Mu'amalar Tarbiyya



Da akwai nau’i na soyayya da a kan kebanci yara da shi wanda su kan su manya babu wani abu da sukan ji don an ba wa yara irin ta, irin wannan ne Annabi Ya’akubu (a.s) ya bai wa Yusuf da dan’uwansa Bunyamin, sannan akwai fifiko da kebanta da zabi daga Allah gare shi wanda bai buya ga kowa ba.

A sanadiyyar wannan son ne ‘yan’uwan Annabi Yusuf (a.s) suka gaya wa babansu Annabi Ya’akuba suna masu jin haushinsa cewa: “Lallai kai kana cikin dadadden sonka”[5]. Irin wannan kuwa ba ya shafar ismar[6] Annabawa, sai dai su ‘yan’uwan Yusuf (a.s) sun kasance mutane ne mahassada ga ‘ya’yan babar Yusuf (a.s) wacce take kishiyia ga babarsu. Sannan a nan akwai nuni ga cewa su uwaye mata su yi kokarin ganin hadin kan ‘ya’yansu domin kada a samu irin wannan tsakanin ‘yan’uwa a cikin gida.

3- Gasa tana daga cikin hanyar tarbiyyar yara mai muhimmanci; ga wanda yake son karfafa zumuncin yaransa da dankon soyayya tsakaninsu, yana iya shirya musu gasa. Ana iya shirya wa yara gasar bayar da kissa, da tarihin Annabawa, da karatun Kur’ani, da kwarewa a salla ko alwala, ko ta rashin jin wani zagi; kamar gasar cewa duk wanda a wannan satin ba a ji ya yi zagi ba, to za a ba shi kyautar sabuwar jakar zuwa makaranta.

Amma mu sani cewa duk yaron da ya kiyaye, to ya zama dole a yi masa abin da aka alkawarta da gaggawa, idan ba haka ba zai zama abu mafi sauki wajan rusa tarbiyya da himmar yaro, maimakon gina yaro sai ya kasance an rusa shi ne. Don haka alkawarin da ba za a iya cika masa shi ba, daukarsa yana daga cikin mafi munin hadari, idan an san ba za a iya cika masa shi ba, to tun farko kada a dauka.

Amma a kyautar gasa sai a saya da yawa, wanda ya yi na daya sai a bashi kaso mafi girma, na biyu a kokari yana biye masa, sannan sai na baya har zuwa na karshe, domin yara ba kamar manya ba ne, idan ba a basu ba, to za a karya zuciyarsu ko da kuwa ba su yi nasara ba.

Gasa ta zo a littafi madaukaki, duba abin da ya zo a Surar Yusuf game da ‘yan’uwansa, da Madaukaki yake cewa: “Suka ce: Ya babanmu lallai mu mun tafi muna gasar tsere kuma muka bar Yusuf a wurin kayanmu…”[7].Sa’annan wannan yana nuna mana muhimmancin wasanni da tsalle-tsalle ga yara da samari.

Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com

Sunday, November 15, 2009


[1] Yaron ya zauna wurinsu ne saboda shi ne ya kawo musu abinci da ruwan sha.

[2] Majma'uz Zawa'id, alhaisami, j 8, shafi: 159.

[3] Biharul Anwar, j 101, shafi: 92.

[4] Markazur risala, hukukul ijtima’iyya: s 95. Tafsirul Ayashi: 2/166. Kanzul ummmal: 16/446, h 45358.

[5] Yusuf: 95.

[6] Isma shi ne cewa: mai dauke da wannan siffa ba ya sabo.

[7] Yusuf: 17.

 



back 1 2 3 4