Tattaunawa Ta Shida



Ina ganin dakatar da wannan tattaunawa domin: Kana ganin hadisi zai iya inganta sannan sai kuma ya sabawa kur’nai mai girma, wannan abu ne mai ban mamaki daga gareka, ba ka san mutlak da mukayyad da amm da khas da sauransu na Kur’ani ba, amma kai tsaye kana ta kawo ayoyi kana fitar da hukunci, kada ka manta na sha nuna maka wannan inda ka kawo ayoyi ba a mahallinsu ba, sannan kuma mafi mamaki kana ganin hadisi ya inganta amma sai a rushe shi da ayoyin Kur’ani, alhalin babu karo tsakaninsu, sai dai kai ne saboda sanin wasu â€کyan kalmomi na larabci sai ka yi tsammanin sun yi karo da juna. Wannan kuwa al’amari ne mai hatsari da ya sami duniyar musulmi, kuma abin takaici da â€کyan ustazai suka dauka suka dora wa kansu a kasashenmu, sannan kuma wai haka ne addini yake, na gaya maka Annabi (s.a.w) ya fassara wannan addini da ya kawo, bai bar mu da ra’ayoyinmu ba, kuma wanda ya fassara da ra’ayinsa to ya tanadi wajen zamansa a wuta kamar yadda ruwayoyi suka zo da shi.

Sannan kuma muna bahasi kan wasu mas’aloli daban amma kai kuma kai tsaye kana kawo wasu daban, misali ka kawo maganar sahabbai a wannan fayaloli uku na karshe da ka aiko, alhalin bahasin namu ba akan sahabbai yake ba. Bahasinmu ya riga ya tabbatar mana da cewa; Shi'a suna kan gaskiya bisa abin da suke bi ga wasiyyar Annabi (s.a.w) ta halifofinsa sha biyu, kuma wannan wani abu ne da akan shi wasu masu kiyayya da wannan biyayya suke gaba da su, da yi musu sharri iri-iri, saboda kawai sun gabatar da wanda Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) suka gabatar da jinkirtar da wanda suka jinkirtar, ba su yarda da bin son rai ba da ake neman kiransu a kai har abada. Kuma akan haka ne suka sha wahala a tarihin rayuwar Ahlul Bait (a.s) da mabiyansu.

Ka yi mana kagen zagi ko la’ana ko sukan sahabbai kamar dai yadda kuka saba yi wa mabiya Ahlul Bait (a.s), wannan kage ko sharri ko kazafi kamar yadda bahaushe yake kiransa, an dade ana yi wa mabiya Ahlul Baiti (a.s) shi, sai dai kai a matsayinka na dan’uwana a musulunci ni mai yafe maka ne. Da fatan zaka daina yi wa mabiya Ahlul Bait (a.s) irin wadannan kage-kage. Idan ka san cewa; ba zaka iya yarda da dalili ba, to babu amfanin wannan muhawarori.

Hada ni da wasu mutane daban kamar Parisawa da kiran su mayaudara, alhalin bahasinmu ba shi da alaka da Parisawa, ba ni da wata alaka da su sai wacce kake da ita ta cewa; â€کyan’uwanka ne musulmi, kuma su ma wasu shekaru da suka gabata ba da dadewa ba, su ma ahlussunna ne kamarka (sai dai su ba wahabiyawa ba ne) suka fahimci mazhabar Ahlul Bait (a.s), idan kana jin haushinsu kan haka sai ka fara sukar larabawa da suka kawo musu wannan koyarwar ta Annabi (s.a.w), sannan kuma sai ka fara da Imam Ali (a.s) da sahabban Annabi mabiyansa da suka kawo wa larabawa wannan koyarwa, ka ga ke nan sai ka fara sukan daga tushe, kai kana ma iya kaiwa ga wanda ya kawo wajabcin biyayya ga Ahlul Baiti (a.s) da Ubangijin da ya aiko shi, wal’iyazu bil-Lah.Wannan kuwa ba ina yi maka fatan ka kasance haka sai dai nuna maka cewa; jin haushin biyayya ga Ahlul Bait (a.s) zai koma wa abin da na kawo maka ne. Domin wanda ya kawo wannan addinin ba bahaushe ba ne, kuma su ma Imam Ali (a.s) da sahabban da suka bi shi kan wasiyyar Annabi (s.a.w) ba hausawa ba ne, kuma addinin nan na musulunci ba bahaushe ba ne, kuma kabilanci a wannan addini haramun ne. Kuma ina godewa Allah da na san addini na fahimci Ahlul Bait (a.s) da wajabcin riko da tafarkinsu tun kafin ganin wani bafarise a idanuwana, balle ka kawo mini irin wannan tsammani. Sai dai ka sani shiriya idan ta zo ko tahannun waye kodakuwa bafarise ne da kake zagi, to sai a karbe ta, domin koyarwar addini ta umarce mu da neman ilimi koda kuwa a kasar Sin ne.

