Tattaunawa Ta Uku



Sai in ce maka: A ina ka samo cewa Manzo (s.a.w) da fitar da Ummu salama yana nufin wadanda aka haramta wa sadaka ne. Muslim da Nisa’ai da Ahmad Bn Hambal da Bazzaz da Tirmizi da Tafsirai duka suna cewa Manzo (s.a.w) Ya lullube su da bargo ya ce: “Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin Gidana. Sannan ya fitar da matarsa, kuma ita Ummu Salama da A’isha duka sun fadi cewa ba sa ciki, Zaid bn Arkam da sauran sahabbai sun yarda ba sa ciki, kai kuma a ina ka samo cewa suna ciki.

Abin da na gaya maka ke nan na hadarin da al’umma ta fada na duba ma’anar lugga su fassara Kur’ani ba tare da duba yaya Manzo (s.a.w) ya fassara ba! Abin takaici sai ka ce al’ummar ta fi manzon Allah (s.a.w) sanin abin da aka saukar masa! Ka sani dalilin haramcin sadaka ya zo ne daban a wasu ruwayoyin, ba da wannan ne aka fitar da wannan hukunci ba. Ruwayoyi sun zo daban suna nuna haramncin sadakar ga Alayen Abdulmutallib.

Game da jimlarka ta karshe na riga na maimaita cewa Annabi ne (s.a.w) yake hujja a kanmu gaba daya, kuma bai sanya wadannan: ("aali Aliyu (dukkansu), aali Akilu, aali Jaafar, aali Abbas") cikin Ahlul Bait ba (a.s). Ya riga ya sanya mutane goma sha Uku ne a ciki da ya hada da 'yarsa da halifofinsa goma sha biyu daga alayensa na farkonsu Ali (a.s) na karshensu Mahadi (a.s). Ahlul Baiti (a.s) kalma ce da Kur’ani ya yi amfani da ita kuma ya nuna su wa yake nufi, kuma Manzo (s.a.w) ne ya fassara ya yi bayani, kuma an ce mu bi shi ne a kan hakan, sako daga Allah.

Amma abin da mai musu yake neman ji na dalilin halifancin sayyidina Ali (a.s) wadannan suna da yawa domin akwai: Hadisuddar da muka kawo a baya da manzon Allah ya yi amfani da kalmar halifana, wasiyyina, akwai hadisin manzila cewa tsakaninsa da shi kamar tsakanin Haruna ne da Musa (a.s) in ka cire annabta.

Amma batun batun cewa sayyidi Ali (a.s) ya yi maganar cewa duk wanda ya wuce su ya halaka, ya tabe. Ya kai mai musu kana iya duba hadisai kamar haka: Durrul mansur na Suyudi: j 2, shafi 60. Kanzul ummal j 1, shafi 143. usudul gaba j 3, shafi 137.  Sahawi a cikin istijlabi irtika’il guraf takarda ta 24. Tabarani a mu’ujamul kabir daga Zaid dan Arkam. Ibn Hajar a cikin sawa’ikul muhrika, shafi 89. Hudubar Imam Ali (a.s) a nahajul balaga, ta 97, shafi 189.

Amma batun hadisin cewa Ahlul Baiti sune jirgin ruwan da duk wanda ya shige shi ya tsira, wanda bai haushi ba ya tabe, shi ma kana iya duba: Talkhisul Mustadrak na zahabi. Yanabi’ul mawadda na kanduzi shafi 184. sawa’ikul muhrika shafi 184. tarihil khulafa na Suyudi. Jawahirul Buhari j 1, shafi 361. alfada’il na Ahmad bn Hambal shafi 28. kai suna da dama, akwai tabarani, da kifayatut dalib na genji shafi’I, da majma’azzawa’id. Da sauransu.

Sannan batun rashin yiwuwar sabani tsakanin Ahlul Baiti basu al'amari ne da haka yake ko tantama kuma idan ka samo daya ka kawo shi mu gani, sannan kuma babu alaka tsakanin rashin sabaninsu da cewa wahayi ake yi musu kamar yadda kake kokarin alakantawa domin su ba wahayi ake yi musu ba, sai dai sanarwa ce daga Annabi (s.a.w) da suke gada kakanni zuwa uwaye zuwa 'ya'ya har zuwa na karshensu. Sannan kuma maganar da ka fada da fassarar da ka yi wa ayar nan "walaukana min inda gairil-Lahi…." tana komawa ga abin da muka ce a baya. Sannan kuma ina ganin ba mahallinta ba ne, domin Sunna ba ita ce Kur’ani ba.

Kada ka yi kuskuren da mafi yawa wadanda ba Shi'a ba suke yi na rashin fahimtar imaman Shi'a (a.s). Imam Shi'a su ne dai wadannan halifofi 12 wadanda sunnarsu ita ce hujja a kan duk wani taliki a bayan kasa. Amma sauran malaman Shi'a masu daraja kuma jagororinsu kamar sayyid Abulkasim Khu’i (Allah ya tsarkake ruhinsa) ko kuma rayayyu kamar sayyid Sistani (Allah ya tsawaita mana rayuwarsa) su mujtahidai ne da suke duba abin da ya zo daga sunnar manzon Allah da halifofinsa domin su fitar da hukuncin shari’a.

Ahlul bait (a.s) su ne Kur’ani mai magana: don haka ne ma su ne Manzo (s.a.w) ya gadarwa iliminsa tun daga Ali (a.s) birnin iliminsa shi kuma ya ba wa na bayansa har zuwa kan na karshe. Don haka duk abin da suka ruwaito yana komawa ga Annabi ne, kuma sun karfafa cewa duk abin da suka fada yana tukewa ne zuwa ga Manzo (s.a.w).

Amma tambayarka cewa don me a tarihi masu mulki ba sa son Ahlul Baiti?. Wannan lamari ne wanda yake a fili bayan sanin cewa mulki nasu ne. An tambayi Shafi’i game da Imam Ali (a.s) sai ya ce: me zan fada game da mutumin da masoyansa suka boye darajojinsa saboda takiyya (tsoro) kuma makiyansa suka boye saboda gaba, amma duka da haka (falalarsa da darajarsa) ta cika sasannin duniya biyu (gabas da yamma).



back 1 2 3 next