Ali dan Abu dalib



Tarihin imam Ali dan Abu dalib (AS)

Sunansa da nasabarsa :Ali  dan Abi dalib dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdul manafi.

Mahaifiyarsa :Fadimatu â€کyar Asadi dan Hashimi dan Aabdu manafi.

Al-kunyarsa :Abul Hasan , Abul Husaini, Abus sibdaini , Abur raihanataini , Abu turab…….

Lakabinsa :Amirul munin , Sayyidul muslimin , Imamul muttakin , Ka’idul gurral muhajjalin , sayyidul ausiya , sayyidul arab , Almurtada , ya’asubuddini , Haidar , Al-anza’al badin , Asadul lahi……

Ranar haihuwarsa :13rajab shekara talatin bayan shekarar giwa wato bayan haihuwar annabi(SAW)  da shekara talatin.

Inda aka haife shi:Makka cikin ka’aba.

Yakokinsa:ya yi musharaka a yakokin manzo (SAW)  gaba daya banda yakin Tabuka da manzo ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al’amuranta amma yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin halifancinsa su ne :Aljamal da Siffaini da Annahrawan.

Matansa:1-Fadimatuz zahra (AS)’yar manzon Allah (SAW) 2- Amama â€کyar abil asi 3-Ummul banin Alkilabiyya 4-Laila â€کyar mas’ud 5-Asma’u â€کyar Amis  6-Assahba’u â€کyar Rabi’a (ummu habib) 7-Khaula â€کyar Ja’afar  8-Ummu sa’ad â€کyar Urwa 9-Makhba’a â€کyar Imru’ul kais.

  
 Ã¢â‚¬Ú©ya’yansa :
masu tarihi sun yi sabani kan yawan â€کya’yansa amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyin daban daban, sai dai mu zamu ambaci fitattun cikinsu ne:(1→4) su ne Al-Hasan   da Al-husaini da zainabul kubura da zainabul sugura (AS) su ne â€کya’yan zahra (AS)   5-muhammad al-ausad 6-Al – Abbas  7- Ja’afar (AS) 8-Abdullahi (AS) 9-Usman dan Ali (AS) 10-Muhammad dan hanafiyya 11-Muhammad Al- asgar (abubakar) 12-Yahaya 13- Umar dan Ali 14-Ummu hani 15-Maimuna 16-Jumana (ummu ja’afar) 17-Nafisa……..

Tambarin zobensa :Al-mulku lillahil wahidil kahhar.



1