Zubo ayoyin Kur’ani ba tare da yi wa Littafin Allah (S.W.T) adalcin fassara shi ba, domin yana da ayoyi mutlakat kamar yadda kake kawo su babu tadabburi kana mai fassara su kamar yadda ka gina akidarka da mazhabarka a kai, kana kuma tsayawa a matsayin Allah a fahimtarka, ta yadda kake kiran fahimtarka a matsayin abin da Allah yake nufi, ra’ayin wani da fahimtarsa kuma shi ne abin da ya sabawa Allah da manzonsa. Me zai hana ka ka tambayi masana marasa bin son zuciya, koda kuwa ya sabawa mazhabarsu, me ya sa ba zaka komawa mukayyadat ba, kamar “faman nakasa fa’innama yankus ala nafsihiâ€‌ da gomomin irin wadannan mukayyadat da Allah ya saukar a littafinsa mai girma.

Sannan kuma wanda ya ce: hadisin wane ba daidai ba ne, shi kuma a wa? Yaushe ne wata ruwaya ta zo tana cewa; idan wane ya ce hadisi kaza ba ingantacce ba ne ta zauna, kai ba ka sani cewa kowa yana da mazhaba ba a wannan kwamacalar da ake ta tafkawa ana jingina ta ga addini. A ina ka samu wata ruwaya ta cewa abi malaminka wajen tace hadisai, wani abin mamaki kana magana kana warwara, ka ce: hadisai Allah ya kare su, kana kuma cewa; akwai masu tacewa; kuma ka kira tacewar da kariyar Allah, wato; ke nan Allah ne ya ce; wane zai zo ya tace sai ku bi shi, wal’iyazu bil-Lah idan dai haka addini yake a hannun ma’abotansa. Ka sani babu wani wanda Allah ya wajabta binsa sai manzon Allah (s.a.w) da halifofinsa goma sha biyu. Sai ka koma wa addininka ka bincika.

Kafin ka zargi malaman Shi'a da zagin sahabbai sai ka fara da Buhari da ya ce: wadanda zasu shiga cikin aljanna daga cikinsu kamar wani garken rakuma ne marasa makiyaye. Buhari: fatahul bari; j11, shafi 333. ya ce: Manzon rahama a wannar ranar lahira zai ce a yi nesa da su, kuma ya kawo dalilin hakan da cewa; tun da Manzo ya yi wafati suka yi ridda! Kuma aka gaya wa Annabi cewa; ba ka san abin da suka yi a bayanka ba. Sannan kana iya sukan Maliku da yake fada a muwatta: manzon rahama ya ki nema wa Abubakar gafara, duk da kuwa ya gaya masa muma munsulunta kamar yadda wadannan shahidai suka musulunta, kuma mun yi yaki kamarsu. Amma duk da hakan manzon rahama ya ce masa: Ban san abin da zaku yi bayana baâ€‌.

Kai kana iya fara sukan ma sahabban kansu, domin uwar muminai Allah ya kara mata yarda ta ce wa usman “ku kashe Na’asal hakika ya kafirtaâ€‌ tarihin Dabari: j 3, shafi: 477. Kuma ibn Mas'ud yana cewa: “katalani ibn zami’atal kafir, bi amri usmanil kafirâ€‌, sharhi nahajul balaga, j 3, shafi: 44. Ko kuma mugira da yake cewa; game da Mu'awiya; “ji’itukm min indi akfarin nasiâ€‌ kamar yadda ya zo a murujuzZahab na mas’udi, kuma ya fadi haka lokacin da Mu'awiya ya so cire ash’hadu anna muhammadar rasulul-Lah daga kiran salla yana mai sukan Annabi (s.a.w) kan ya sanya wannan a kiran salla, don sunansa ya wanzu!

Don haka kafin ka zagi malaman Shi'a kana sukansu da zagin sahabbai, sai ka fara da sahabban kansu ke nan da suka zagi sahabbai, ko ma neman kawar da sunan Annabi (s.a.w) da mugira ya fada game da Mu'awiya. Idan kuwa ba ka yi haka ba, to dole ka sani ba ka yi adalci a cikin mazhabinka ba, da kake ganin laifin wasu kana boye naka, idan kuwa ba ka sani ba ne, to wannan musiba ce gareka cewa; ba ka san mazhabinka ba. Idan kuwa ka sani amma kana ganin kuskure ne sahabbai suka yi sai dai ka boye, to ka daina sukan wasu akan wannan, kuma su ma sai ka ba su uzurin cewa; kuskure ne suka yi kamar yadda kake ganin sahabbai sun yi ka ba su uzuri. Domin babu adalci kuskuren da ka yarda da shi ka ba shi uzuri ya kasance daidai, amma na wasu ba daidai ba ne!

Duk wani dalili duk karfinsa a wajenka matukar yana karfafar biyayya ko falala ga Ahlul Bait (a.s) ba dalili ba ne a wajenka, ka ga ke nan a irin wannan babu amfanin wata muhawara a kai. Domin indai haka ne fagen addini da ilimi zai koma, to ba shi da bambanci da magana a bakin titi, da kowa ya ga dama sai ya fadi abin da ya so.



1 2 next