Tattaunawa Ta Biyu



Na bakwai: Idan muka yi kokwanto kan tana nufin masoyi ko shugaba, to sai mu yi hukunci da duka ne da ya hada da wajabcin sonsa da kuma mika jagoranci gareshi; domin ka’idan nan ta ilimin Usul ta komawa ga ma’ana gamammiyya “ammaâ€‌ idan an rasa komawa ga kebantacciyar ma’ana “khasâ€‌. Don haka wannan ya tabbatar da ma’anar shugabancinsa da jagorancinsa kan duk wani mutum bayan Manzo (s.a.w), domin umarnin Allah bai kebanta da musulmi ba.

Na takwas: Akwai ayoyin Kur’ani da hadisai masu yawa da suke karfafar ma’anar jagora. Kamar ayar “kawai shugabanku … da muka kawo a bayanin da ya gabata wanda a karara take nufin jagora saboda karinar ayar da ta gabace ta, da wacce ta biyo baya da kuma tafsiran masu tafsirai.

Na tara: Daga hannunsa da Manzo (s.a.w) ya yi a wannan wuri da kuma nuna shi ga al’ummarsa.

Ya kai  mai jayayya da akwai abubuwa masu yawa da lokaci ba zai ishe mu kawo su ba, amma Sheikh dan fodio yana cewa: Masu hikima sun ce: Nuni ya isar wa yin magana ga mai hankali. "ط§ظ„ط¥ط´ط§ط±ط© طھط؛ظ†ظ‰ ط¹ظ† ط§ظ„ظ…ظ‚ط§ظ„ط© ظ„ظ„ط¹ط§ظ‚ظ„"

Na goma: saukar azaba kan Nu’uman yayin da ya ki yarda da shugabancin Ali (a.s) nan take, da musun da ya yi wa Annabi (s.a.w) da cewa yaya zai ce su bi dan amminsa bayansa (s.a.w), da saukar azaba kansa wanda yake nuna dalilin saukar da ayoyin farko na surar Ma’arij. Ka duba tafsirin Durrul Mansur, da asbabun nuzul na Suyudi, da littattafai kamar Nurul absar na shiblanji basha’fi’e.

Na sha daya: Ya tabbata a ilimi mantik da palsapa cewa; Ma’ana gamammiya “ammâ€‌ fuska ce ta “khasâ€‌, don haka wilaya a nan tana nufin ma’anar jagoranci, musamman da yake khas ana kawo shakku kansa, domin ka sani har abada ba yadda za a yi khas ya kasance fuskar amm.

Ka sani wannan kalma ta wilaya kalma ce da tana daga cikin kalmomin da aka yi wa tawili kamar yadda aka yi tawili ga watanta da wasu umarnin Annabi don son rai ko kuma saboda rashin yarda da wannan abin. Wasu sukan yi kokarin tawilin wasu abubuwa ne domin gyara barnar da aka yi wa addini wanda wannan cin amanar Allah da manzonsa ne.

Kuma wannan ba sabon abu ba ne, domin ba kawai tawili domin rashin yarda ba, hatta da zamanin Annabi (s.a.w) da yawa ya bayar da umarni amma ba a bi umarninsa ba.

Ya kai mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s), Amma maganar da ka yi ta cewa sauran mazhabobi zasu dawwama a wuta ba haka na ce ba, abin da na ce shi ne: Tunda ka kawo bahasin kasuwar al’umma gida saba’in da uku, don haka ne na tabbatar maka cewa Ahlul Bait (a.s) su ne suke kan tafarkin jama’a mai tsira; wato wannan guda daya. Kuma na kawo dalilai a kan hakan.

Amma batun Annabi (s.a.w) ya rayu akan tafarki da shi da mabiyansa ba bisa mazhaba ba; ai ba komai muka tabbatar maka ba da wannan maganganun bayan da muka kawo game da kasuwar jama’a 73 sai wannan, wato: cewa wannan jama’ar da take kan abin da Annabi (s.a.w) ya bari su ne mabiya Ahlul Bait (a.s). Ai wasiyyar da Annabi (s.a.w) ya yi ta bin Littafin Allah (S.W.T) da Ahlul Bait (a.s) yana nuni da hakan. Kuma bin su shi ne dawwama kan tafarkin Annabi yardajje gun Allah (S.W.T).

