da Shugabanci bayan Allah da Manzonsa shi ne Ali (a.s) Sa’annan masu biyo wa bayansa na daga wasiyyai, kamar yadda zamu ga ta sauka ne a lokacin da ya yi sadakar zobensa alhalin yana cikin ruku’i. Wasu littattafan suna cewa; ta sauka game da muminai Ali (a.s) ne na farkonsu, Mahadi (a.s) na karshensu.

Hada da hadisai da suka zo game da wannan al’amari da suka hada da; hadisuddar, da hadisin wilaya, da hadisin jirgin ruwa, da hadisin aminci, da hadisin sakalain, kuma da hadisul manzila da muke magana a kai.

Hafiz muhamad Sa'id

Thursday, September 24, 2009



[1] - Surar Ra’adi: 7.

[2] - Gayatul marami: 235. Al’aka’idul hakka: 283.

[3] - Biharul anwar:23/88.



back 1 2 3