Karya da Tsoro gun Yara



Yana da kyau mu san dalilin da yake sanya yara yin karya domin mu san yadda zamu bullo wa abin, domin kada manyan gobe su taso da wannan dabi'a mummuna a cikin al'ummarsu, don haka zamu yi nuni da wasu bayanai game da kashe-kashen karya a takaice kamar haka:

Karyar Sake-saken Tunani: Irin wannan karya ita ce; wacce yaro yakan yi saboda wasu abubuwa da suke yi masa yawo a tunani, sau da yawa tsoro a duhu, ko a mafarki, ko jin wani labari mai ban tsoro ga yaro, yakan sanya shi bayar da labarin abubuwan da zuciyarsa ta sawwala masa. Irin wannan lamarin ba ya kasancewa daga karya mummuna, yana kama da aikin mawaka da masu kirari ne da suke suranta wani abu su kamanta shi da mutum, wannan lamarin yana nuna karfin tunanin sake-saken zuciya da yaro yake da shi ne, don haka sai iyaye su yi amfani da wannan damar domin tarbiyyantar da yaro.

Karyar Rikirkicewa: Sau da yawa wasu lamurra sukan faru sai su cakude wa yaro, sai ya kasa bambance gaskiyar lamari, sai ya rika ganin abin da ba gaskiya ba shi ne gaskiya. Kamar ya ji wani labari, ko ya ga wani mafarki, sai ya dauka gaske ne, ko kuma ya ji wata tatsuniya har ta sanya shi tunani kan abin saboda gaskatawarsa da shi. Kuma yana iya dora wasu ayyukansa da tunaninsa a kan wannan mafarki ko tatsuniya, har ma ya rika bayar da labarin abin kamar dai ya faru. Shi ma wannan nau'in ba shi da aibi, domin yana girma yana yin wayo, sai irin wadannan tunani su kawu da kansu.

Karyar Kirkira: Yaro ba ya son jingina masa aibi, kamar yadda ba ya son jingina wa babansa ko wani na kusa da shi wata tawaya, don haka ne yana iya yin karya domin ya kawar da jin tawaya daga kansa. Kamar dai ya yi da'awar cewa shi ma babansa yana da wani abu don saboda abokinsa ya fadi na babansa domin kada a ga babansa yana da tawaya. Wani lokaci kuma yana iya yin karya domin shi ma a kula da shi, kamar ya nuna kamar ba shi da lafiya saboda a dauke shi, domin yana ganin tun da aka samu sabon jariri an watsar da shi. Don haka yana da kyau iyaye su kula da irin wadannan abubuwan domin gudun kada a samu girman jin tawaya ga yaro, sai ya haifar masa da wannan hali mummuna na yin karya da jin kaskanci. Saboda haka ya hau kan iyaye su nuna masa halin da yake ciki na yin wayo da girma ba tawaya ba ne nau'i ne na ci gaba domin ya yarda da halin da yake samun kansa a kai.

Jin kaskanci ga mutum yana da hadari matuka, don haka ne zamu ga ruwaya ta yi nuni da hadarin hakan kamar yadda zamu gani: Imam Ali al-Hadi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ransa ta wulakanta (a gunsa), to kada ka aminta daga sharrinsa”[1].

Karyar Hadafi: Ita irin wannan ita ce karyar da yaro yake yi domin cimma wani hadafi nasa. Kamar idan yana son babansa ya ba shi kudi ya sayo alewa, sai ya ce; yana son kudi domin ya sayo wa kaninsa alewa, ko kuma domin ya sayo wa babarsa wani abu. Ita ma wannan nau'in tana da muni, don haka idan an gane yana da wannan halin sai a kawar da shi da tarbiyya ta gari, da ganar da shi munin wannan nau'in karya. Sannan a dauki matakin kamar cewa; idan ya sake yi to za a hana shi abin da ya nema, da sauran hanyoyin da malaman tarbiyya suka yi nuni da su.

Karyar Daukar Fansa: Iyaye su gane cewa yara sukan yi wa junansu karya domin su dauki fansa, ko su huce haushinsu a kan 'yan'uwansu da suke ki. Wadannan sabuban kin suna da yawa da wasu ba a iya gane su, wasu kuwa yana yiwuwa a gano su ta hanyar maganganun yaro kan dan'uwansa. Idan yaro yana jin ba a daidaita shi da dan'uwansa, to lallai zai shiga yi masa kulle-kulle da dubarunsa, don haka yana iya yi musu karyar da zata kai ga a yi musu wani abu kamar duka don ya ji dadi ya huce haushinsa.

A lokaci guda kuma su wadanda aka kawo kara, idan ya kasance babu wani laifi da suka yi, sai iyaye suka hukunta su, zai zama suna ganin iyaye sun zalunce su ne. Kuma su ji haushin dan'uwan nasu, kuma ta yiwu su nemi hanyar daukar fansa, daga nan sai gaba, da kiyayya, su yi kamari a tsakaninsu. Don haka yana da muhimmanci iyaye su san da irin wannan halaye, su rika bincike duk sa'adda aka kawo karar daya tsakanin 'ya'yansu.

Haka nan idan yaran unguwa suka san idan sun yi wa yaro karya a gidansu ana dukansa, wasu mugwayen yara masu keta suna iya samun wannan damar su takura wa yaro kan ya yi wani abu, idan ya ki sai su je su gaya wa gidansu karya a kansa don a doke shi. Sukan iya sanya shi ya yi munanan abubuwa, kai har ma sukan iya sanya shi sato wani abu na gidansu ya kawo musu, idan ba haka ba, sai su yi masa kage gun iyayensa domin ya sha duka. Akwai abubuwan lura masu yawa game da rayuwar yara, don haka ya hau kan malaman tarbiyya, da iyaye, da sauran jama'a, su dage wurin ganin an samu yara na gari a cikin al'ummarsu.

Karyar Kare Kai: Ita wannan karya ce da yaro yakan yi ta domin ya kare kansa daga duka ko cutuwa. Wani yaro yakan yi irin wannan karya domin ya kare matsayinsa da kimarsa da ake ganin sa da ita, kamar idan ya yi abin kunya alhalin ana ganin sa da kirki, to sai ya yi karya domin kare wancan matsayin. Ko kuma idan ya san akwai ukuba ko gargadi da za a yi masa sakamakon wani abu da ya yi, tayiwu ya yi da gangan ne ko da kuskure, muhimmi dai a nan shi ne; ya yi karya. Mafi munin wannan karya shi ne ya yi wa wani wanda ba ruwansa sharri kan abin da ya yi domin shi ya kubuta, ko kuma ya ce tare da wane muka yi saboda kawai yana kin sa.



1 2 3 next