Mushrikai



Mushrikai

Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlil Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wannan addini wanda a cikinsa akwai usulubi mai kyau na muhawara da ma'abocin wata Akida da ta saba ta da mai muhawara, wanda a cikinta zamu koyi muhawara da mukabala da munazara da hanyar da take mafi kyau kamar yadda aka yi umarni da (Bil lati Hiya Ahsan). Yana kuma koyar da Hanyoyin kafa dalili Mubashir wato dalili na kai tsaye da kuma Gaira mubashir, da kuma Jawabil halli wato Hanyar warwara da kuma Jawabin Nakdi, wato Hanyar kama mutum da abin da ya yarda ya kuma yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wannan Addini da yadda ma’abotansa suke fassara Akidojinsa. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinin da ya gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakarai wajan fahimtar Addinin Allah.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba zuwa Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa’ibawa da sauransu. Amma wannan al’umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Alkur’ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkwarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa Ayar Alkur’ani mai girma.

MUNAZARAR MANZO (S.A.W)

Imam Assadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.

Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan ala’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

MUSHRIKAI

Sa’annan sai Manzo (S.A.W) ya fuskanci Mushrikan larabawa ya  ce: Ku me ya sa kuke bautawa gumaka sabanin Allah (S.W.T)? Sai suka ce: Muna neman kusanci da Allah da wannan ne. Sai ya ce da su: Shin ita (gumakan) tana mai ji mai biyayya ga Ubangijinta ne kuma mai bauta gareshi shi ya sa kuke neman kusancin Allah da bauta mata da girmama ta?. Sai suka ce: A’a. Ya ce: Ku ne kuka saka ta da hannunku? Suka ce: Na’am. Ya ce: To ai da ya halatta bauta ga wanin Allah, da ita tafi cancanta da ta bauta muku da ku ku bauta mata! ahe kenan wanda ya umarce ku da bauta mata bai san maslaharku ba da sakamakon al’amarinku! kuma ba shi da hikima cikin abinda ya kallafa muku.

Yayin da Manzo ya fadi wannan Magana sai suka yi sabani, wadansunsu suka ce da wasunsu: Allah ya shiga cikin wasu mutane ne da suke da wannan kamanni saboda haka ne muka suranta surarsu muna girmamata saboda mu girmama Ubangijinmu ta hanyar wannan sura da Ubangijinmu ya shige ta (surantu da ita).

Wasunsu suka ce: Wannan surar ta wasu mutane ce da suka gabata suna masu bauta ga Allah kafinmu sai muka suranta surarsu muka bauta mata domin girmama Allah. Wasu kuma saka ce: Yayin Allah da ya halicci Annabi Adam (A.S) ya umarci Mala’iku da su yi masa sujada domin neman kusanci ga Allah, ashe kenan mu muka fi cancanta da yin sujada a kan Mala’iku, amma tun da wannan ya kubuce mana shi ya sa muka suranta su muna yi musu sujada domin neman kusanci zuwa ga Allah kamar yadda Mala’iku suka nemi kusanci da Allah ta hanyar yin sujada ga Adam (A.S)

AMSAWA GA RA’AYIN FARKO

Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Kun kuskure hanya kun bace. Amma ku (yana Magana da masu ra’ayin farko) da kuka ce: Allah ya shiga jikkunan wasu mutane ne nagari da kuka suranta surarsu kuna girmamata don girmama wannan surar da ya shiga ciki, da haka kun siffanta Ubangijinku da siffofin ababan halitta, shin zai yiwu Ubangijinku ya shiga cikin wani abu har ya zama wannan abin ya kewaye da shi?. To menene bambancinsa da sauran abinda ya ke abubuwa na shiga cikinsa na daga launi da dandano da kanshi da taushi da kaushi da nauyi da sako-sako? Don me abinda ake shiga cikinsa ya zama Fararre kuma Kadimi ba tare da an samu warewar wannan Kadimi wancan kuma Fararre ba daban daban? Yaya wanda bai gushe samamme ba kafin waje zai bukaci waje? Alhalin shi Mabuwayi Madaukaki ya kasance bai kuma gushe ba yana nan yadda yake.

Idan kuwa kuka siffanta shi da siffar Ababan halitta to ya lizimta muku ku siffanta shi da siffar gushewa, idan kuwa kuka siffanta shi da gushewa da faruwa to dole ku siffanta shi da karewa, domin wannan su ne suka hada siffofin masu shiga da wadanda ake shiga cikinsu, kuma dukkan wadannan siffofin masu jirkita ne, idan kuwa zatin Ubangiji Madaukaki bai jirkita ba sakamakon shigarsa cikin wani abu to ashe kenan haka yana yiwuwa!?.



1 2 next