Mushrikai



Yana yiwuwa kada ya canja ya zama yana motsi ya zama yana baki yana fari yana ja yana yalo kuma siffofin ababan halitta suna faruwa akan mai siffantuwa da su, har ya zama yana da siffar fararru gaba daya, ya zama Fararre, (Allah kuwa ya daukaka daga haka daukaka mai girma). Sa’annan (S.A.W) ya ce: Idan abin da kuke tsammani na Allah yana shiga cikin wani abu to abin da kuka yi gini a kai yana rusa maganarku ne. Ya ce: Sai mutanen suka yi shiru suka ce: Zamu duba al’amarinmu. 

AMSAWA GA RA’AYI NA BIYU

Sannan Manzo (S.A.W) ya fuskanci jama’a ta biyu ya ce: Ku ba ni labari idan kuka bauta wa surar wanda yake bauta wa Allah kuka yi mata sujuda kuma kuka yi mata salla kuka dora fuskokinku masu daraja akan kasa domin sujada a gareta me kuka rage wa Ubangijin Talikai?, amma kun sani cewa yana daga hakkin wanda ya lizimci a girmama shi da ibada kada a daidaita shi da bawansa.

Shin ba ku sani ba ne cewa da wani sarki ko wani mai girma zaku daidaita shi da bawansa a girmamawa da kasakantar da kai da tsoronsa, shin wannan ba kasakantarwa ba ne ga babba kamar yadda yake girmamawa ga karami ba? Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin ba ku san cewa idan kuna bautawa Allah ta fuskacin bautawa surar bayinsa masu bauta a gareshi kuna kasakantar da Ubangijin talikai ba ne!?. Ya ce: Sai mutanen suka yi shuru kadan suka ce: Zamu duba al’amarinmu.

AMSAWA GA RA’AYI NA UKU

Sannan Manzo (S.A.W) ya ce da jama’a ta uku: Kun buga misali da mu da ku kuka kamanta mu da juna, alhali da mu da ku ba daya ba ne, saboda mu Bayin Allah ne Ababan halitta da muke biyayya ga abin da aka umarce mu da shi muke hanuwa da abinda aka hana mu ga barinsa, muke kuma bauta masa kamar yadda ya so, idan ya umarce mu ta wata fuska daga fuskoki sai mu bi shi ba kuma zamu ketare wannan iyakar ba zuwa ga abinda bai umarce mu ba, domin ba mu sani ba ta yiwu da ya nufe mu da na farko ba ya son mu yi na biyun kuma ga shi ya hana mu shiga gaba gareshi, yayin da ya umarce mu da mu fuskanci Ka’aba sai muka bi shi, sannan ya umarce mu da bauta a gareshi ta hanyar fuskantarta duk inda muke a sauran garuruwa wanda a cikinta ne muke yi masa biyayya, da wannan ba mu fita daga wani abu na daga biyayya a gareshi ba.

Yayin da Ubangiji (S.W.T) ya yi umarni da sujada ga Adam (A.S) bai yi umarni da yi masa sujada ba saboda surarsa da take ba ita ce shi (Adam) din ba, saboda haka ba ku da ikon kiyasta wancan akan haka, domin ku ba ku sani ba tayiwu yana kin abin da kuke yi, domin bai umarce ku da shi ba.

Sannan Manzo (S.A.W) ya ce: Shin kuna ganin da wani mutum ya umarce ku da ku shiga gidansa wata rana da kansa shin zaku iya shiga bayannan ba da umarninsa ba, ko kuma ku shiga wani gidan nasa daban ba wanda ya yi muku umarni da ku shiga ba? Ko kuma kuna ganin da wani mutum ya ba ku tufafi daga tufafinsa ko bawa daga bayinsa ko dabba daga dabbobinsa shin kuna iya karbar wannan?. Suka ce: Na’am. Sai ya ce: To zai yiwu ku dauki wani daban ba wanda ya ba ku ba? Suka ce: A'a, domin bai yi mana izini kan na biyun ba kamar yadda ya yi izini a na farko. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: To ku gaya mini shin Allah (S.W.T) shi ne ya fi cancanta kada a shiga gaba gareshi ba tare da umarninsa ba ko kuma sashen Ababan mallaka na daga bayi?. Suka ce: Allah ne ya fi cancanta kada a shiga gabansa a mulkinsa ba tare da izininsa ba. Sai ya ce: To me ya sa kuka yi haka? Yaushe ya umarce ku da ku yi sujada ga wadannan surorin?.

 Imam Assadik (A.S) ya ce: Sai suka ce : “Zamu duba al’amarinmu”. ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko shi (S.A.W) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (S.A.W) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace Kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!!.”

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKA.

 



back 1 2