Raddin Suka



 

A yau na bude wannan shafin "nana_fatima" sai na ga wannan abin mamaki na hujumi kan masoya Ahlul Baiti (a.s) sai na ga ya kamata in tofa albarkacin bakina; musamman duba zuwa ga cewa; wasu miyagun akidu sun shigo da suke nuni da raini ga Ahlul Baiti (a.s) da matsayinsu. Mai magana ya yi wa rubutunsa taken: ((HATTARA DAI MUSULMI 2!!)) sannan sai ya ci gaba da cewa: ((A rubutu na da ya gabata ya tada hankalin da yawa daga mabiya Addinin Shi'a na wannan majalisa kai harma da yan'uwa Musulmi wayanda basu gama gano sharrin Addinin Shi'a ba har suke daukarsa wani bangare ne daga Addinin Musulunci kamar yadda yahudawa da kiristoci suke rayawa cewa su addinaine haka shian'ci yake a matsayin addini mai zaman kansa)).

Don haka nake cewa da shi: Babu wani wanda hankalinsa ya tashi sai kai da ka ga amsa gamsasshiya kan abin da kake kira sunnanci bisa karya, domin sunnaci yana girmama Ahlul Baiti (a.s) amma sai muka ga naka sunnacin yana kyamar tafarkinsu. Da haka ne sai muka gane irin naka sunnacin yana goyon bayan Banu Umayya ne makiya aali Muhammad (s.a.w).

Sannan rashin basira ya sanya ka ganin Shi'a suna ganin kansu a matsayin wani addini mai zaman kansa alhalin Shi'a su ne hakikanin musulmi masu biyayya ga manzon Allah da dukkan abin da ya zo da shi, wannan ne ma ya sanya su duk wani abu da wani ya haramta indai ba manzon Allah (s.a.w) ba ne to a wurinsu batacce ne domin shi ne Allah ya aiko. Idan ka isa ka kawo hukuncin manzon Allah guda daya da Shi'a suka canja!

Sannan ba mu yarda da mugaladar da kake yi ba ta wakiltar sunnanci wallahi babu wani wakiltar sunnaci da kake yi domin Sunna suna son gidan Annabi (s.a.w) kuma suna girmama Shi'a mabiyansu. Amma idan kana nufin Sunna (la'antar Imam Ali (a.s)) da ake kira Sunna da kuma jama'a (wato ittifakinsu kan kin jagorancin alayen Muhammad (s.a.w) da yardarsu da jagorancin Banu Umayya wanda Hajjaj yake cewa shekarar arba'in ita ce shekarar Sunna) to na yarda kai mai kare Sunna ne, domin asalin "Sunna da jama'a" ke nan. Kuma da wannan ne sauran ahlussunna ba su yarda cewa su Ahlussunna walja'ama ba ne, har ma ya kasance kalma ce da ake gaya wa 'yan hadisi a akida masu tunanin hashawiyya kan Allah.

Amma rashin gano sharrin Shi'anci daga sauran musulmi wannan yana nuna kyakkyawar niyyarsu ga son Ahlul Baiti (a.s) da tafarkinsu ne sabaninka da ire-irenka, amma kuma daukar addini mai zaman kansa wannan ka yi wa Shi'a kage ne, sai ka nemi afuwarsu ko ka koma da nauyin zunubin haka ranar kiyama randa babu wani wanda zai maka afuwa sai abin da ka girba.

Amma da yake cewa: ((Wannan ra'ayi nawa zan kareshi a yau da tarin dalilai da zan kawosu a kasa kuma insha Allahu har mai ruduwa zai gane cewa Shi'a addini ne wanda yayi hannun riga da Addinin Allah na Musulunci, nayi alkawarin a wannan rubutun nawa bazan kawo wata hujja ba ko guda daya daga litattafan Musulunci, zan shiga littattafan addinin Shi'a ne na kawo hujjojina, inaso ku bini cikin nutsuwa. Dalilan da suka nuna Shi'a addini ne mai zaman kansa ba kungiya bace daga kungiyoyin Musulunci)). Sannan sai ya ba shi take kamar haka: 

((1) Sabaninsu da Musulmi Akan Allah (SWT): yana mai yin bayani kamar haka: ((Ni'imatullahi Jaza'iri Azzindiki yace acikin littafinsa Anwarul Nu'umaniyyah Mujalladi na biyu shafi na 278 "Babu hada da "Musulmi ba" akan Allah ko akan Annabi ko akan Imami saboda su "Musulmi" suna cewa Allansu shi ne ya aiko Muhammadu da Annabta kuma Abubakar ya zama halifan Annabin, mu kuwa "Yan Shi'a" mun san wannan ba Ubangijinmu bane kuma Annabin nasu ba Annabinmu bane, mu muna cewa du ubangijin da Halifan Annabinsa ya zama Abubakar to Ubangiji ba Ubangijinmu bane kuma Annabinmu ba Annabinmu bane". To ai Magana ta kare domin ga daya daga cikin masadir na Addinin Shi'a ya fayyace komai to ni Adamu meye laiifin da nayi dan na fadi abin da na gani a rubuce ko bani da hakkin fadar ra'ayi na, ayi mini adalci mana)).

Sai in ce masa: Ka kawo magana da a irinta ne Imam Ali (a.s) yake gaya wa Hawarijawa cewa "Kalmar gaskiya da ake nufin barna da ita" yayin da suke cewa "Babu hukunci sai ga Allah", domin ka kawo magana amma ba ka kawo fuskar maganar ba: domin wannan ya yi kama da ka ce  ne "Ubangijin da Annabi Isa (a.s) dansa ne to wannan ba ubangijinmu ba ne" kamar yadda Imam Ridha (a.s) yake gaya wa wani kirista cewa: "Isanku" a maganar da yake yi da shi a wata munakasha, wato ba Isanmu (a.s) ba. Ka sani haka wannan magana take: Mu ba yi imani da ubangiji ko annabin da ba shi da hadafi ba, ta yadda zai tafi ya bar al'umma bai nuna musu wanda zasu yi riko da shi ba, har ya sanya kashe-kashe tsakaninsu kuma daga baya suka yi rigima a Sakifa aka kuma wulakanta 'ya'yan annbinsa duk saboda wannan lamarin, sannan kuma masu karbar jagorancin al'umma suka nuna ba su san ma makomar al'umma ba da nadamar abin da suka yi na jagoranci da cewa kuskure ne kuma sharri ne da Allah ya kare musulmi sharrinsa, sannan daga karshe kuma ta sabbaba nisantar Kur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w) da aalyanesa.

Mu mun yi imani da Allah (s.w.t) da Annabi (s.a.w) masu hadafi ne wadanda suka komar da mutane zuwa ga littafin Allah da aalayen Annabi Muhammad (s.a.w) kuma suka shiryar da al'umma ta yadda babu wani abu sai da suka yi bayaninsa a addini, suka shelanta musu Ali (a.s) a matsayin mai maye gurbin Annabi (s.a.w).

Amma da kake cewa:  ((2) Waye Allah a Addinin Shi'a



1 2 3 next