Babar Babanta!



Haka nan aka gaggauta mata fitunu da jarabawowi a rayuwa a shekaru na budurci har zuciyar ta ta tsage saboda rashin uwa!! Bak'in ciki ya girgiza ta tana k'arama mai rauni, ta kusa ta fad'i k'asa ba don juyawa da Baban (s.a.w) ya yi zuwa gare ta ba da gaggawa yana mai shafe mata hawaye kamar yadda take shafe masa, ta kafu a kan hak'uri da juriya!!.

Tana mai d'imuwa cikin lamarinta, ba ta san mai zata yi ba; shin zata yi juriya ne da bala’in da ya same ta na rashin uwar da babu wata uwa kamarta ko kuma zata yi wa Babanta da babu uba kamarsa ta’ziyyar rashin matarsa da babu wata mata kamarta ne!.

Nan da nan sai ta zabi ta kasance mai ta’aziyya da lallashi ga uban domin bazatar da aka yi masa na amminsa da matarsa, tana mai yak'ini cewa ba ya rasa mata maras misali ne kawai ba, har ma ya rasa mai kariya ne mai d'auk-ba-dad'i da gwagwamarya domin kare hadafinsa kamar yadda amminsa Abu Talib (a.s) yake d'aya rukunin mai kare shi mai kuma lallashi da tausayi mai juriya, kuma ga shi ya rasa masu ba shi kalmomi masu dad'i da ra’ayi mai dacewa.

Sai Fad'ima ta yunk'ura ta motsa a wannan karon ba domin ta tambayi Babanta ba sai domin ta lallashe shi ta k'ara masa k'arfin gwiwa ta kawar da bak'in cikinsa tana mai shafe masa hawayi daga kumatunsa masu albarka (s.a.w) tana nuna masa k'auna irin wacce uwa kan nuna wa d'anta da kuma son nan da ya rasa daga Khadiza, domin haka ne ta zama Babar banta kuma ‘yarsa a lokaci guda[3].

Haka nan ta zama uwa ga uban (a.s) a kiyayewa da k'auna kuma ‘ya a nasaba da tarbiyyatarwa da koyi amma uwa a kula da kiyayewa.

Haka nan ta fara wata marhala ta rayuwa sabuwa ta fara sabon shafi na rayuwa da Babanta ko zata iya zama kamar khadija ga Babanta (s.a.w) kamar yadda Ali (a.s) ya zama kamar amminsa (s.a.w) Abu Talib (a.s) gareshi.

Haka nan Fad'ima ta sha wahala tana mai cire k'ayoyi daga digadigan Babanta tana mai shafe masa jini daga k'afafunsa tana mai wanke hannyansa da shafe masa k'asa daga fuskarsa tana mai kawar da bak'in cikin nan na ‘ya’yan hanji da kayan ciki daga bayansa da k'irjinsa, har shekarar ta ta tara ta wuce.

Babanta ya kasance k'arkashin zaluncin masu mak'wabtaka da shi har ta wayi gari tana mai nemansa wata rana sai ta yi kicibis da k'azanta a kansa da k'asa da k'ayoyi, saboda haka ta gaggauta tana mai kawar da wannan da hannayenta masu ni’ima tana mai kuka saboda abin da ya sami Babanta na daga cutarwar K'uraishawa da gabarsu da kuma cutarwar mak'ota da makusantansa daga Bani Abdi Manafi, sai wannan ya sanyaya masa zuciya, fushinsa ya kau, zuciyarsa ta kwanta hankalin ‘yarsa ya faranta, tana mai kuka daga halin da ta gan shi a ciki, shi kuma yana mai ce mata: “Kada ki yi kuka ya ‘yata Allah zai kare Babanki”.

Kafirai ba su k'yale Fad'ima (a.s) ba kamar yadda ba su k'yale Babanta ba kamar yadda wani mafi wautarsu Abu Jahal (L) ta ji shi yana zagin Babanta (s.a.w) saboda haka ne ma ta kasa mallakar kanta ta yi raddi ga shi Abu Jahal (L) da kalmomi masu hikima da ke cike da fasahar nan ta Bani Hashim amma saboda Abu Jahal ba shi da kunya da mutunci bai san shi ba har abada, sai ya daga hannunsa ya mare ta a fuskarta yana mai ci gaba da zagi da cin mutunci ga Manzo (s.a.w), Fad'ima (a.s) ta tafi tana mai bak'in ciki da kuka sakamakon abin da yake yi wa Babanta, har ta wuce wuri da Abu Sufyan yana mai jin kukanta da ganin hawaye na zuba a kumatunta (a.s) yana mai tambayar ta me ya same ki ya ‘yar Muhammad!

Haka nan wata rana Fad'ima (a.s) ta wuce wasu mutane daga manyan K'uraishawa suna shawara kan al’amarin Muhammad (s.a.w) sai ta ji wasu suna cewa: Wallahi ba ma ganin Muhammad (s.a.w) zai daina abin da yake yi, idan mu ka k'yale to lallai zai shuna mana bayinmu a kanmu da ma’aikatanmu, kuma zai canza matanmu da ‘ya’yanmu ta yadda babu wata dubara da zata rage garemu, me kuke gani?.



back 1 2 3 next