Hada Salloli Biyu



2- Daga Jabir dan Zaid daga Ibn Abbas ya ce: “Na yi salla (raka’a) takwas a hade tare da Manzo (S.A.W)”[13].

3- Daga Jabir dan Zaid daga Ibn Abbas: “Hakika Manzo (S.A.W) ya yi salla a Madina bakwai-bakwai, takwas-takwas azahar da la’asar da kuma magariba da issha[14].

4- Daga Abdullahi dan Shakik, ya ce: Dan Abbas ya yi mana huduba wata rana bayan sallar la’asar har sai da rana ta fadi, taurari suka bayyana mutane suka rika cewa salla-salla, ya ce: Sai wani mutum daga Bani tamim ya zo masa bai gushe ba yana cewa salla-salla, sai Ibn Abbas ya ce da shi: Ni zaka sanar sunna, kaiconka? Sannan sai ya ce: Na ga Manzo (S.A.W) yana hadawa tsakanin azahar da la’asar da kuma magariba da issha, sai Abdullahi dan Shakik ya ce: Sai wani abu na kokwanto ya same ni, sai na zo wajan Abu huraira na tambaye shi, sai ya gaskata maganarsa”[15].

A wata ruwaya sai Ibn Abbas ya ce: “Kaiconka! mu zaka nuna wa salla? Mun kasance muna hada salla biyu ne a lokacin Manzo (S.A.W)”[16].

5- Daga Ibn Abbas: “Manzon Allah ya yi sallar azahar da la’asar a hade a Madina ba tare da tsoro ba ko tafiya”. A bu zubair ya ce: Sai na tambayi Sa’id me ya sa (Manzo) ya yi haka? Sai ya ce: Na tambayi Dan Abbas kamar yadda ka tambaye ni sai ya ce: Yana son kada al’ummarsa ta wahala ne”[17].

6- Daga Dan Abbas ya ce: “Manzo (S.A.W) ya hada sallar azahar da la’asar da kuma magariba da issah a Madina ba domin tsoro ko ruwan sama ba”[18]. A wani hadisin Abu Mu’awiya, an ce da Dan Abbas: Me yake nufi da hakan? Sai ya ce: Yana nufin kada al’ummarsa ta wahala”[19].

7- Daga Ma’azu dan Jabal ya ce: “Manzo (S.A.W) ya hada sallar azahar da la’asar da kuma magariba da issha a yakin Tabuka, ya ce: Sai na ce: Me ya sa ya yi hakan? Sai ya ce: Yana nufin kada al’ummarsa ta wahala”[20].

Buhari a sahihinsa ya rawaito wasu ruwayoyi da suka yi nuni karara da halarcin hada salla ya kuma ambaci wannan a karkashin fasalin ‘Jinkirta azahar da la’asar’ a babin ‘lokutan salla’;

Daga Jabir dan Zaid daga Dan Abbas: “Annabi ya yi salla a Madina bakwai da kuma takwas, azahar da la’asar da kuma magariba da issha”. Sai Ayyuba ya ce: Tayiwu a dare mai ruwan sama ne sai ya ce: Ta yiwu”[21]. Sharafuddin ya yi ta’aliki a game da karshen wannan magana da aka kara wacce ba ta cikin ruwaya da cewa: Ba komai suke bi ba sai zato.

Daga Amru dan Dinar ya ce na ji Jabir dan Zaid daga Ibn Abbas yana cewa: “Manzo (S.A.W) ya yi salla raka’a bakwai a hade (magarib da issha) da kuma raka’a takwas (azahar da la’asar) a hade ”[22].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next