Cutarwa



Cutarwa

Duka yana daga cikin makami da manya kan yi amfani da shi a kan yara, amma ya kamata su sani cewa don ka haifi yaro ba yana nufin kana da ikon cutar da shi ba[1], domin yaro amana ce da Allah ya ba ka. A bisa koyarwar musulunci babu mai ikon dukan yaro sai mahaifinsa kawai, don haka Uwa, ko malami, ko makoci, ba su da ikon dukan yaro sai da izinin shugaban daular Musulunci idan akwaita, ko kuma izinin babansa[2].

Sayyid Sistani yana cewa: Ya halatta dukan ‘yan makaranta idan suka cutar da wasu, ko suka aikata haram, amma da izinin waliyyansu (Uba), kuma dole ne dukan ya kasance ba mai sanya fata ta yi ja ba (ta tashi), idan kuwa ya kai ga hakan sai an biya diyya[3].

Shi ma Uba, ba a yarda ya doki yaro ba, sai idan akwai maslaha da tsammani mai karfi na cimma wannan maslahar, kuma ya zama dukan ba ya tayar da fata, ko ya sanya wata alama a kanta, balle kuma ya kai ga fitar da jini, duka ne wanda ba ya lahanta naman jikinsa, ko kashinsa, ko canja masa launin fata.

Sannan bai kamata ba a ajiye wani abin duka domin yaro ya rika gani yana tsorata, wannan ba ya kara masa komai sai kashe masa kuzari, da azama, da kai shi ga sukewa daga rayuwar cikin gida. Don haka bai kamata ba a ajiye bulala domin duka sai dai don tsoratarwa ga laifin da aka san haka zai yi tasiri wajan tarbiyyarsa.

Sau da yawa wasu mutane sukan ajiye abin duka kusa da yaro a kan laifin da bai kai ga haka ba, ko kuma ya kasance ba shi ne mafita ba, kamar wasu da sukan ajiye bulala don yaro ya ci abinci, yaron da ba ya cin abinci yana bukatar likita ne ba duka ko ajiye bulala ba, domin ta yiwu da bitamin “C” cokali uku a rana matsalarsa ta warware.

Amma wasu iyayen sun dauka komai duka ne maganinsa, sai su yi ta dukan yaro ko daka masa tsawa, alhalin da yawa wasu abubuwan malami, ko likita, ko makoci, ko abokai, zasu iya warware su ga yaro ba iyaye ba. Wani abin ma laifin iyaye ne amma sai su doki yaro: kamar yaro ya ga suna wani abu shi ma sai ya yi, kamar wani da yake shan taba amma da ya ga yaronsa yana sha a boye sai ya zane shi.

Kausasawa da tsanantawa a kodayaushe ba sa magani ga yaro, sabanin tausasawa da nuna kauna da mayar da shi abokin hira, da cin abinci, da zama tare, da tafiya yawo ko unguwa tare da shi. Bisa tarbiyyar da muka samu wajan iyayenmu, da abin da muka samu na tajribar da wasu suka bayar da labari game da rayuwarsu, wannan ya fi tasiri.

Yawancin wadanda aka horar ta hanyar kausasawa da takurawa ana bata su ne su taso mutane masu kekashewar zuciya, da bushewar zuciya, da rashin tausayi, da rashin kunya, har ma sukan iya jin ba a kaunarsu ne don haka sai su kama hanyar iskanci da rashin kunya, ko su yi tunanin daukar fansa kan wanda ya azabtar da su, a wani lokaci ko da kuwa kan iyayensu ne.

Ka taba jin labarin wani dalibi da a furamare da malaminsu ya gallaza masu, bayan ya gama jami’a sai ya zama shi ne mai kula da fayel din Furamare Board a jahar tasu, wata rana yana binciken fayaloli sai ya ga malaman makarantarsu ta furamare, da ya duba sai ya ga sunan malamin wanda a wannan lokaci har ya manta da malamin amma ganin fayel din sai ya tuna masa shi. Saboda haka sai ya batar da fayel din, a lokacin da aka zo Pepa red sai ya zama shi malamin ba a ga na shi fayel ba, a sakamakon haka ya rasa nasa albashi da aiki, ya zama sai dai ya je wajan abokansa in an dauki albashi don su taimaka masa da wani abu na cefane.

Wasu malamai masu tsangwamar yara sukan samu kyama daga dalibai musamman wanda ya zama mai bulala, an ce lokacin da turawan yamma suka zo kasashenmu a makaranta sai a ba wa malamin ilimin Addini ya zama shi ne mai duka sai duk dalibai ka ga suna kin malamin da ma darasin nasa, shi kuma yana daure fuska da barazana ga dalibai wai shi ne mai bulala. Da haka ne sai yara su nisanci darasinsa, su gan shi a matsayin wani ci baya ne, kuma su ga cewa ba abin da ma’abotansa suka sani sai su yi bulala ga dalibai.



1 2 3 4 next