Karya da Tsoro gun Yara



A nan yana kan iyaye su kasance mutane masu yafiya da rangwame ga kurakuran yaransu, domin kada su sanya su fadawa cikin wannan mummunan halin, sai su nemi su gaya musu gaskiya, sannan su yi maganin abin ta hanya mai sauki, ko yafewa da afuwa.

Karyar Koyi: Wannan ita ce mafi munin karya, domin karya ce da yara sukan yi sakamakon sun ga iyayensu suna yi, wannan ya hada da rashin cika alkawari. Idan yaro ya ga iyayensa suna cutar da makota ko abokan mu'amalarsu, ko ba sa cika alkawari, sai ya dauki wannan dabi'ar a matsayin wani abu mai kyau, har ta zamo masa dabi'a.

A nan babu wata mafita sai iyaye ko wadannan mutanen na kusa da shi a matsayin abin koyi su yi kokarin gyara halayensu, da haka ne zai fahimci munin abin shi ma ya nisance shi[2].

Karyar Rudewa: Kamar yadda rudewa take samun wasu tsofaffin mutane, haka ma take samun yara kanana, wasu yaran suna da dabi'ar rudewa, duk wani abu ya same su, sukan dauki matakin rudewa a kansa, wannan lamari sau da yawa yakan sanya su yin karya. Sau da yawa wani yaro yakan nuna wani ya ce ya doke shi, alhalin ba shi ba ne; wani yaro ya taba nuna gidan wani mutum wanda ba shi ya doke shi ba, ita kuwa uwar yaro sai ta zo ta yi sallama da mai gidan, da ya fito sai ta fara zaginsa, sai ya tsaya yana mamaki, da yaron nata ya zo sai ya ce kuma ba shi wannan mutumin ba ne ya doke shi.

Shi dai wannan yaron sau da yawa yakan fadi, ko ya yi tuntube ya yi ta kuka, idan iyayensa sun tambaye shi wanda ya yi masa, maimakon ya ce; ya fadi ne, sai ya duba ya ga sa'adda ya fadi wane yaro ne kusa da shi, sai ya laka masa karya, su kuwa iyayensa sai su bi wancan yaron su doka. Wannan lamarin ba komai ya nuna wa jama'ar wurin ba sai karancin hankalin iyayensa, ta yadda ya kai ga wasu yara sun taba zagin babansa saboda ya doke su haka kawai sakmakon dogaro da maganar dansa. Don haka ne yana da kyau iyaye su sanya hankali a cikin tarbiyyar 'ya'yansu ba makauniyar kauna ba, makahon so ba ya kai su ko'ina sai nadama.

Tsoro Gun Yara

Tsoro wani hali ne da yake daga dabi’ar mutum, yakan iya karuwa ko raguwa ta hanyoyi daban-daban, ga yaro tsoro wani abu ne da yana iya tasowa da shi, yarinta abu ne mai cike da tsoro musamman saboda yara suna cike da jahiltar abubuwa da dama wadanda a bisa dabi’arsu yana iya tsorata su ko ya kayatar da su. Haka ma rashin sabo yakan sanya yara tsoron abubuwan da suke kewaye da rayuwarsu, hada da raunin da suke da shi, da karancin karfin da zasu iya kare kawukansu daga abubuwa masu hadari.

Mutumin da yake tashi a matsoraci ba ya iya amfanar al’ummarsa ko ya kawo mata wani sauyi, wannan kuwa haka yake ga mai kawo sauyin gyara a cikin al’ummarsa wanda yake salihi irin Shehu Dan Fodio (r), ko mutumin da yake mabarnaci Hetla, don haka ne ake son yaro ya tashi da kwazo, da jarumtaka, da juriya. Matsoraci ba zai iya tabuka komai ba, sannan zai samu faduwar gaba a duk abin da ya sa gaba, don haka ne ba zai iya zama mai juriya da sadaukarwa ba, kuma ba zai iya samar wa al'ummarsa canji ba.

Tsoro yakan sa mutum ya fita daga halinsa na dabi’a har ya yi galaba a kan iradarsa da azamarsa ya zama mutum mai rauni, ya rasa karfin tabuka komai. Saboda haka; ba wa yara labari da tatsuniyoyi na ban tsoro da sukan iya rusa musu irada da niyya, da azama, yana daga mummunan abu. Wani lokaci domin uwa tana son yaro ya yi shiru, sai ta ba shi tsoro kamar ga mage nan! ko ga sunan! mu sani fa wannan lamari ne mai matukar muni.

Tsoro ga yaro ya dan bambanta da tsoro gun manya, domin tsoronsa bai doru bisa dalili na hankali ba, misali yaro yana tsoron duhu; don haka ne ma bai dace ba a yi bacci tare da yaro sai kuma a tashi a bar shi a cikin duhu, wannan yana iya sa yaro ya tashi a gigice har ma yana iya fadawa kan wani abu da kan iya yi masa lahani. Tsoron talauci ya doru kan hankali ne, irin wannan yana tasowa daga tunanin matsalolin rayuwa ne, don haka irin wannan yana kebantuwa da manya ne.

Yaro yakan ji tsoron wanda bai sani ba da wanda bai saba da shi ba, shi ya sa idan zaka je wani gida don ganin kananan yaran ‘yan’uwanka da ba su sanka ba, kuma kana so su saba da kai, sai ka kai musu wani abu kamar kayan wasanni da wasu abubuwa da yara suke so, kuma ka yi musu wasa. A lokacin ne zaka ga sun kawar da wani tunani na bakunta da suke da shi game da kai na tsoron wanda ba su sani ba daga tunaninsu, ko kuma ya ragu sosai.



back 1 2 3 next