Tattaunawa Ta Biyu



Zan fara da maganar da kai mai musun wilayar jagoranci da tafarkin Ahlul Baiti (a.s) ka yi ta Gadir Khum a inda Annabi (SAW) yake cewa "man kuntu mawlahu, fa Aliyu maulahu". Kana mai cewa; Ai wannan bai nuna khalifanci ga Imam Ali a ba, kana  mai kari da musun ma'anar karshen hadisin da yake cewa: "Allahumma wali man walahu wa adi man adahu" da cewa duk bai nuna halifanci ba!.

Game da al’amarin Gadir Khum, ka sani hannun Annabi a bude yake a kan ya yi amfani da wannan kalma ta "wali", don haka babu mai iya iyakance masa irin kalmar da zai yi amfani da ita, kuma shi ne shugaban masu hikima. Kuma a sarari tana nuna wajabcin biyayya gareshi hada da wajabcin soyayya kamar yadda ka kawo. Kuma wannan yana nuna halifancin Ali (a.s) kai tsaye ko tantama babu, saboda abubuwa kamar haka:

Na daya: Shin in tambaye ka Ya kai mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s): Kana ganin Annabi (s.a.w) zai tara mutane dubu hamsin zuwa dubu dari (bisa sabanin tarihi kan adadin) a wuri har ya sanya a dawo da wadanda suka yi gaba, a kuma tsaya har na baya su iso a wannan hanya mai zafi da suke cire rawunansu suna sanyawa kasan takalmansu, ga wahalar tafiya…! Domin kawai ya ce musu “Duk wanda nake abin sonsa ne to Ali (a.s) ma abin son sa ne. ko kuma duk wanda nake abokinsa ko mai taimakonsa Ali ma abokinsa ne ko mai taimakonsa neâ€‌. (Sai ya zama ke nan wato; Duk wani sahabi ko aboki ko abin taimako, ko mai son Annabi (s.a.w) ya zama ke nan sahabi ga Ali (a.s) ko abokinsa ko abin taimakonsa, ko mai sonsa, alhalin tarihi ya nuna mana wadanda suka yi zamani da Manzo (s.a.w) suka nuna masa so, amma bayan wafatinsa suka ki Ali (a.s), sai ya zama ke nan wannan bayanin na Manzo (s.a.w) ya zama labari ba insha’i ba, alhalin Manzo (s.a.w) ya barranta daga wasa)

 A hankalinka wani mai hankali zai yi hakan balle Annabi (s.a.w) da ya fi kowa kamala; Ashe yana bukatar haka bayan ya riga ya gaya wa musulmi gaba daya da cewa su abokai ne masoya juna mataimaka juna, kai har ma ya ce idan daya ya koka yana gabas ko yamma daya kuma yana gabas ko yamma bai taimaka masa to shi ba musulmi ba ne. ashe duk bayan wannan sai Annabi ya tara mutane domin kawai ya gaya musu hakan game da Ali (a.s)!

Na biyu: sannan kuma har Annabi ya yi addu’a da Allah ya taimaki wanda ya taimaka masa, ya tabar da wanda ya ki taimaka masa, kuma ya kebance shi da wannan banda sauran musulmi. A yanzu kana ganin wannan idan yana nufin so kawai zai kebanta da shi a cikin dukkan sahabbai! Don haka sai ya kasance sauran sahabbai bai wajabta son su ba ke nan, don haka ba laifi idan mutum ya ki su, kai yanzu ka yarda da hakan!.

Na uku: Bai’ar da aka yi masa, kuma hatta da halifofi sun yi masa bai’a a wannan wuri ba ta nuna so kawai, ta hada har da mika wuya ga jagorancinsa.

Na hudu: Murnar da Abubakar da Umar suka yi masa suka ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Talib, ka zama shugabana kuma shugaban kowane musulmi. Ban sani ba ko kana nufin Umar bn khattab ko Abubakar ba su fahimta ba ne, da su da sauran sahabbai da suka yi wa Imam Ali (a.s) murnar zama jagoransu. Ko kuma kana nufin ka ce suna taya shi murnar cewa dole ne su so shi, alhalin soyayya abu ne wanda yake na tarayya tsakanin musulmi, wanda da yadda kake nufi ne da ba su taya shi wata murna ba. Ko kuwa bai'ar da suka yi masa a wannan sahara mai zafi tana nufin soyayya da kauna kawai!, kuma idan haka ne wannan bai kebanta da shi ba, sai a yi wa kowane musulmi bai'a domin nuna soyayya da kauna gareshi. Sannan kuwa idan an yi masa bai'a domin nuna soyayya da kauna ne to yaushe ne aka nuna masa kauna da soyayya bayan wafatin Annabi (s.a.w) yayin da aka kewaye gidansa da wuta aka doki matarsa har ta yi bari da sauran munanan abubuwan da tarihi ya ruwaito.

Duba littattafai kamar: Shawahidittanzil na kanduzi bahanife: 1/ 175. Yana bi’il mawadda: juzi 1, shafi: 30 -31. Tarikhi bagdad: 8/ 290. Kuma Ahmad da ibn majah sun kawo haka daga Barra’. Kamar yadda Tirmizi da nisa’I daga Zaid. Ka duba littafin Gadir, zaka ga daruruwan masdarori da suka kawo wannan al’amarin. Haka nan dabari ya kawo wannan magana ta taya murna gareshi.

Na biyar: Gabatarwar da manzon Allah (s.a.w) ya yi a farkon hadisin yayin da yake cewa da su: “Shin ba ni ne shugaban kowane mumini da mumina ba?! A fili yake cewa ba komai ne karshe yake nufi sai abin da farko yake nufi.

Na shida: Maganar da ya rufe da ita na cewa Allah ka shaida bayan ya gama da kuma shaidawarsu. Ka ga ke nan sun shaida kan wannan al’amari mai girma ne da ya kebance shi a cikin sauran musulmi na wannan lokaci.



1 2 next