Ka sani Annabi (s.a.w) shi ne shugaban masu hikima da hankali, sannan kuma ya san babu wani Annabi bayansa, kuma babu wani wahayi bayan nasa, don haka ya dauki matakai da zasu hana bacewar al’umma da karkacewarta. Idan kuwa ka ga al’umma ta ki to wannan ita tajiyo wa kanta. Don haka wahalhalun da kake gani da rarraba duk ya faru ne tun farko saboda barin wasiyyoyinsa. Kuma abin da ya faru ga yahudawa da Kirista shi ne ainihin abin da ya faru ga musulmi kwabo da kwabo, sai dai mu musulmi muna da ludufin Allah (S.W.T) na cewar muna iya bugun kirji mu ce: Duk wanda yake son ya ga sakon manzon Allah (s.a.w) ba tare da wani jurwaye ba to ga shi nan a tare da Ahlin gidansa (a.s).

Ya kai mai musu; Ka sani Maliku a Muwatta’ da Baihaki su ne kawai suka ce Littafi da Sunna aka bari, amma sauran ingantattun littattafai gaba daya sun ce an bar Littafin Allah ne da Ahlin gidan Annabi da aka fi sani da Alayensa. (Kuma wannan ba matsala ba ce, saboda ruwayoyin ba suna kore juna ba ne, suna fassara juna ne: wato; Littafin Allah da Sunnarsa da ta zo ta hannun Ahlul Bait (a.s)) Ba Litttafin Allah da ingantattun hadisai ba kamar yadda ka ce. Hada da cewa Littafin Allah da Sunnata yana da rauni sai ka koma ka duba. Ka sani sanin ingantattun littattafai zai yi maka wahala musamman da yake an kona hadisan manzon Allah (s.a.w) da sahabbai suka rubuta bayan wafatinsa, aka tattara su aka banka musu wuta, kuma aka kira su da cewa tatsuniyoyi ne irin tatsuniyoyin Ahlul Kitab! wayyo Allah!!

Kuma aka hana rubuta duk wani abu da aka ji daga Annabi (s.a.w) (ibn Kutaiba ya so ya kare wannan mummunan abu da ya faru a tarihi da tawiloli amma ya kasa!) sannan aka hana sahabbai yaduwa garuruwa domin kada hadisan su yadu. Idan an bar hadisai ne ingattattu, kai ya zaka san ingantacce bayan an fara hada su ne da wafatin manzon da wucewar (kusan) karni guda!, alhalin a lokacin siyasa ta shiga kowane loko. Duba ka gani a misali: Maliku bai yarda da Usman da Ali ba, kuma ya rubuta Muwatta. Buhari bai yarda da Imam Sadik ba, kuma ya rubuta Sahih Buhari. Banu Umayya suna la’antar Imam Ali har shekara 80 kuma an hana rawaito hadisansa. To kai irin wannan yanayi yaya kake tsammanin ka samu sahihi kamar yadda yake lokacin Manzo (s.a.w). hada da cewa Muslim ya tabbatar da cewa suna ruwaito ma’ana ne ba lafazin Annabi (s.a.w) ba! (Ka san kuwa cewa; da lafazin Annabi (s.a.w) ne da ta yiwu masu tunani su fahimci wani abu da shi mai ruwayar ba haka ya fahimta ba!!!) to ka sanin nan ne sirrin barin Ahlul Bait (a.s) zai bayyana gareka, kuma munin nisantar su yake futowa a fili.

Amma batun abin da Allah ya saukar, to yana cikin sakon Annabi ne gaba daya. Domin duk abin da ya fada Allah ya zartar da shi da cewa duk abin da ya zo da shi to mu karba Kamar yadda Kur’ani ya tabbatar da hakan.

Hafiz Muhammad

Kammala gyarawa

01 /July/ 2009

 



back 1 2